Ba a ba noma muhimmanci a kasafin kudin badi ba – Farfesa Dadari

Farfesa Salihu Adamu Dadari, Malami ne a Sashen Bincike da Nazarin Aikin Gona na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma mai shirhi ne a kan al’amuran yau da kullum. A tattaunawar da ya yi da wakilinmu, ya ce ’yan siyasar Najeriya da suke canza sheka daga jam’iyyunsu suna komawa wasu jam’iyyun, masu son mulki […]

Ba a ba noma muhimmanci a kasafin kudin badi ba – Farfesa Dadari

Farfesa Salihu Adamu Dadari, Malami ne a Sashen Bincike da Nazarin Aikin Gona na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma mai shirhi ne a kan al’amuran yau da kullum. A tattaunawar da ya yi da wakilinmu, ya ce ’yan siyasar Najeriya da suke canza sheka daga jam’iyyunsu suna komawa wasu jam’iyyun, masu son mulki ne, ba masu son gyara kasa ba.  Har’ila yau ya yi bayani kan yaki da cin hanci a Najeriya tare da nuna damuwa kan yadda ba a bai wa aikin noma kaso mai yawa ba a kasafin kudin shekara mai zuwa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

A ’yan kwanakin nan wadansu ’yan siyasa suna ta canja sheka daga jam’iyunsu suna komawa wasu jam’iyyun, yaya kake kallon wannan lamari?

Wato siyasar ra’ayi da akida ita ce siyasa ta gaskiya. Amma irin wannan hali na ’yan siyasar Najeriya na tsalle-tsalle ko sun samu mulki ba za su yi komai na ci gaba ba a Najeriya. Saboda suna canja sheka ne don su samu biyan bukatarsu ta neman mulki. Amma da ana siyasa ce tsakani da Allah, don a yi wa jama’a aiki irin wannan tsalle-tsalle ba zai taso ba. Don haka duk dan siyasar da ka ga yana canja sheka daga wannan jam’iyya zuwa waccan jam’iyya, idan ya samu biyan bukata babu abin da zai yi wa jama’a. 

Saboda idan ’yan siyasa suna son su yi wa jama’arsu aiki ne, to su rika zama a cikin jam’iyyunsu suna yi wa jama’arsu aiki. Kuma ya kamata jama’ar Najeriya su dauki mataki watsar da duk  dan siyasar da ya canja sheka ya koma wata jam’iyya. Domin yana neman biyan bukatarsa ce ta mulki, ba don ya yi wa jama’a aiki ba. 

Me za ka ce game da shirin yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Buhari take yi a yanzu?

Cin hanci da rashawa a Najeriya yana da tarihi. Domin lokacin da aka karbi mulkin Najeriya daga hanun Turawan mulkin mallaka, shugabannin kasar nan na baya sun yi wa kasar nan adalci. A lokacin babu man fetur amma duk da haka, an yi kokarin yadda kasa za ta ci gaba ba tare da sace-sacen kudaden kasar ba. Amma sai aka wayi gari da soja suka karbi mulki suka ji dadi, kudi ya shiga hanunsu, har ta kai ga wata gwamnatin soja ta fada wa duniya cewa matsalar Najeriya a lokacin, ita ce yadda za ta kashe kudin Najeriya, saboda kudade sun yi yawa, wannan ya sanya ’yan jari hujja suka hau kan Najeriya, suka yi dai-dai da tattalin arzikinta, suka rika diban kudin Najeriya suna kai wa waje. Suka jefa mu cikin bashi wannan shi ne ya yi sanadin lalacewar Najeriya, a takaice dai mulkin sojoji ne sanadin lalacewar Najeriya musamman kan cin hanci da rashawa.

Domin tun lokacin sojoji, cin hanci da rashawa ya bunkasa aka wayi gari ko aiki za a dauki mutum, dole sai ya bayar da cin hanci. Idan mutum ya mutu yana aiki, idan iyalansa za su karbi hakkokinsa sai sun bayar da cin hanci. Za ka ga ma’aikaci yana da gidaje sama da 100 a Abuja, kuma kowa ya san cewa albashinsa bai fi ya gina gida daya ba. Kudaden kasar nan da aka sace aka kai kasashen waje su ne ake zuwa a karbo rance, kuma a zuba mana ruwa. Akwai zaluncin da ya kai wannan?

Sai aka wayi gari Allah Ya kawo gwamnatin Buhari ta zo ta kama wannan aiki, na yaki da wannan mummunar dabi’a ta cin hanci da rashawa a kasar nan. 

To a ganinka gwamnatin Buhari ta samu nasarar wannan yaki da cin hanci da rashawa da take yi?

Gwamnatin Buhari ta yi kokari wajen fito da tsarin ajiye kudaden Gwamnatin Tarayya a asusu daya. Domin ta dalilin wannan tsari kudi na zuwa wajen gwamnati kai-tsaye. Amma matsalar da aka samu ita ce shin ana amfani da kudaden da aka kwato? Domin talakan Najeriya yana cewa har yanzu bai gani a kasa ba. Ita kuma gwamnati tana cewa kudaden da aka karba, sai doka ta bayar da umarnin a yi amfani da su tukuna. 

A gaskiya a tafiyar akwai sanyi domin muna son mu ga an kama ayyuka da wadannan kudade da aka kwato. Duk da mun san cewa kudaden da aka samu daga mai ba su isa wajen kasafin kudin kasar nan, wato ana cike gibi da wadannan kudade da aka kwato.  Muna fatar Allah Ya wayar da kan gwamnatin Najeriya ta yi amfani da kudaden da ta kwato wajen yi wa al’ummar kasar nan ayyuka. Domin a kullum talakawa suna kukan cewa ba su gani a kasa ba.

Abin da muke so shi ne gwamnatoci su yi wa jama’a aiki, yanzu hanyoyin Najeriya a lalace suke. Makarantunmu da asibitocinmu a lalace suke, kamfanoninmu a durkushe suke. Miliyoyin daliban Najeriya sun gama makaranta babu aikin yi. Babu yadda za a yi a ci gaba a Najeriya a irin wannan hali.  

A kwanakin baya Shugaban kasa ya gabatar wa Majalisun Dokoki ta kasa kasafin kudin shekara mai zuwa, a matsayinka na masanin harkokin noma yaya kake ganin kason da aka ware wa noma a kasafin kudin?

 A gaskiya a wannan kasafin kudi ba a dauki noma da muhimmanci ba, kamar yadda aka yi a sauran kasafin kudin Najeriya na shekarun da suka gabata. A tsarin Majalisar dinkin Duniya duk kasar da take son ta ci gaba, dole ne ta bai wa harkokin noma muhimmanci a kasafin kudinta, akalla ana son kowace kasa ta bai wa harkokin noma kashi 15 zuwa 25 cikin 100 na kasafinta. Saboda an dauki noma kamar wata shinfada ce ta ci gaba da yalwatuwa da tasiri. 

Don haka ko kasashen da suka ci gaba kamar Amurka da Birtaniya ba su cigaba ba sai da suka bunkasa noma. Abin da ya sa noma ya samu matsala a Najeriya shi ne sanya kabilanci a cikin kasafin kudinmu. Wato kabilancin da muke sanyawa a cikin kasafin kudi shi ne ni idan ba za a yi abu a wajenmu ba, ba zan goyi baya ba.

 Yanzu a jihohin Arewa muna da yanayi da kasar noma mai kyau, abin da yake faruwa idan aka gabatar da kasafin kudi dan Kudu ba ya goyon bayan a bai wa harkokin noma karfi a kasafin kudin Najeriya, saboda ba a noma a yankinsa. Don haka ’yan majalisa daga Arewa ne ya kamata su tsaya su kare harkokin noma a majalisa, domin a bai wa harkokin noma kaso mai tsoka a kasafin kudin kasar nan. Domin suna wakiltar mutanen Arewa ne, wadanda noma da kiwo ne karfinsu. Don haka duk abin da ya shafi noma da kiwo ya kamata ’yan majalisa daga Arewa su ba shi muhimmanci. 

Kuma ko wa ke mulki a kasar nan, idan ya ga sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai na Arewa sun tsaya kan a ware wa harkokin noma kaso mai yawa dole ne zai yi.  Don haka ’yan majalisa daga Arewa suna san cewa an saukar da harkokin noma kasa a kasafin kudin badi, don haka ya kamata su tashi su yi magana domin a halin yanzu wannan kasafin kudi yana nan a gabansu. 

 Kuma ya kamata ’yan Nijeriya baki daya wato ’yan majalisa daga Arewa da Kudu su san cewa yanzu ana bai wa noma muhimmanci a duniya. Domin suna zuwa kasashen waje suna ganin yadda ake bai wa harkokin noma muhimmanci. Don me ba za su hada kai a ba wai harkokin noma muhimmanci don arzikin Najeriya ya rayu ba? Domin idan ba an inganta noma ba, tattalin arzikin Najeriya ba zai taba rayuwa ba.