Ba a kira daga kwance
’Yan Najeriya dai shu’uman mutane ne, wadanda ba su saurin nuna gamsuwarsu ko kuma jinkirta bayyana kosawarsu game da wasu al’amura, musamman ma wadanda suka shafi shugabanninsu, ko kuma yadda ake jan ragamar mulkinsu. Shi ya sa sau da yawa ake jin suna yawan babatu game da kamun ludayin wasu da ke rirrike da madafun […]
’Yan Najeriya dai shu’uman mutane ne, wadanda ba su saurin nuna gamsuwarsu ko kuma jinkirta bayyana kosawarsu game da wasu al’amura, musamman ma wadanda suka shafi shugabanninsu, ko kuma yadda ake jan ragamar mulkinsu. Shi ya sa sau da yawa ake jin suna yawan babatu game da kamun ludayin wasu da ke rirrike da madafun iko, walau dai don fahimtar cewa akwai gazawa tare da su, ko kuma don watakila sun kasance tamkar akuyar da aka dora wa kayan taiki, sun kasa matsawa ko’ina. A ’yan watannin baya jama’a da yawa sun nuna damuwarsu game da irin rawar da wasu ministocin Shugaba Buhari ke takawa, wacce suka ce ba ta gamsarwa, domin suna hada ta da tsalle kamar gada, ba ta kuma burge kowa. A sakamakon haka ne Shugaba Muhamadu Buhari ya bukaci jama’ar da suke ganin haka su kara zuba idanu, suna mayar da hankali kan kwazon ministocin don su fayyace masa cancantarsu na ci gaba da dumama kujerunsu, ko kuma a sauya su da wadanda ake ganin masu kamar zuwa ne don a ji dadin aikensu yadda ya kamata. Amma duk da haka nan babu mutum guda daga cikin wadanda suka raina tsayuwar wata da suka hau sama domin su gyara, ma’ana babu wadanda suka fito fili firi-falo, suka fayyace irin raunin da suke gani tattare da wasu ministocin ga wanda ya nannada su, balle ya san yadda zai yi da su.
Haka nan kuma bayan cikar ministocin shekara guda a bakin aiki sai ga Shugaba Buhari da kansa yana horon su da su nuna wa jama’a cewa su na kwarai ne, kuma ababen dogaro da amincewa a ko da yaushe, su kuma yi aiki tukuru domin samun yardar jama’a. To idan suna tabuwa me zai kawo wannan batun? Bisa ga dukkan alamu dai Shugaba Buhari na cewa ne ministocinsa ba su turza sosai ba wajen aiwatar da ayyukan da za su biya bukatun jama’ar kasar nan. Watakila wasunsu sun yi aiki ba ji, ba gani, wasunsu kuma shantakewa suka yi, domin kuwa an fahimci suna ta yin bori ne da sanyin jiki, kuma hakan ya sa ana ta ganin wallen Gwamnatin Buhari, ana cewa wai ba haka aka so ba, kanin miji ya fi miji kyau.
Sai bayan watanni biyar da rantsar da Shugaba Buhari sa’annan ya nannada ministocin da aka dauka cewa za su zabura da aiki ne ka’in da na’in da zarar an rantsar da su. Amma sai ga shi nan suna ta jan-kafa kamar kajin da kwai ya fashe musu a ciki, duk kuwa da cewa ba za a zargesu su kadai ba game da haka, sanin cewa barewa ba za ta yi gudu ’yarta ta yi sassarfa ba. Wasu da yawa daga cikinsu sun tabuka, sun kuma aikata abin yabo, domin sun yi fitsari da kumfa, amma duk da haka nan ana cewa sun kasance tarin tsintsiyar jam’iyyarsu, babu wata sharar kirkin da suka yi, kuma hakan ya sa matsalolin da ke addabar tattalin arziki suka kara kamari har sai da ta kai ga an gamu da karayar tattalin arzikin da ya sa kasar dingisawa.
Abin mamaki game da ministocin Buhari shi ne zarginsu da aka yi na kasa tsara kasafin kudI mai ma’ana, kuma ingantacce da zai gamsar, ya kuma zame karbabbe ga ’yan majalisar tarayya, wadanda za su tottona shi sosai, su tabbatar ya dace da biyan bukatun ciyar da kasar gaba cikin hanzari. Sa’anan ko da aka yi ta kai ruwa rana kafin a amince da shi, ba a aiwatar da dukkan abubuwan da ya kunsa ba kan kari, kuma daidai da yadda aka tsara, domin kuwa an kasa samar da wadatattun kudin gudanar da ayyukan da aka sanya a kasafin kudin bana daidai da yadda gwamnati ta yi alkawarin aiwatarwa, duk kuwa da cewa ga kudi nan tsundun a asusun gwamnati ba wai babu ne ba.
Baicin haka nan kuma an kasa cika muhimman alkawuran da aka dauka don habaka aikin gona. Ko da yake an samu gagarumar nasara kan kudin da aka narkar wajen noman shinkafa, amma ba a dauki kwararan matakan rage yawan asarar da aka fuskanta ba wajen girbewa da adanawa. Sai kuma ga shi nan duk da nasarorin da aka samu wadanda suka sanya jama’a zarya don murna, gwamnati na ikirarin zuwan yunwa saboda karancin abincin da ta ce za a fuskanta daga farkon shekara mai zuwa domin za a kyale bakin haure su jide amfanin da aka samar zuwa kasashensu.
To idan tun da farko gwamnati da ministocinta sun yi alkawarin samar da wadataccen abinci a bana, ta kuma ce hakan zai magance sawo abinci daga kasashen ketare, to mene ne kuma na yi wa jama’a barazana da yunwa?
To muddin aka ci gaba da cewa ministocin Shugaba Buhari sun gaza wajen sauke nauyin da ke bisa kawunansu, me zai hana ba zai sake nazarin matsayinsu don ya tabbatar da cancantarsu a bakin aikin da ya ba su da kuma dacewarsu bisa kujerunsu, wacce daga bisanta za su nuna kwazonsu na gudanar da ayyukansu daidai da manufofin jam’iyyar da ta kafa gwamnatinsu ba? Wajibi ne fa gwamnatin Buhari ta kara matsa lamba da kuma sanya idanu wajen ganin irin damun da ministocinta ke yi a ma’aikatunsu, ta kuma kara bullo da dabarun karfafa musu gwiwa da yi masu jagoranci na gari don a kai ga biyan dukkan bukatun da aka sanya a gaba.
Yanzu dai ga shi nan an cinye shekara guda, ana tafiyar kura, a yi gaba, a yi baya, kuma ba za a ci gaba da tafiya haka ba, domin inda aka dosa ba kusa ne ba, sa’annan kuma ko rabin tafiyar ba a yi ba. Ga dai shekarar 2016 ta zo karshe, sai a ja damarar yin ban-kwana da matsalolin da suka sanya aka yi ta tafiyar sanda da rarrafe a cikinta, a kuma mike tsaye sosai a yi ta kazar-kazar wajen ganin an shiga sabuwar shekara da kafar dama.
Talakawa dai na son ganin canji ko sauyin da aka sa ran amfana matuka daga gare shi don ya kankama tun daga yanzu, ya kuma ja geza zuwa sabuwar shekarar da za mu shiga cikin ’yan kwanakin nan. Yanzu dai saura makonni uku a ga bayan wannan shekarar da kuma irin kudin da aka kasafta don yi wa jama’a ayyuka a cikinta, amma har yanzu karfen da aka sanya a cikin wuta bai yi ja ba balle a janyo a buga shi. Abin fa na yi ne, kuma kowa da kowa sai ya ja damara, an jure duk wahalhalun da ake cin karo da su a wannan shekarar, an kuma daddage don shawo kansu a shekara mai zuwa. Kodayake ana cewa wuya ba ta kisa, amma ba ta da dadi, ko da magani ne kuwa.To an dai ga bayan wucewarta, sai kuma a yi ta shan dadi. Ba za a sha dadin ba hakan a fayu, domin ba a yin kira daga kwance!