Ba a dakatar da tsarin kunshe kaya ba, an ma fara shi – Bello
Babban Sakataren Hukumar Kula da Sufurin jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), Barista Hassan Bello, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta dakatar da da tsarin kunshe kaya a manyan jiragen ruwa na dakon kaya ba, inda ya ce tsarin yana ci gaba da gudana tun farkon Janairun bana. Shugaban Hukumar NSC, ya musanta jita-jitar dakatar da […]
Babban Sakataren Hukumar Kula da Sufurin jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), Barista Hassan Bello, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta dakatar da da tsarin kunshe kaya a manyan jiragen ruwa na dakon kaya ba, inda ya ce tsarin yana ci gaba da gudana tun farkon Janairun bana.
Shugaban Hukumar NSC, ya musanta jita-jitar dakatar da tsarin daga gwamnati, inda ya ce hukumar tana sahun gaba wajen yayata bukatar gabatar da tsarin.
Barista Bello ya ce tsarin yana nan a dogon lokaci ba tare da an aiwatar da shi ba.
Ya yi wannann bayani ne a ranar Alhamis din makon jiya a Legas a wani taro da masu ruwa-da-tsaki kan alfanun fara aikin Tashar Teku-Huta ta Kaduna.
Ya ce, “Ina son yin amfani da wannan dama in yi bayani a kan kunshe kayayyaki. Ina jin akwai wata jarida da ta ce an dakatar tana ruwaito Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa, wannan ba gaskiya ba ne. Batun kunshe kaya ya ci gaba da gudana tun daga 1 ga Janairu. Don haka babu ja baya kan tsarin kunshe kaya, saboda tsarin yana nan tuntuni a kasa, Hukumar NSC ce ta ce mu tallata ga masu ruwa-da-tsaki.”
Ya kara da cewa: “Mun dauki kukan masu ruwa-da-tsaki zuwa ga hukumomin da suka dace, kuma hukumomin sun share musu hawaye suka yi kokarin magancewa da warware duk matsalolin da suke akwai, Ba a dakatar da kunshe kaya ba; kuma babu gudu babu ja da baya kan kunshe kayan.”
Game da fara aiki a Tashar Teku-Huta ta Kaduna, Bello ya ce: “Batun Tashar Teku-Huta yana da matukar muhimmanci ga Gwamnatin Tarayya kuma mun zaku sosai mu ga an samu nasarar gudanar da ita.
“Dalili ke nan ya sanya muka zo nan domin neman shawarwari da hadin kanku. A farkon lamarin irin wannan, dole ne a samu matsaloli, amma na yi amanna, tare da ku za mu samar da hadin kai da masu ruwa-da-tsaki da suka kamata,” inji shi.
Manajan Daraktan Hukumar Jiragen kasa ta Najeriya, Mista Fidet Okhiria ya ce akwai shirin da ke kan hanya na sayo karin kan jiragen kasa daga waje.
Okhiria ya ce taragogin daukar kaya za su rika safarar kayayyaki masu yawa daga tashoshin ruwa zuwa na Teku-Huta, inda ya cewa duk kwantainonin da za a rika kaiwa Kaduna, za a rika kai su ne ta jirgin kasa.
A wurin taron, Manajan Tashar Teku-Huta ta Kaduna (KIDP), Mista Rotimi Raimi ya roki gwamnati ta gina layin dogo zuwa tasharsu ta Kaduna. Ya ce tashar ta Teku-Huta za ta samar da ayyukan yi da yawa ga ’yan Najeriya. Ya nuna bukatar cewa masu manyan motocin safara ya kamata su shigo cikin tsarin, domin safarar kayayyaki daga tashar. Ya kara da cewa tashar ta Teku-Huta za ta bunkasa kasuwanci sannan kuma ta samar da kudin shiga.