Ba a ba mu abincin tallafi ba —Gwamnatin Adamawa
Gwamnatin Jihar Adamawa ta musanta karbar tireloli 20 na abincin tallafi daga Gwamnatin Tarayya.
Gwamnatin Jihar Adamawa ta musanta karbar tireloli 20 na abincin tallafi daga Gwamnatin Tarayya.
Ta bayyana cewa duk da haka, maimako zaman jira, ta dauki matakin raba nata kayan tallafin domin rage wa al’ummar jihar halin da suke ciki na matsin rayuwa.
Kwamishinan yada labaran jihar, Iliya James, ranar 29 ga watan yuni, ya sanar cewa, gwamnatin jihar ta karbi kasonta na takin zamani da Gwamnatin Tarayya ta bayar domin raba wa al’umma.
A cewarsa, gwamnatin jihar a shirye take domin inganta walwalar jama’a, duk da kalubalen da ake fuskanta kasar.
- Sayar wa Dangote danyen mai: ’Yan Arewa sun yaba da matakin
- Ya ƙone budurwa saboda ta ƙi auren shi
- ’Yan bindiga 31 sun shiga hannu a Nasarawa
Sai dai ya shawarci al’ummar jihar da su guji shiga taruka da ka iya haddasa tarzoma da mummunan sakamako kamar yadda aka gani a lokacin zanga-zangar ‘End SARS’.
Kwamishinan ya jaddada muhimmacnin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali don cigaban al’umma, yana mai gargadi ga masu neman barnata dukiya ko haddasa tashin hankali.
A cewarsa, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da gwamnatinsa za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa don magance matsalolin da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya da kuma inganta rayuwar al’umma.