A takarda kawai aka ba mu shinkafar tallafin Tinubu —Gwamnatin Gombe

Gwamnatin Gombe ta ƙaryata iƙirarin ministan yaɗa labarai na cewa an ba ta tireloli cike da shinkafar tallafin Tunubu domin raba wa talakawan jihar

A takarda kawai aka ba mu shinkafar tallafin Tinubu —Gwamnatin Gombe

Gwamnatin Jihar Gombe ta ce har yanzu ba a ba ta shinkafar tallafi da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa jihohi alƙawari ba.

Mai magana da yawun gwamnatun jihar, Ismaila Uba Misilli, ne ya  munsata iƙirarin  Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, na cewa jihar ta karɓi tireloli 20 na shinkafar tallafin da Tunubu ya yi alkwari domin rage wa talakawa raɗaɗin yunwa da tsadar rayuwa.

Ismaila Uba Misilli, ya tabbatar da cewa kawo yanzu, sanarwar ware musu shinkafar ce kawai aka yi, amma ba a kai ga ba wa Jihar Gombe ba.

Ya ƙara da cewa, a iya saninsa, jihohi maƙwabtan Gombe a yankin Arewa maso Gabas irin su Adamawa, Yobe, Taraba, su ma ba a ba su masu shinkafar ta tallafi ba.

Daraktan yaɗa labaran, ya buƙaci ministan ya fito ya yi ƙarin bayani kan maganar ba wa Gombe kasonta na shinkafar tallafin domin kawar da zargi.

A ƙarshe ya buƙaci ministan ya tantance gaskiyar iƙirarin da ya yi, da kuma gano haƙiƙanin inda shinkafar ta maƙale.

A ƙarshe ya yi fatan nan ba da jimawa ba za a ba wa Jihar Gombe nata shinkafar tallafin domin raba wa talakawanta.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna