Ba a janye dakatar da Nafisa Abdullahi ba – Arewa,MOPPAN
Makonni biyu bayan kwamitin Gyara Kayanka da ke karkashin kungiyar Arewa Film Makers da MOPPAN da ta dattawan ‘yan fim da kuma ta daraktoci ya dakatar da fitacciyar jaruma Nafisa Abdullahi na tsawon shekara biyu, kungiyoyin sun karyata jita-jitar janye dakatarwar da aka yi wa jarumar. Jita-jita ta baza gari cewa jarumar ta samu goyon […]

Makonni biyu bayan kwamitin Gyara Kayanka da ke karkashin kungiyar Arewa Film Makers da MOPPAN da ta dattawan ‘yan fim da kuma ta daraktoci ya dakatar da fitacciyar jaruma Nafisa Abdullahi na tsawon shekara biyu, kungiyoyin sun karyata jita-jitar janye dakatarwar da aka yi wa jarumar.
Jita-jita ta baza gari cewa jarumar ta samu goyon bayan kungiyar MOPPAN, kuma har an janye dakatarwar da aka yi mata.
Bayan Aminiya ta gudanar da bincike ta gano har yanzu ba a janye dakatarwar ba.
Isma’il Afakallah wanda shi ne Shugaban kungiyar Arewa Film Makers, kuma mamba a cikin kwamitin Gyara Kayanka ya karyata jita-jitar, inda ya ce batun dakatarwa na nan kuma kwamitinsu ba na kungiya daya ba ce.
Ya ce: “A gaskiya Nafisa ba ta samu goyon bayan MOPPAN ba, abin da nake so a fahimta shi ne, kwamitin Gyara Kayanka ba na kungiya daya ba ne. Kwamitin hadin gwiwa ne tsakanin kungiyoyin da suka shafi fina-finan Hausa. Kwamitin ya kunshi kungiyar Arewa Film Makers wanda ni ne shugabanta, akwai kuma Khalid Musa Shugaban kungiyar MOPPAN, akwai mataimakin shugaban kungiyar daraktoci ta Arewa, akwai Falalu dorayi daga MOPPAN kuma mamba a kungiyar daraktoci, akwai Kamilu Jigon Hausa Shugaban kungiyar Dattawan ‘yan fim (Elders Forum), don haka kwamitin ba wai na kungiyar Arewa ba ne kawai.”
Ya ce, tabbas Nafisa ta je MOPPAN don an ce mata ai Arewa ce ta dakatar da ita, ita kuma mambar MOPPAN ce, da ta je sai ta nuna katin shaidar ita mambar MOPPAN ce, sai shugaban MOPPAN din ya ce babu batun ko ‘yar wace kungiya ce, domin shi ma yana cikin kwamitin, don haka batun Arewa ce ta dakatar da ita bai ma taso, domin shi ne sakataren kwamitin, kuma shi ya rubuta takardar dakatarwar. A takaice dai har yanzu dakatarwa na nan daram.
Da aka tambaye shi ko me zai ce dangane da batun da ake cewa kwamitin gyara kayanka na sulhu ne ba wai ladaftarwa ba sai ya ce, “karya ne kwamitin ba wai kawai na sulhu ba ne har da ladaftarwa, domin ya taba dakatar da Maryam Malika da Safiya Musa.”
Khalid Musa Shugaban MOPPAN ya ce ba a janye dakatarwar ba.
Ya ce: “Dukkan ladaftarwa da ka ga an yi, ana yin ta ne ba don kiyayya ba sai don a daidaita sahu. Kuma mun ladaftar da ita ne ba wai kan zargin shigar badala da shirya shagulgulan da ta yi ba, a’a, mun ladaftar da ita ne sakamakon rashin da’a na amsa kiranmu.”
Ya ce, tabbas Nafisa ba ta amsa kiransu na farko da suka yi ba, kuma da a ce ta amsa gayyatarsu za su nusar da ita hade da ba ta shawarwari ne. Bayan an kira ta a waya kuma sai ta yi kalamai marasa dadi, “Daga baya da ta zo ofis dinmu sai ta ce a gaskiya dalilin da ya sa ba ta zo ba don ba a tura mata takardar gayyata daga kwamitin a rubuce ba. Kuma ko da aka kira ta a waya ba ta san wanda ya kira ta a gaban kwamitin ba.”Inji Khalid Musa.
Ya ce: “A yanzu dai mun ce ta rubuta takardar ba da hakuri, sai dai har yanzu ba ta rubuto ta turo ba, idan ta kawo sai mu duba mu ga yadda za a yi. Idan sai kwamitin ya sake zama sai a zauna, idan kuma ba sai mun sake zama ba dai, takardar da za ta rubuto ne za ta nuna hakan.”
An ce an kafa kwamiti gyara kayanka don sulhu ba wai don ladaftarwa ba, sai ga shi kuma ya ladaftar da Nafisa ko me za ka ce kan hakan? Sai ya ce: “Tabbas wannan kwamitin yana da hurumin ladaftarwa. Ka sani duk kwamitin da zai yi sulhu zai iya ladaftarwa. Domin ladaftarwa ai sulhu ne, dukkansu sukan kawo gyara.”
Wakilinmu ya kira jarumar ta waya don ya ji ta bakinta, amma ba ta dauki waya ba, ya tura mata sako ma amma ba ta ba shi amsa ba.