Ba a Banza Matasa Ke Samun Kudi Da ‘Mining’ Ba
Mamallakan mining [coins] ɗin ba kuɗi suke bayarwa ba, coin za su ba ka ladar wahalar da yi musu ta gina musu community har coin ɗinsu ya samu shiga kasuwa
Wani matashi wanda ya fahimci harkar crypto a baya-bayan nan ya bayyana cewar laifin wadanda suka dade a harkar ‘mining’ ne ya sa mutane suka yi wa harkar mummunar fahimta suke ganin kudin banza suke samu.
Matashin mai suna Najib Salisu, wanda ya yi wannan jawabi a shafinsa na Facebook ya ce “kuna ce wa mutane ana ba ku ne kudi a kyauta ba tare da wahala ba… motsi kadan ku saka hoton wasu daloli ko rasit na kudi.”
- Najeriya ce kasa ta 10 a yawan ’yan Crypto a duniya – Rahoto
- CBN ya soke harajin tura kudi ta intanet
Matshin ya ce sam lamarin ba haka yake ba, saboda sai bayan ya shiga ya gane cewa su wadannan kamfanonin biyan mutane ladan wahalarsu suke yi ta hanyar ba su coins din da suka yi kokari suka gina masu ta hanyar mininig.
“Waɗannan mamallakan mining [coins] ɗin ba kuɗi suke bayarwa ba, coin za su ba ka ladan wahalar da ka musu ta gina musu community har coin ɗinsu ya samu shiga kasuwa,” in ji shi.
Ya kara da cewa “idan sun ba ka coin ka siyar ko ka riƙe kayanka.”
Lamarin crypto musamman a Arewacin Najeriya na ci gaba da karɓuwa inda wasu da dama har da malamai ke nuna rashin goyon bayansu a kai, inda suke ganin ya ci karo da addinin Musulunci.