Ba a kama zomo a zaune

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatar alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labari mai suna “Ba a kama zomo a zaune.” Labarin na nuni ne ga illar kiwa a rayuwar mutum. A sha karatu lafiya:   Ado yaro ne mai kwazo da hazaka. Yana da aboki Bello. Bello […]

Ba a kama zomo a zaune

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatar alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labari mai suna “Ba a kama zomo a zaune.” Labarin na nuni ne ga illar kiwa a rayuwar mutum. A sha karatu lafiya:

 

Ado yaro ne mai kwazo da hazaka. Yana da aboki Bello. Bello kuma babu abin da ya tsana a rayuwarsa kamar karatu. Gani yake kamar ana takura wa rayuwarsa idan aka ce ya tafi makaranta. Musamman idan ya dawo daga makarantar boko sai iyayensa su sake ce da shi ya je Islamiyya abin ba karamin ci masa tuwo a kwarya yake ba.

Ado kuma ya kasance mai son karatu da son koyon sababbin abubuwa da yawan tambaya a ajinsu. A kullum shi yake zuwa na daya.

Idan an zo jarrabawa sai Bello ya matsa wa Ado ya ba shi satar amsar tambayoyin ko kuma ya yi masa duka idan an tashi daga makaranta.

Bayan shekaru da dama Ado ya girma ya zama hamshakin mai kudi yana dan zagawa can sai ya hango wani tsoho na sayar da kayan miya a bakin kasuwa. Sai ya tsaya domin su yi ciniki. Daga kan tsohon ke da wuya sai ya kira Ado da sunansa.

Abin ya bai wa Ado mamaki ya tambaye shi a ina ya san shi. Sai ya ce da shi ai shi ne Bello wadda suke aji daya a makaranta.

Ado ya yi salati ya ce da shi “Ai ka ga irinta nan shi ya sa  aka ce ‘Ba a kama zomo a zaune.’ Ga irin abin da ka janyo wa kanka.”

Tare da fatar Manyan Gobe za su zama masu kwazo da hazaka wajen yin karatu domin zama masu wadata a gaba.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos