Ba a dauki rayukan mutane a bakin komai ba a Najeriya —Atiku
Abun bakin ciki ne a ce rayuwar mutane ba ta da wata daraja a kasarmu.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce a halin da ake ciki ba a dauki rayukan mutane a bakin komai ba a Najeriya.
Waziri Adamawa ya bayyana hakan ne cikin wani sako ya wallafa ranar Lahadi a shafinsa na Facebook.
- Ya zama tilas a yaba wa Buhari —Majalisar Dattawa
- Muhimman abubuwa a rikicin Tigray na kasar Habasha
Atiku ya yi tir da hare-haren ’yan bindiga da suka haddasa mutuwar mutane 38 a Jihar Kaduna a karshen mako.
“Kashe-kashen mutane da ake yi kusan kullum bisa kowane irin dalili abun Allah wadai ne.
“Abun bakin ciki ne a ce rayuwar mutane ba ta da wata daraja a kasarmu, a cewar Atiku.
Ya kara da cewa, “ina taya iyalan wadanda abun ya shafa alhinin rashin da suka yi.
A karshen makon da muka yi bankwana da shi ne ’yan bindiga suka kashe mutane 38 a wasu hare-hare da suka kai Kananan Hukumomin Giwa, Chikun, Zariya da Zangon Kataf duk a Jihar Kaduna.