Ba a gyara barna da barna

Salam. Ina kira ga gwamnatin Jihar Kaduna de cew koran malaman makaranta sama da dubu 20 da kike shirin yi sam bai dace ba, duk kuwa da cewa gwamnatin na ikirarin daukar sabin malamai dubu 25 a madadinsu. A cikin wadannan malamai da ake shirin kora, wasu shekarunsu sun ja nan da wani dan lokaci […]

Ba a gyara barna da barna

Salam. Ina kira ga gwamnatin Jihar Kaduna de cew koran malaman makaranta sama da dubu 20 da kike shirin yi sam bai dace ba, duk kuwa da cewa gwamnatin na ikirarin daukar sabin malamai dubu 25 a madadinsu. A cikin wadannan malamai da ake shirin kora, wasu shekarunsu sun ja nan da wani dan lokaci ma ritaya za su yi, ya kamata a barsu su karasa. Da koyarwar suka dogara, babu wani abu da suke yi na samun kudi wajen tafiyar da rayuwarsu. Ina laifi ma ace korar ta tsaya ga wadanda gwamnatin da ta gabata ta dauka ba bisa ka’ida ba. Daga cikin malaman da ake shirin kora akwai yiwuwar za a kori wanda ya koyar da gwamna ko kwamishinan ilimi ko wasu mukarraban gwamnati. Ina ba gwamnatin Jihar Kaduna shawara da ta nemi wata hanyar da za ta gyara ilimi maimakon wacce ta daukanr wa kanta a yanzu.

Al’ummar Kaduna ko ya kuka gani? Ku yi alkalanci a kalamai na da kanu.

Sako daga Nasiru Kainuwa Hadejia 08100229688/09073801967