Azzaluman duniya sun doshi halaka al’ummar Najeriya
Tare da alhini da takaici nake bude wannan tsokaci mai take na sama. Tun ma kafin in gabatar da maudu’in wannan tsokaci, duk wani da ya kwana kuma ya tashi, zai iya kirdadon abin da ya saka ni cikin takaici da alhini, musamman ganin cewa tatsuniyar gizo dai ba za ta wuce koki ba. A […]
Tare da alhini da takaici nake bude wannan tsokaci mai take na sama. Tun ma kafin in gabatar da maudu’in wannan tsokaci, duk wani da ya kwana kuma ya tashi, zai iya kirdadon abin da ya saka ni cikin takaici da alhini, musamman ganin cewa tatsuniyar gizo dai ba za ta wuce koki ba. A takaice dai kowa ya san yadda Najeiya ta zama wani dandali na zubar da jinin talakawa, wadanda ba su ji ba kuma ba su gani ba. Tun daga Jihar Borno Jihar yobe, ga Jos da Kano da Kaduna. A shekarun baya kadan ma, har da wasu sassa na Jihar Naje, uwa uba, har ma da Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya, kullum sai zubar da jini ake.
Har kullum tambayoyin da ke karakaina a kwakwalwar mabambantan mutane su ne, shin su wane ne ke samun farin ciki da nishadi wajen halaka al’umma? Su wane ne kanwa uwar gamin da ke haddasa wannan ta’addanci? Shin me ke manufarsu, da suka zabi su ruguza rayuwar mayawaitan al’ummar kasar nan? Shin ta ina suke samun wadannan bama-bamai masu tsananin karfi, da har suke cin ma wannan karkatattar manufa tasu? Ya zama dole ga mutane da suke tofa wadannan mabambantan tambayoyi, domin kuwa barnar ta yi yawa.
Domin neman gamsassun amsoshin wadannan tambayoyi, masu tunani sun yi, masu hasashe sun yi, haka ma masu ba da amsa kai tsaye sun ba da amma duk da haka, har yanzu abin bai gamsar ba, ganin cewa har yanzu ta’annatin sai kara afkuwa yake. Jami’an tsaro kuwa sai suka kasance cikin tsoro da kara haddasa tsoro ga al’umma, maimakon su ba da kariya da tsaro, kamar yadda dokar kasa ta tanada.
Bari mu duba amsa ta farko, wadda ke ta’allaka wannan ta’annati ga dakarun Boko Haramun. Wannan kuwa a fili yake, musamman ganin cewa da zarar an samu tashin bam, musamman a Arewacin Najeriya, sai kakakin rundunar ya ba da sanarwar cewa kungiyarsu ce ke da ruwa a ciki, musamman ma a lokacin mulkin Jonathan. Idan muka fara lissafin tashin bama-bamai a Maiduguri da Damaturu da wanda ya faru a hedikwatar ’yan sanda da ke Abuja da wanda ya faru a ginin Majalisar dinkin Duniya da ke Abuja da kuma wanda a garin Madalla a 2011, duk kungiyar ce ta dauki alhakin faruwarsu. Yanzu kuma da aka samu canjin gwamnati, ga shi nan an kai munanan hare-haren bama-bamai a jihohin Borno, Yobe, Jos, Kano da kuma a Zariya a Jihar Kaduna.
Abin tambayar shi ne, to su wane ne ainahin ’yan Boko Haramun? Domin kuwa har yanzu babu wanda ya fito fili ya ce sunansa wane dan wane, kuma shi ne jagoran kungiyar, tun bayan kisan gillar da aka yi wa shugabansu na farko, Muhammad Yusuf. Hatta shi kansa Shekau, akwai shakku sosai a kansa, musamman yadda ma a can baya hukumomin tsaro suka yi ta cewa ya mutu har kusan karo uku. Ke nan akwai yiwuwar cewa wasu ne ke fakewa da kungiyar suna son cin ma wata boyayyar manufarsu.
A wasu nazarce-nazarce da na gudanar, na ci karo da bayanai masu dimbin yawa, wadanda ke ba da amsa karara ga wannan abu da ke faruwa a Najeriya. A wannan nazari da na gudanar, na gano wadanda suke gudanar da wannan ta’annati da kuma wadanda suka daure gindi ake gudanar da shi. Ka fadi da ihu, ba wasu ne ba masu wannan karkatattar akida da mugun nufi sai azzaluman duniya. Game da abin da suke nufin cin mawa kuwa, na gano cewa babban burinsu shi ne, su tarwatsa Najeriya, ya zamanto nan gaba an share sunanta daga doron kasa. Za mu ga karin bayani nan gaba kadan.
A wani littafi mai suna ‘Dajjal: The AntiChrist’ wanda wani kwararren malamin Musulunci na duniya, Ahmad Thomson ya rubuta. Ya tona asirin makiya al’umma, makiya Musulunci, azzaluman duniya. Haka kuma ya kira su da sunan Masu Bautar Shaidan, wadanda ba su son ganin duk wata akida ko al’ada ta kirki tana gudana a duniya. Babu abin da suka sanya gaba sai duniya da bautar abin duniya. Domin cin ma manufarsu, za su iya yin duk wani abu komai muninsa, kama tun daga tsafi, kisan kai da sauransu.
Wadannan karkatattun mutane, masu siffar shaidanu, sun yi sansani ne a manyan kasashen duniya. Su ne ummul haba’isin duk wata ja’iba da ke faruwa a sassan duniya. Tashin-tashina da bala’o’in da ke addabar kasashen Musulmi, kamar su Irak, Pakistan, Libya, Siriya, Masar da Afganistan da sauransu, duk aika-aikar wadannan karkatattun azzaluman duniya ne.
Wani dalili da ya sanya na yanke hukuncin cewa wadannan azzalumai ne ke da alhakin tashe-tashen hankulan da ke faruwa a Najeriya shi ne, a can baya, wani daga cikin jami’in wadannan azzaluman duniya, ya taba fitowa baro-baro ya tabbatar da cewa, Najeriya za ta wargaje, nan da shekarar 2015. Tun daga wannan lokaci abubuwa rikitattu suka yi ta faruwa, wadanda suka hada da tashe-tashen hankula masu yoyo da kabilanci, siyasa ko addini da sauransu.
Ban gama fahimtar haka ba, sai da na karanta wata makala da wani kwararren dan jarida na duniya, mai suna Gordon Duff ya rubuta kuma aka wallafa a wasu jaridun kasar nan a 2011. A makalar tasa, wacce ya yi wa taken: ‘An Durfafi Tarwatsa Najeriya’ kamar yadda ya ce, ya rubuta ta ne a matsayin gargadi ga shugabannin Najeriya domin su dauki matakan da suka dace, domin hana afkuwar wannan mugun kuduri na azzaluman duniya.
Idan mun duba yadda a cikin kwanaki uku kacal, aka kai hari Jos, wurin wa’azin Musulunci da kuma majami’a, da kuma yadda aka kai hari a masallaci a Kano, da yadda a safiyar Talatar da ta gabata aka kai hari a Zariya, wajen tantance ma’aikata, wannan ya isa ya nuna maka cewa al’ummar kasar nan kawai ake son halakawa, Musulmi da Kirista.
Manufar wannan aika-aika ita ce, a haddasa gaba da kiyayya tsakanin al’ummar Najeriya, kamar yadda ake son raba mutane da ibada.
Muna rokon Allah, albarkacin wannan muhimmiyar ibada ta azumi, Allah Ka kawo mana dauki a kasar nan, Ka yi mana maganin wadannan mutane da ke halaka bayinKa. Allah Ka yafe mana zunubbanmu, Ka tausaya mana ba don hakalyenmu ba, sai don rahamarKa da jinkanKa. Allah Ka kawo mana dauki!