Ba a korar dabban farauta na Harami
Babi na Tara: Ba a korar dabban farauta na Harami 308. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: “Abdul Wahab ya ba mu labari, ya ce, Khalid ya ba mu labari daga Ikramata daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa: Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Hakika Allah Ya haramta Makka ba ta […]
Babi na Tara:
Ba a korar dabban farauta na Harami
308. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: “Abdul Wahab ya ba mu labari, ya ce, Khalid ya ba mu labari daga Ikramata daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa: Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Hakika Allah Ya haramta Makka ba ta taba halatta ga wani ba gabanina. Kuma ba za ta halatta ga wani ba a bayana ba, kuma lallai ni ma an halatta mini ita na dan wani lokaci ne daga cikin yini ba a cire makiyayarta. Ba a tumbuke itaciyarta, ba a korar abin farautarta, ba a daukar tsuntuwarta face ga mai sanarwa.” Abbas ya ce, “Ya Manzon Allah! Sai dai ban da tsaure saboda makerarmu da kaburburanmu.” Sai (Annabi) ya ce, “To, ban da ciyawar tsaure.” An karbo daga Ikramat ya ce, “Shin ka san ma’anar kore abin farauta? Shi ne mutum ya kore shi (dabba) daga inuwa shi ya maye a mazauninsa.”
Babi na Goma:
Yaki ba ya halatta a Makka.
Abu Shuraih (RA) ya ce, “Daga Annabi (SAW) ya ce, “Ba a zubar da jini cikinta.”
309. An karbo daga Usman dan Abu Shaiba ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga Mansur daga Mujahid daga dawus daga dan Abbas (RA), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce, a ranar da ya ci Makka da yaki. Babu hijira daga Makka zuwa Madina amma akwai kokari (jihadi) da kyakkyawar niyya. Idan aka kira ku zuwa ga yaki ku tafi da gaggawa. Amma babu shakka Allah Ya haramta wannan da yaki tun ranar halitta sammai da kassai don haka haramun yake har zuwa Ranar kiyama. Kuma lallai ku sani yaki bai halatta a cikinta ba gabanina. Kuma ba a halatta mini ba face na dan sa’a daya daga yini, saboda haka haramun yake bisa haramcin Allah zuwa Ranar kiyama, ba a cire kayarta (wanda ba ta cutarwa), kuma ba a korar farautarta. Ba a daukar tsintuwarta face ga mai sanarwa da ita. Ba a cire makiyayarta.” Abbas ya ce: “Ya Manzon Allah! Ban da ciyarwar tsaure, domin makerarmu da rufin dakunanmu,” (annabi) ya ce, “ban da ciyarwar tsaure.”
Babi na Goma Sha daya:
Yin kaho ga mai Ihrami, dan Umar ya yi wa dansa lalas (sakiya) alhali na mai Ihrami. Mai harami na magani matukar babu turare cikinsu.”
310. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Amru ya ce, mana: Farkon abin da na ji Adda’u yana cewa: “Na ji dan Abbas (RA), yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya yi kaho alhali yana mai Ihrami.” Sa’an nan na ji shi yana cewa: “dawus ya ba ni labari daga dan Abbas na ce, “Mai yiwuwa ya ji su daga gare su (biyu).”
311. An karbo daga Khalid dan Makhlad ya ce: “Sulaiman dan Bilal ya ba mu labari daga Alkamata dan Abu Alkamata daga Abdurrahman A’raji daga dan Buhainata (RA), ya ce: “Annabi (SAW) ya yi kaho a tsakiyar kansa lokacin da yake cikin Ihrami a Lahyi Jamal.”
Babi na Goma Sha Biyu:
Auren mai Ihrami da Hajji ko Umara
312. An karbo daga Abul Mughirah Abdulkudus dan Hajjaju ya ce: “Auza’iy ya ba mu labari ya ce, Adda’u dan Rabah, daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya auri Maimuna alhali yana mai Ihrami.”