Azumin Yara

A addinin Musulunci, yara ma suna da gagarumar rawar takawa, musamman su ma suna aikata wasu daga cikin ibadojin da suka wajabta ga baligai, duk kuwa da cewa su a gare su ba wajibin ba ne. Azumi na daya daga cikin ibadojin da yara kan kwatanta aikatawa. Muhimmancin haka ya sanya fasihin marubucin wakokin Hausa, […]

Azumin Yara
Azumin Yara

A addinin Musulunci, yara ma suna da gagarumar rawar takawa, musamman su ma suna aikata wasu daga cikin ibadojin da suka wajabta ga baligai, duk kuwa da cewa su a gare su ba wajibin ba ne. Azumi na daya daga cikin ibadojin da yara kan kwatanta aikatawa. Muhimmancin haka ya sanya fasihin marubucin wakokin Hausa, Malam Nasiru (08098559946) ya gabatar da wadamnnan baitocin:

Allahu Sarki mai niya,
Hikima Ka ba ni a rayuwa.
Azumi ga yara zan batu,
Domin gudun rafkannuwa.
Azumi farilla wajibi,
Ga dukan Musulmi ’yan uwa.
Maza da mata ba rabe
Amma ga mai hankaltuwa.
Majnunu ba azumi ga shi,
Zai ci ya sha ba damuwa.
Haka nan ga yara kankana,
Tsoho tukuf har tsohuwa.
Yaro gaban yai balaga,
Azuminsa bai shar’antuwa.
Don babu alkalami bisa,
Kayinsa don saukakuwa.
A rabin wuni in ya matsu,
da’am a ba shi ya sha ruwa.
Da hakan ga zai saba da yi,
Wata ran ya zam kammaluwa.
Ladan iyaye nasa ne,
Ga uwa uba kan basuwa.
Bisa ka sanya shi bisa,
Hanyar kwarai mai haskuwa.
A bar matsa mar kan ya yi,
A bi shi a sannu da natsuwa.
Balle idan har za a sa,
Shi ayyuka na hidimtuwa.
A zam yabonsa idan ya kai,
A ba shi kayan shan ruwa.
In an ga zai rame kwarai,
A tsayar da shi yai hutuwa.
karfi idan har ya mayar,
La ba’asa yai komuwa.
Manufa ya zam saba da yi,
Kafin ya kai ga balagtuwa.
Duk san da ya ce za ya yi,
A bar shi kar ai hanuwa.
In ya gaza kaiwa kuwa,
Gare shi ban da tsanantuwa.
Aikin ibada kwai wuya,
Yaro a sannu ka sabuwa.
Allah Ya ba mu juriya,
Yara mu tarbiyyantuwa.
Su zamo mutane nakwarai,
A nan gaba su nagartuwa.
Allah Ka karbi dukan iba-
darmu gare Ka ta amsuwa.
Azumi ya cece mu idan,
Mun zo a ranar tsayuwa.
Mai baitukan nan Nasiru
G. Ahmad ne dan uwa.
            ***