Baƙuwar cuta ta kashe ƙananan yara 5 a Nasarawa
Kananan yara biyar sun rasu cikin kasa da awa 24 sakamakon wata bakuwar cuta a Karamar Hukumar Obi da ke Jihar Nasarawa
Aƙalla ƙananan yara biyar ne aka tabbatar sun rasu cikin kasa da awa 24 sakamakon wata baƙuwar cuta a Ƙaramar Hukumar Obi da ke Jihar Nasarawa.
Babbar Jami’ar Binciken Cututtuka ta Jihar Nasarawa, Dokta Grace Tsakpa, ta tabbatar da mutuwar kananan yaran, inda ta ce an tura jami’an lafiya zuwa yankin domin gudanar da bincike.
Ƙauyen Gidinye da ke yankin Jenkwe na daga cikin wuraren da aka samu ɓullar wannan baƙuwar cutar mai kisa.
Wakilin Aminiya ya gano cewa yaran shekarunsu 5 ne zuwa 15, kuma sun yi fama da ciwo ciki da ciwon kai da amai da gudawa a ranakun Litinin da Talata kafin su rasu.
- An kashe rai an harbi wasu 6 a rikicin sojoji da matasa a Bauchi
- NAJERIYA A YAU: Tasirin Fitattun ’Yan Soshiyal Midiya Wajen Sauya Ra’ayin Al’umma
Sakataren Yaɗa Labaran Ƙungiyar Matasan Magili, Mista Samuel Akala, ya shaida wa wakilinmu cewa, yaran da suka rasu, sun bar gida tare da iyayensu zuwa gona a kusa da Karamar Hukumar Keana ne, inda a can suka fara rashin lafiya.
A cewarsa, “Cikin ƙasa da awa 24 muka rasa ƙananan yara biyar a yankin nan.
“Sun je gona da iyayensu, a can ne ɗayasu ya fara kukan ciwon kai, ya fara amai da gudawa a ranar.
“Kafin a daɗe numfanshinsa ya fara sarƙewa, shi ne aka kawo shi gida, a nan ya rasu.
“Sauran yaran ma irin wannan alamar suka nuna kafin su rasu, kuma abin ƙaruwa yake yi, duk da cewa ba mu san ainihin dalilin mace-macen ba.
“Muna roƙon Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (PHCDA) da Hukumar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) su gudanar da bincike a ƙananan hukumomin Obi da Keana, domin ganowa da shawo kan wannan baƙuwar cuta,” in ji shi.