Azumin bana: Kowa ya ci tuwon gidansu – El-Rufa’i
A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta iya cigaba da raba sukari da madara da shinkafa da sauran kayan masarufi ga musulman jahar kamar yadda gwamnatocin da suka gabata suke yi a watan Ramadan da wadansu lokuta ba. A cewarsa, gwamnatin jahar […]

A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta iya cigaba da raba sukari da madara da shinkafa da sauran kayan masarufi ga musulman jahar kamar yadda gwamnatocin da suka gabata suke yi a watan Ramadan da wadansu lokuta ba.
A cewarsa, gwamnatin jahar ba tada kudi a halin yanzu da za ta iya raba wadannan kayyakin, saboda haka sai ya nemi jama’a da su yi hakuri.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da kungiyar kiristoci ta kai masa ziyara ‘yan sa’a’o’i kadan bayan kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) rashen jahar Kaduna ta kai masa ziyarar tare da yi masa addu’ar samun nasara a mulkinsa.
Ya ci gaba da cewa, ya gaji wadansu shirye-shirye daga gwamnatin PDP da yake kokarin canza su. “An sanar da ni cewa a lokacin watan Ramadan ya kamata mu fara raba shinkafa da madara da kuma sikari, amma ba za mu iya raba komai ba, da farko dai, bai kamata gwamnati ta rika saka kanta cikin al’amuran addini ba. Na biyu kuma ba mu da kudi,” inji shi.
Wannan jawabi na gwamnan ya janyo kace-na-ce a tsakanin al’ummar jahar , inda wadansu ke ganin hukuncin da aka dauka ya yi daidai, wadansu kuma na ganin bai kamata gwamna ya dakatar da wannan ihisani da aka saba yi a duk shekara ba.
Masu ra’ayin ganin ya dace a daina raba kayan masarufin sun ce ko da ake rabawa a shekarun da suka gabata ainihin mutanen da yakamata a bai wa kayan masarufin a lokacin azumin ba su ke amfana ba. Su kuwa wadanda suke ganin ya dace a cigaba da raba kayan, hujjarsu ita ce, kudin da ake kashewa wajen sayan kayayyakin masarufi domin raba wa talakawa da kungiyoyin addini bai taka kara ya karya ba da har gwamnati za ta koka a kansu.
Ga al’ada dai a duk lokacin da wani shi’ani ya taso kamar azumi da sallah karama da babba da kirsimati da ista, gwmnatin jihar Kaduna ta kan raba kayan masarufi, irin su shinkafa da man girki da suga da madara da sauransu, ga kungiyoyin addini da manyan ma’aikata da kafafen yada labarai da sauransu. A wadansu lokutan azumi kuma musulmin na taruwa a wadansu masallatai da ma’aikatu da kuma harabobin ofishoshin kungiyoyin musulunci na jahar domin karbar wannan tallafi.
Gwamnatocin da suka gabata suna kashe makudan kudade wajen sayan kayayyakin masarufi duk shekara domin rabawa. Sai dai ita gwamnatin El-Rufai ta bayyana cewa ana amfani da sunan sayan kayan ne ana cutar gwamnati ta hanyar kwashe kudaden jama’a kuma ita ba za ta amince da hakan ba.
Wata sanarwa da Mai ba Gwamna shawara kan harkokin manema labarai Samuel Aruwan ya sanya wa hannu ta nuna cewa, bincike ya nuna cewa manyan ‘yan siyasa da kuma masu hannu da shuni ne suke amfana da kayayyakin amma ba talakawa da aka yi dominsu ba. ‘’ Ana amfani da kudin gwamnati a sayo kayan masaraufi a raba wa manyan jami’an gwmanati amma sai a bar talaka da lashe hannu.’’
Gwamna El-Rufa’i sai ya kalubalanci masu hannu da shuni su rika amfani da dukliyarsu wajen taimaka wa talaka maimakon wawure abin da aka tanadar musu. Ya ce shi da abokansa suna kokarin ganin sun ciyar da talakawa daga aljihunsu a lokacin Ramadan.
Tallafin ba wajibi ba ne – Shaikh Ahmad Gumi
Shaikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa dakatar da tallafin ya dace, domin a cewarsa, dama can ba wajibi ba ne ga gwamnati, mustahabbi ne. Ya ce wadanda ya wajaba a kan gwamnatin jahar ta kula da su da jin dadinsu sune ma’aikatanta wadanda hakkinsu ne idan wata ya yi a biya su hakkinsu na albashi. “ Hukuncinsa gaskiya ya yi daidai, domin ba a kaddamar da mustahabi a kan wajibi, mutum baya yin sallar nafila alhalin ana binsa bashin farilla. wajibin hukuma ne ta biya ma’aikatanta da ke binta bashi, sannan idan kudi ya rage sai ta iya yin wannan mustahabbi.
“ Ma’aikata ba a biya su kudi ba sannan a ce wai an dauki kudi ana ciyar da mai azumi, wannan bai yi daidai ba. Idan ka dubi abin da ke faruwa a kasar nan, akwai rashin kudi inda ma’aikata sun yi aiki na watanni amma babu albashi. Hatta irin daukar nauyin mutanen da ba abin da suke zuwa yi a aikin hajji da gwamnati ke yi bai dace ba, domin Allah da kanSa cewa Ya yi wanda ba shi da halin biya wa kansa aikin hajji bai rataya a kansa ba.’’
Dakatarwar kuskure ne – Shaikh Abubakar Baban Tune
Shi kuwa Shugaban Majalisar Limamai da Malamai na jahar Kaduna Shaikh Abubakar Baban Tune a ganinsa kuskure ne babba da gwamna ya dauki irin wannan mataki ba tare da shawartar wadanda abin ya shafa ba, domin akwai mutanen da ake bai wa tallafin da suka cancanci a ba su, kuma ko addinin musulunci ya yarda a taimaka wa irin wadannan mutane. Inda ya kawo misali da cewa, ‘’akwai tsari na tallafa wa wadanda ke da bukata ko suka shiga cikin halin neman bukata. Don haka a ce gwamnati ta hana ba su irin wannan tallafi, abin da gyara.’’
Shaikh Abubakar wanda shi ne limamin matatar mai na Kaduna, ya nemi a hana wadanda ake ganin sun fi karfin wannan tallafi, kamar manyan jami’an gwamnati da sauransu.
“Saboda haka akwai bukatar gwamna ya dauki mutanen da suka dace su rika ba shi shawara a kan irin wadannan abubuwa. Na biyu, akwai matsala wajen raba shi kansa wannan abincin, abin da ke akwai shi ne, a kan bai wa mutanen da ba su cancanta ba. Za ka ka ga mutum tsohon ma’aikacin gwamnati ne ko kwamishina ne, wanda yana da abin da zai ci, ko tsohon gwamna ne, sai a kai msu irin wadannan abubuwa. Irin wadannan mutane suke daukar kusan kashi biyu cikin uku na abin da ake badawa, wanda hakan ke sanya gwamnati tana ganin tana asarar kudade masu yawa’’.
“Irin wadannan da masu wadata da za su iya saya da kudinsu su bayar, idan an soke nasu, wannan babu laifi. Wannan bai shafi kungiyoyin addini da malamai da makamantansu ba. Saboda haka kamata ya yi a duba, akwai wadanda ba sa bukata gaba daya sai a hana su. Sannan akwai wadanda kuma suke da bukata kuma shari’a ta amince a taimaka musu a zamanance da gwamnatance, saboda akwai gundunmuwar da suke bai wa al’umma da gwamnati. Saboda haka ba su irin wadannan abubuwa ba asarar dukiya ba ce. Ina daya daga cikin Malaman kasar nan, amma ba ni da bukatar wannan abu, amma akwai wadanda ke da bukata,” inji shi.
Sanarwar da Samuel Aruwan ya fitar dai ta nuna cewa, gwamnati ba za ta amince da yin amfani da sunan addini ba ana cutar jama’a. “ Gwamnati ta hana bada kwangiloli ga manyan ‘yan siyasa domin a kawo kayayyakin masarufi a lokacin watan Ramadan, amma mun fahimci akwai almundahana a ciki. Abu ne a karara cewa ana amfani da batun ciyar da marasa galihu ne domin a sace kudaden jama’a. Bincikenmu ya nuna cewa akasarin masu amfana da wannan tallafi a watan Ramadan da lokacin bikin kiristimti jami’ain gwamnati ne da sauran manyan mutane a maimakon talakawa. Su kuma talakawa sai a barsu da bin dogayan layi suna karbar dan abin da bai taka kara ya karya ba. Alhalin miliyoyin Naira ake kashewa,” inji shi.
Don haka sai ya ce, gwamna zai cigaba da taimaka wa talakawa ta hanyoyin da suka dace, kamar fitar da zakka da yake yi a duk shekara, ba tare da sai an yada ba, a matsayinsa na musulmi.