Azumi ya fara yin ban kwana
Aminiya, bayan gaisuwa da fatan alheri. Ina kira ga daukacin al’ummar Musulmi musamman wadanda suke Najeriya da cewa mu kara dagewa wajen gudanar da ibada a wannan wata mai albarka musamman yanzu da muka doshi goman karsheMu rika kyautata wa juna da kuma barin munanan ayyuka da suka hada da surutai marasa kan gado. Mu […]
Aminiya, bayan gaisuwa da fatan alheri. Ina kira ga daukacin al’ummar Musulmi musamman wadanda suke Najeriya da cewa mu kara dagewa wajen gudanar da ibada a wannan wata mai albarka musamman yanzu da muka doshi goman karshe
Mu rika kyautata wa juna da kuma barin munanan ayyuka da suka hada da surutai marasa kan gado. Mu dage wajen yin salloli da nafilfili da zikiri da karatun Alkur’ani da Salatin Manzo (SAW) da sauran kyawawan ayyuka.
Mu guji cin naman juna wajen yin gulma da zunde da makamantansu.
A halin yanzu azumi ya fara yi mana ban kwana, don haka mu kara zage damtse don neman Rahamar Ubangiji.
Allah Ya sada mu da alherin da ke cikin wannan wata.
Naku Sani Shado Mai Neman Matar Aure Birnin Gwari, Jihar Kaduna.
07058233392
Sakonnin waya
Tsokaci kan budcaddiyar wasikar Farar Lema
Salam. Mai girma Editan jaridarmu mai tsage gaskiya duk dacinta (Aminiya). Don allah ka ba ni fili in jinjina wa malamina, Dokta Ibrahim Aliyu Katsina a kan budaddiyar wasikar da ya rubuta wa ’yar fim. Hauwa Farar Lema. Da ma a ce tun farko irin ku manyan masana Harshen Hausa da al’adunmu kuna amgana da wadannan masu yada badala da ruguza tarbiyya da sunan fadakarwa, ba su yi mana illar da suka yi a yau ba. Duk abin suke nunawa karyace da koya wa matasa dogon buri. Gyarana a rubutnka shi ne ba fa a Kano kawai ake shirya ko muke da ’yan fim. Babu jihar da babu su a Arewa. Daga dalibinka AbbdurRazak S. Inuwa Kano 08069391276.
Ga al’ummar Mali
A ranar 28 Ga wannan watan kasar Mali za ta yi zabe. A nan ina son in yi kira ga ‘yan uwana talakkawan kasar Mali da su tashi tsaye wajen zaben shugaba adali, mai gaskiya da rikon amana, wanda zai jagoranci kasarku zuwa ga makoma ta gari, ta yadda za a kauce wa kabilanci da bangaranci . Ku dauki darasi daga bin da ke faruwa ga talakawan Najeriya. Domin kwadayi mabudin wahala ne.
Daga Abdulmalik Saidu Mai biredi, tashar Bagu Gusau.
Ga Shugabanin Najeriya
Shugabanin Najeriya a daina zalunci, ko kun zauna lafiya. Daga Nasiru A. Suleja 07083273957.
Shawara ga mutanen Filato
Don Allah Aminiya ku mika min rokona zuwa ga mutanen Filato, Kirista da Musulmi su rungumi Allah. Mu zauna lafiya da juna; ku daina kashe juna. Shekaru. Haba! Daga 2001 zuwa 2013 fadan addini kabilanci ba zai taimake mu ba. Kada ’yan siyasa su rudemu, zaman lafiya shi ne ci gaban Jihar Filato da kasa gaba daya. Daga Sardaunan Jobdi 07080811417.
Ga Baba Buhari
Slm edita ina so ka ba ni dama na mika gaisuwa ta ga Gen Muhammadu Buhari Shugaban kasarmu a 2015 da yarda Allah. Allah ya kara kare shi da dukkan masoyan sa Ameen. Daga Sultan Musa Kano 08183145623.
korafi ga masu dakon mai
Salamun alaikum. Aminiya ina so ki ba ni dama in yi korafi kana bin da yake faruwa a cikin sana’armu ta tukin mota, wato masu dakon mai. Don shugabanninmu su gyara. A gaskiya tsarin duk daya ne d ana masu jiniya ina nufin ba adalci. Daga Ibrahim Hotoro Kano 08060316569.
Kwankwaso ka biya diyya
Mai girma Gwamna Kwankwaso, don Allah don Annabin Rahma ka taimaka ka biya mu diyyar filayenmu d aaka karba aka yi makarantar Ungozoma (Midwifery) a garin Burji, Madobi. Don Allah a taimaka mana. Daga Naziru Habibu Ali. 08033371691.
Gyara ya yi Edita
Edita gyaran da aka yi wa shafin adon mata ya yi kyau, kwarai da gaske, ana ta yabawa. Dama an ce mai shawara aikinsa baya baci, mu ci gaba da aminta da juna a shawarwarin kwarai, don kara amintar da amintacciyar jaridarmu. Allah Ya sa mu dace amin. Daga AbdulMumin Yahaya Sheka 08038386842
Ga Aminan Aminiya
Assalam ina yi wa daukacin yan’uwa masu karanta jaridar Aminiya fatan alkairi da fatan za mu sha ruwa lafiya. Daga Isah Abdussalamu Funtua
Ga dan majalisa Sheikh Umar
Hakika yabon gwani ya zama dole.Saboda haka,nake yin fatan alheri ga dan Majalisar mu, mai wakiltar Katsina ta tsakiya,a majalisar wakilai Abuja.Wato Sheikh Umar. Musamman yadda yake zama cikin talakkawan sa,yake tallafa masu iya iyawar sa,saba nin yadda wasu shugabannin ke yin wasan buya da talakkawan su. Daga Haruna Muhammad 07039205659.
Sabuwar adawar Hadejia
Edita na ji wani yana cewa babu adawa a Hadejia da Auyo Kafin-Hausa. To ko miyar gidanka ta yi zaki ne? Kar fa ka manta ba mutnaen garinku ne kadai suk zabi Hussaini Namadi. Don haka karya kake akwai adzawa sabuwa. Daga Yahaya Ahmed Jabo K/Hausa , Jihar Jigawa 08026392800.
Allah Ya hada kan Arewa
Allah Ya hada kan ’yan Arewa sako daga Ali Inuwa Panshekara, Chairman Kabo Air Pilgrims Welfare Association, Jihar Kano. 07039647872.
Ga Gwamna Lamido
Aminiya jaridar talakawa don Allah ina so ku isar mana da kukanmu ga Gwamna Sule Lamuido Jigawa da a taimaka mana da gyaran hanyarmu daga Gagarawa zuwa Malam Ada. Daga Maishada Damaski Malam Ada Gagarawa. 08094269001.
Matakin shugaban kasar sudan, Hakika wannan matakin da shugaban sudan silber kinn ya dauka na rushe ‘yan majalisa da ministoci don kawo karshen cin hanci da rashawa akasar yayi dai dai, don tabbas a duniya duk kasar da taci gaba, tofa ta yi yaki da cin hanci da rashawane fa kafin suka kai matsayin, sako Daga faisal Muhammed Girer, Yola, 08032390278.
Ga Ministar Ilimi Farfesa Rukayyatu
Aminiya ku gaya wa Ministar ilimi ta kasa Farfesa Rukayya Rufai Ahmad da ta kawo ziyarar gani da ido a mazauni na dindindin na Federal Unibersity Dutsinma, domin kuwa ’yan kwangilar dake gudanar da gine-gine a makarantar wasunsu tarkon mutuwa suke ginawa .Ta hanyar amfani da kayan gini marasa inganci, musanman dutsin Kankura, da kuma na wanda ake kankare da shi suna amfani da mataccen dutsi bugun hannu, domin kuwa za ka ga kasa da ciyawa da itace a ciki .Muna fatan za ku zo ku duba, domin kuwa ko gidan dabbobi bai kamata a gina da irin wannan dutsin ba. Saboda haka mu ka ga ya dace mu sanar cewar wurin da za a tara dubban mutane, bai kamata a yi amfani da mataccen dutsi ba. Muna fatan za a duba domin yin gyara. Daga Dutsinma Area Debelopment Association. Daga [email protected].
Ga Shugaban karamar Hukumar Bungudu
Shugaban karamar Hukumar Bungudu ka ji tsoron Allah, domin har yanzu baka aiwatar da ayyuka a yankinmu na Sankalawa ba, a ce gunduma kamar Sankalawa kun kas agina mata dakin shan magani; ko hanya 2.5 kun kasa yi mana. Sannan a 2015 ka ce komawa za ka yi? Daga Isma’ila Abdullahi SPARTY, Sankalawa, Jihar Zamfara 08145890077.