… Ba a kaina EFCC ta fara gayyatar mutane ba – Lamido
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce ba a kansa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta fara gayyatar mutane ba, don haka ba ya tsoron gayyatar hukumar. Alhaj i Sule Lamido ya ce an sha kama ’ya’yansa tare da kama wasu gwamnoni don haka a shirye yake ya amsa […]
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce ba a kansa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta fara gayyatar mutane ba, don haka ba ya tsoron gayyatar hukumar.
Alhaj i Sule Lamido ya ce an sha kama ’ya’yansa tare da kama wasu gwamnoni don haka a shirye yake ya amsa tambayoyin hukuma “Zan kuma je ofishinta domin na kare kaina,” inji shi.
Alhaji Sule Lamido ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tanbayoyin manema labarai a garin Bamaina da ke kusa da Birnin Kudu bayan dawowarsa daga kasar waje.
Alhaji Lamido wanda ya nuna takaici kan rashin ci gabaa a kasar nan a fannoni da dama, ya ce da yana da ikon dakatar da ci gaban kasashen Turai domin a samu irin ci gaban da a Najeriya da ya yi.
Alhaji Sule Lamido ya nuna damuwa kan yadda ake wa shugabanni barazana da EFCC, ya ce babu wani abu da za a yi masa barazana da shi domin a baya ma an yi masa barazana an kama ’ya’yansa domin biyan wasu bukatu, kuma an kama gwamnoni da kwamashinonin gwamnati amma hakan bai hana komai ba.
Dangane da bashin da ya bar wa gwamnatin da ta gaje shi, ya ce babu dalilin da zai sa a yi ta magana ana sakewa, domin abin da ya sani ya bar bashin Naira biliyan 14 ne ba kamar yadda Gwamnan Jihar Muhammadu Badaru yake fada cewa bashin Naira biliyan 117 ake bin gwamnatin Jigawa ba.