Ba a fahimci Buhari ba kan korar Malaman Firamare – Dakta Hakeem

Tsohon Shugaban Jam’iyar APC kuma shugaban Ma’aikata a ofishin Kakakin Majalisar Dattawa, Dakta Hakeem Baba Ahmed ya ce karya ake wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari cewa yana goyan bayan korar malamai a Jihar Kaduna. A cewar Dakta Hakeem masu yada irin wannan karya suna yin hakan ne domin cimma wani buri nasu. Ya bayyana hakan […]

Ba a fahimci Buhari ba kan korar Malaman Firamare – Dakta Hakeem

Tsohon Shugaban Jam’iyar APC kuma shugaban Ma’aikata a ofishin Kakakin Majalisar Dattawa, Dakta Hakeem Baba Ahmed ya ce karya ake wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari cewa yana goyan bayan korar malamai a Jihar Kaduna.

A cewar Dakta Hakeem masu yada irin wannan karya suna yin hakan ne domin cimma wani buri nasu. Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar da ta gabata a wani shiri na gidan talabijin na DITb da Alheri Radio.

“karya ake wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa yana goyan bayan korar malamai a jihar. Abinda kawai na san ya ce shi ne yana goyan bayan shirin gyaran ilimi da gwamnatin jihar ke yi.

Kada fa a mance cewa akwai makarantun Sakandire na tarayya dake karkashinsa amma ai bai kori kowa ba. Dan haka ya ya za a yi ace yana goyan bayan korar wasu. Wannan zance karya ne,” in ji shi.

“Idan har Buhari bai ce a kori malamai ba, to su daina daukar hakkinsa. Akwai bambanci cewa ina goyan bayan gyara da kuma korar malamai. Su daina yi masa kazafi da kuma daukar hakkinsa,” a cewar sa.

ýDakta Hakeem ya kuma kara da cewa akwai bukatar a inganta makarantu kafin a fara korar mutane daga aiki. Ya ce ko an kori malamai an dauki wasu sabbi wannan ba zai canza ba, domin su wadanda za a dauka din dole dai wadannan gurbatattun makarantu za a tura su aiki.

“Babu wanda zai ce El-rufai na kuskure akan gyarar ilimi na ‘ya’yan talakawa. Duk wanda ya ce haka mahaukaci ne. Kuma ma’aikatan nan ba faduwa suka yi ba akwai wadanda suka dauke su aiki. Wa ke sanya ido akan hukumomi irinsu SUBEB wanda su ke da alhakin daukar ma’aikatan, wa ya yi masu jarabawa?” Sannan ya kuma nuna cewa akwai matsaloli sosai a Jihar Kaduna wanda ya ce akwai bukatar gwamnatin jihar ta tashi tsaye wajen magance su a maimakon a saki jaki ana dukan ýtaiki.