Baƙar rayuwar da ke cikin karuwanci a Abuja
Addinin Kirista ya yi hani mai karfi daga aikata zina don neman kudi.
Matasan mata da ’yan mata da dama sukan samu kansu tsundum a cikin sana’ar karuwanci a fadar mulkin Nijeriya, Abuja, duk da dimbin hadarurrukan da suke haduwa da su kamar yadda binciken Aminiya ya gano:
A kowane dare, dubban mata da ’yan mata a Nijeriya sukan fuskanci dimbin matsaloli har ma da yiwuwar rasa rai a sana’arsu ta sayar da jikinsu don samun kudi ga mutanen da ba su taba ganinsu ba da suke haduwa da su a kan titi.
- Rikicin manoma da makiyaya ya yi ajalin mutum 12 a Taraba
- ’Yan bindiga sun sace mutum 150 a ƙauyen Zamfara
Mummumar sana’ar da ake kyama a tsakanin al’ummar Najeriya kuma haramtacciya musamman a jihohin Arewacin Najeriya da ake aiki da Shari’ar Musulunci; amma duk da haka za a rika ganin irin wadannan ’yan matan sun daukar wa kansu kazamiyar harkar don dan abin da suke samu da ka iya jefa su a cikin da-na-sani a karshe.
A rahoton da Statista ta fitar a Intanet a shekarar 2020 ya nuna adadin karuwai a jihohi 10 kadai a Najeriya sun kai dubu 874.
Babu wani kundi a hukumance da yake dauke da adadin masu sana’ar karuwanci da kai-kawo a kan tituna da daddare a Babban Birnin Tarayya, Abuja, amma rahotanni sun nuna harkar na kara yawaita a manyan wurare da suka hada da yankunan Gwarimpa da Kubwa da Utako da Jabi da Wuse Zone 4 da Wuse 2 da Garki II da sauransu.
A cikin wannan rahoto, Aminiya ta yi nazarin irin hadarurrukan da masu sana’ar karuwanci suke fuskanta kamar yadda wasu masu sana’ar suka shaida wa jaridar a Garki II, inda suka bayyana firgici da munanan abubuwan da suka ci karo da su a harkar karuwanci.
Abubuwan takaicin da ke faruwa a Titin Legas
Titin Legas da ke Garki II a garin Abuja sananne ne wajen harkokin kasuwanci da rana, sai dai bayan nan kuma, akwai wani abu da ke biyo bayan shigar duhun dare da ake gudanarwa.
Wata ’yar shekara 32 da ta taba haihuwa mai suna Joy (ba ainihin sunanta ke nan ba) da ke zaune a Lungun Gurguwa, daya daga cikin sassan da ke Titin Legas wacce ta ce ta kwashe kusan shekara takwas tana karuwanci, ta bayyana shekarun da ta kwashe cikin takaici da da-na-sani inda ta ce har ranta ta kusa rasawa a hannun wasu abokan harkarta da ta hadu da su a Titin Legas da kuma yadda wata irinta ta taba rasa rayuwarta a harkar.
Ta fadi yayin da take share hawayen da ke gangarowa daga idanuwanta, yadda wani ya dauke ta a wata yammaci a Titin Legas don zuwa Gwarinpa da ita, sai ya nufi Shataletalen Apo, “Bayan mun isa daidai taransifoma ya gama duk abin da zai yi da ni a cikin motarsa, sai ya zaro karamar bindigar pistol ya yi kokarin harbe ni.
“Ya umurce ni da in fita in bar masa mota kuma ga shi cikin dare ne ba ni da wanda zai taimake ni haka na sauka,” in ji ta.
Ta ce a wata rana kuma da misalin karfe 4 zuwa 5 na asuba wani da ya dauke ta a daidai Zone 4 zai kai ta Wuse 2 yana zuwa daidai gadar Zone 4 sai ya tsaya ita kuma tana tunanin ko ya sauka ne ya dauko wani abu a kasa kawai sai ya zaro wuka ya ce ta ba shi duk kudin da ke tare da ita ko ya kashe ta.
“Na ce masa ba ni da komai a yanzu haka ma na fito neman abin da zan biya wa dana kudin makaranta ne kuma duk tsawon daren ban samu ko sisi ba,” in ji ta.
Ta ce hakan da ta fada masa ne ya sa ya tausaya mata inda ya ce ta fice masa daga mota kuma zai kyale ta ne kawai saboda danta, amma ba don haka ba ya ce sai ya kashe ta ko da ba ta da ko sisi.
Kamar Joy, su ma Binta da Grace (ba sunansu na ainihi ba ne) suna rayuwa ne cikin firgici a yayin da suke gudanar da karuwanci da bakin mutane.
Grace, ‘yar 28 da ta fito daga Kudancin Najeriya, ta ce ta tsallake rijiya da baya, inda ta kusa rasa rayuwarta. Ita kuma Binta, ‘yar shekara 34 da ta fito da Arewa mai nisa, ta ce saboda hadarin da ta tsinci kanta a ciki ya sa ta samu wani kulunboto da take sanyawa a kugunta.
Ta ce, “Duk lokacin da wani mummunan abu ke shirin faruwa da ni yakan nuna min.”
Duk da irin labaran tashin hankalin da suke faruwa da su da rasa rayuka da wasunsu ke yi, duk da haka sauran da ke cikin sana’ar ba sa shiga taitayinsu.
Tsakanin shan kwaya, kawalci da mutuwa
A rahoton da Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi da Laifuffuka (UNODC) ya fitar a shekarar 2018, ya ce a cikin duk mutum hudu da ke tu’ammali da kwaya a Najeriya, to, daya mace ce.
Yawancin matan da suka dauki sana’ar karuwanci ba a raba su da ’yan shaye-shayen kwayoyi.
Da yawa kwayoyin ne ke mantar da su tare da dauke musu damuwar barazanar da suke fuskanta na rayuwar kan titi.
Joy ta tabbatar da cewa mafi munin abin da ta taba cin karo da shi a rayuwarta shi ne lokacin da ta fara shaye-shayen kwayoyi.
“Duk lokacin da na bude ido na gan ni a kan titi sai na zubar da hawaye saboda miyagun kawaye ne suka koya min shan kwayoyi,” in ji ta.
Shi kuma Aliyu (ba sunansa na asali ba ne) kawali ne da ke hada ’yan mata da abokan holewarsu. Da yake bayani ya ce “Matan ba sa iya tabuka wani abin kirki idan ba su sha kwayoyi ba.
“Wasunsu kan sha sigari ne, wasunsu kuma kan sha wiwi, yayin da wasu kuma kan sha kwayoyi irin su Tramadol da sauran miyagun kwayoyi.”
Ya ce shi ma yakan dan taba shaye-shayen. A matsayinsa na kawali, Aliyu ya ce wasu matan kan zo su same shi don ya hada su da abokan holewa bisa tsadancewa, “Yayin da a wani lokaci kuma mazan ne ke zuwa don neman irin matan da suke so su hole da su.
“Muna da mata da suke da shekaru tsakanin 16 da 17 da 18 da sauransu, mu kan hada sai mu kai wa mutum bayan ta dawo sai ta ba mu wani abu.
“Za ka iya samun Naira 2,000 idan ka kai wa wani yarinya, yayin da wani kuma zai bayar da har Naira 3,000. Idan ma ka samu wani babban mutum har Naira 5,000 suke ba mu,” in ji shi.
Aliyu ya kara da cewa suna ganin abubuwa iri-iri na ban tsoro yayin gudanar da kawalci, inda ya bayyana wani al’amari da ya faru kasa da shekara guda kamar haka: “Wani mutum da ba a san ko wane ne ba ya zo ya dauki wata yarinya da na sani, inda ya ba ta Naira dubu 10, ni kuma ta ba ni Naira 2,000 daga ciki kafin su tafi, muka yi sallama da ita.
“Washegari kawai sai muka samu labarin ganin gawarta a kasar gada an bata ta.”
‘Danginmu ba su san abin da muke yi a nan b’
Yayin da ake kallon ’ya’yan da suka san abin da suke yi kan fita bayan sun girma don samun abin dogaro da kai, tare da dawowa su rika kula da iyayensu, yawanci iyayen irin wadannan ’yan mata ba sa sanin irin halin da ‘ya’yansu suke ciki ko me suke aikatawa ba.
Abin da wata ta shaida mana ke nan cewa iyayensu ba su ma san wane irin hali suke ciki ko kuma me suke aikatawa a Abuja ba.
Blessing wacce aka san ta da sana’ar gyaran gashi a lokacin da take tare da mahaifinta da kuma ’ya’yanta guda biyu a yankin Ibo, ta ce iyayenta sun dauka irin sana’ar da take ci gaba da gudanarwa ke nan tun dawowarta Abuja, “Mahaifina ya dauka gyaran gashi nake yi a nan,” inji ta.
Ita ma Binta wacce ta ce ta baro gida ne a sanadiyyar kishiyar uwa, ta ce babu wani daga cikin danginta da ya san me take aikatawa a nan.
Binta ta ce duk da ta mallaki wajen gyaran gashi a Abuja, amma har yanzu tana gudanar da harkar bin maza.
Duk da dai ta bayyana aniyarta na barin harkar don rungumar sana’ar gyaran gashin gadangadan, ta sha alwashin ba za ta bari iyayenta su san me take aikatawa a Abuja ba.
Illolin harkar ga kiwon lafiya
“Wata kawata da ke irin wannan badalar ta zama abin tausayi yanzu, tana cikin wani hali saboda rashin lafiyar da take ciki.
“An ce ta kamu da cututtuka ne da dama, amma dai na san ta kamu da cutar kanjamau ne kuma ta samu matsalar shanyewar barayin jiki,” in ji Binta.
Da yawa daga cikin matan suna sane da irin hadarurrukan da suke tattare da wannan aiki ko dai a kashe su ko su fada cikin wata lalura da hadarurruka.
Dokta Tochukwu, wani likita a Asibitin Rouz da ke Abuja ya shaida wa Aminiya cewa hadarurrukan da suke fuskantar irin wadannan mutane sun hada da harbuwa da cututtukan da ake kamuwa da su ta hanyar jima’i da suka hada da kanjamau da ciwon hanta (HPB) da kansar mafitsara da sauran cututtuka daban-daban.
Dokta Tochukwu ya bayyana abin da ya taba cin karo da shi a asibitin lokacin da aka kawo wata budurwa asibitin da misalin karfe daya na dare jini na ta zuba daga al’aurarta, inda bayan ya yi tambaya aka shaida musu cewa a yayin saduwa da wani ne hakan ya faru.
“Bayan mun yi gwaje-gwaje mun gano ya yi mata lahani inda ta samu matsala a mafitsararta abin da ya dauke mu lokaci mai tsawo kafin mu iya shawo kansa, amma dai a karshe mun yi nasara bayan wahalar da muka sha,” in ji shi.
Baya ga hadarin daukar cikin da ba a shirya yin sa ba da kuma hadarin da ke tafe da zubar da cikin, likitan ya bayyana halin da wasu za su iya shiga na damuwa da ka iya kaiwa ga rasa rayukan matan da akan ci zarafinsu.
Matsayar addini kan wannan baɗala
Duk da yawaitar harkar karuwanci a Nijeriya, karantarwar dukkan addinai na yin Allah wadai da irin wannan harka.
Sheikh Muhammed Abubakar na Masallacin Apo da ke Rukunin Gidajen ’Yan Majalisa ya bayyana wa Aminiya a Abuja cewa duk abin da ya shafi zina haram ne kuma abin kyama.
Ya bayyana fadin Allah Madaukaki a cikin Suratul Isra’i aya ta 32 da ke haramta kusantar zina da aikata ta koda ta dalilin neman kudi ne ko kuma don jin dadi.
Kuma babban kuskure da laifi ne daukarsa a matsayin hanyar neman kudi.
“Aikata hakan haramun ne a Musulunci kuma hakkin al’umma ne da na gwamnati da daidaikun mutane su hana aikata hakan.
“Kada mu zauna mu nade hannayenmu muna kallon yadda ’ya’yanmu ke bi lay-layi suna gararamba a kan tituna suna aikata irin wannan fasikanci,” in ji shi.
Shi ma Rabaran Emmanuel Alex Bunka na cocin Anglican Church of the Resurrection da ke Maiduguri, ya ce an haramta duk wani nau’i na saduwa tsakanin namiji da mace ba tare da aure ba.
“Addinin Kirista ya yi hani mai karfi daga aikata zina don neman kudi. A cikin Littafin Romawa Sura ta 12 aya ta 1 da ke cikin Baibul an ce mu mika gangar jikinmu ga Ubangiji a matsayin sadaukarwa, wanda hakan ke nuni kai-tsaye cewa kada mu cakuda jikkunanmu da na matan banza sai dai a cikin Ruhu Mai tsarki.
Haka ma cikin Littafin Korantiyawa na 1 aya ta 6 zuwa ta 16 Baibul ya ce, “Yanzu wannan jikin ba na kazantar zina ba ne, amma na Ubangiji ne Ubangijin gangan jiki.”
Baibul ya umurci dukkan maza da mata su yi aiki cikin kunya da girmamawa don samun kudin shiga maimakon kutsawa cikin neman kudi ta hanyar fasikancin zina.