Ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Saudiyya
Ta tabbata sai ranar Laraba, za a yi sallah a ƙasar Saudiyya.
Hukumar Kula da Ganin Wata ta ƙasar Saudiyya, ta sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a ƙasar.
Hakan na nufin za a azumci ranar Talata, inda Ramadanan bana za a cike ya zama an yi azumi 30 kenan.
- Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da rabon hatsi tan 42,000 a Sakkwato
- Obaseki ya zaɓi ɗan shekara 38 sabon mataimakin gwamnan Edo
Don haka ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, 2024 ce za ta yi daidai da 1 ga watan Shawwal na shekarar 1445 bayan hijira.
A kan haka ne hukumar gudanarwar ƙasar Saudiyya, ta umarci jama’ar ƙasar da su cike azuminsu zuwa 30, sannan su yi idi a ranar Laraba.
Tun a ranar Lahadi ne dai wasu masana Ilimin Taurari da Sararin Samaniya suka yi hasashen cewar ba za a ga jinjirin watan Shawwal ba a ranar Litinin ba, har sai zuwa ranar Laraba.