Azumin bana: Ba don waya ba da masu kama-baki sun yi yawa

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Musulmin Najeriya suka kashe kunne suna jiran samun labarin ganin watan Azumin Ramadan daga bakin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar wanda ya umarce su kan su fara duban jinjirin watan a ranar. Sai dai kuma ba domin waya ba a bana da masu kama-baki sun […]

Azumin bana: Ba don waya ba da masu kama-baki sun yi yawa
Azumin bana: Ba don waya ba da masu kama-baki sun yi yawa

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Musulmin Najeriya suka kashe kunne suna jiran samun labarin ganin watan Azumin Ramadan daga bakin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar wanda ya umarce su kan su fara duban jinjirin watan a ranar. Sai dai kuma ba domin waya ba a bana da masu kama-baki sun yi yawa, sakamakon yadda aka kasa samun bayanin ganin watan har wajen karfe 1:00 na dare.
Tun misalin karfe 8:00 na yamma a ranar ne wakilinmu ya isa fadar Sarkin Musulmin inda ya same ta cike matasa a waje suna murnar ranar duban wata suna da naka’aut, a cikin fadar kuwa a dakin da aka ware wa ’yan kwamitin ganin wata, jama’a ne ke shiga suna fita har zuwa karfe 11:30 na dare.
Lokacin da mambobin kwamitin suka kai wa Mai alfarma Sarkin Musulmi rahoton da suka hada sun bar wasu mutane da suka zo daga karamar Hukumar Silame don ba da shaidar ganin watan da suka yi.
Bayan share fiye da awa daya da mambobin kwamiti suka yi a can cikin fadar Sarkin Musulmi, alamu sun nuna ransu bai yi dadi kan tattaunawarsu da Mai alfarmar ba, kan haka ne manema labarai suka nemi jin ta bakin shugaban Kwamitin Ganin Wata Farfesa Sambo Wali Junaidu don jin halin da ake ciki ganin sun kwashe fiye da awa biyar suna jira a sanar da su halin da ake ciki, sai Farfesa Wali ya ce “Lamarin ganin wata kamar yadda kuke gani an dade a wannan yanayi, hakan ta faru ne domin an tsaya a tantance gaskiya don jama’ar Musulmi su gamsu da ganin watan. Bayan an tattauna sosai tsakanin kwamitina muka yi matsaya tunda an samu labarin ganin wata a wasu wurare a Jihar Kebbi Sarkin Gwandu ya ba mu labarin an ga wata a wasu wurare, shi ma Wazirin Sarkin Kabin Argungu ya ba mu tabbacin an ga wata a wasu wurare, a nan Sakkwato an samu ganin wata a Durbawa da Isa da wasu wurare. Saboda haka bayan an samu matsala ta bayar da bayanin ganin wata cewa sai ranar Lahadi za a tashi da azumi.”
Ya kara da cewa “Komai za ka yi in ka san ka yi kure bai kamata ka doge kan kuskuren ba, sai dai ka yi kokari ka san mene ne hakikanin gaskiya don ka bi ta, kuma wannan ba sabon abu ba ne ko Saudiyya ana ba da bayanin an ga wata lokaci kaza daga baya a canja a fadi an yi kuskure. Saboda haka a Musulunci ba wani jin kunya in ka san ka yi kure ka gyara, abin da yake aibi ka san ka yi kuskure ka ki gyarawa don gudun kada a ce ka yi kuskure, kan haka muka canja tunda mun samu rahotanni cewa an ga wata a wasu wurare a Najeriya, ko kauye guda aka samu tabbacin ganin wata da aka amince ya zama wajibi mu dauki azumi, saboda haka gobe (Asabar) in AllahYa kai mu za a tashi da azumi.”
Wannan shi ne karo na farko da shugaban kwamitin ganin wata ya ba da labarin ganin wata da umurtar al’ummar Musulmin Najeriya su tashi da azumi maimakon Sarkin Musulmi da ya saba ba da sanarwa.