Ba a kwace wa yaro garma
Gwamnatocin Jihar Kaduna na lokutan farko da kuma na yanzu kan ware makudan kudi kowace shekara a kasafin kudi don inganta ilmi, kuma a sakamakon haka an samar da makarantun firamare da na sakandare kusan a dukkan unguwannin da ke fadin Jihar Kaduna, har ma ta kai ga an mayar da wasu makarantun sakandaren kwana […]
Gwamnatocin Jihar Kaduna na lokutan farko da kuma na yanzu kan ware makudan kudi kowace shekara a kasafin kudi don inganta ilmi, kuma a sakamakon haka an samar da makarantun firamare da na sakandare kusan a dukkan unguwannin da ke fadin Jihar Kaduna, har ma ta kai ga an mayar da wasu makarantun sakandaren kwana na je-ka- ka-dawo don a fadada su ta yadda za su dauki dalibai masu yawa a kowace shekara. Domin a tabbatar iyayen yara na sakin jiki wajen tuttura ‘ya’yansu makarantu sai aka mayar da harkar bayar da ilmi kyauta, illa kawai dan abin da ake karba daga hannun iyaye saboda gudanar da kungiyar Malamai da Iyayen yara. Ko wannan ma Gwamnatin Muhamad Namadi Sambo ta hana karba sa’ilin da ta zo a shekarar 2007.
Haka nan aka ci gaba a irin wannan halin kafin zuwan Malam Nasir el-Rufa’i, kuma ko shi ma da ya zo bai canja ba, ya ci gaba da bayar da ilmi kyauta yadda aka saba tun can fil-azal a Jihar Kaduna. Ya samu makarantu na gudana yadda ya kamata, domin gwamnatin da ta gabaci tasa ta narkar da makudan kudi wajen inganta su da kulawa da su. Amma da zuwan gwamnatinsa sai aka fara cewa wai za a bayar da ilmi kyauta, kuma a sakamakon haka wai yawan almajiran makarantun firamare a jihar ya nunka, ninkin-ba-ninkin domin wai da ma can abin da ke hana yara zuwa makaranta shi ne kudin da iyayensu ne ba su iya biya, alhali kuwa ba haka zancen yake ba, kyauta ake bayar da ilmi tun kafin kafuwar gwamnatin Malam Nasir.
Duk da cewa akwai makarantu a wurare da yawa a Jihar Kaduna, suna kuma cikin kyakkyawan hayyaci kafin shekarar 2015, a kan ci karo da matsalolin sayen kayayyakin da ake bukata a-kai-a-kai, ko kuma loto-loto, wadanda gwamnati kan fitar da kudi domin haka. Amma tun daga zuwan wannan gwamnati mai ci sai aka fara gamuwa da cikas game da haka, domin kuwa ba ta fitar da kudi yadda ya kamata dangane da haka don sayen kayayyakin gudanar da makarantu, sai da taimakon iyayen yara.
Ana cikin haka ne kuma sai ga gwamnatin tarayya ta taso da batun cika alkawarin da ta yi lokacin yakin neman zabe na ciyar da almajiran wasu ajujuwan makarantun firamare da abincin safe a fadin tarayyar kasar nan. Tun kafin a kai ga haka, sai Gwamnatin Malam Nasir ta riga Ladan tayar da kabbara, ta ce ita za ta ci gaba da yin haka kafin gwamnatin tarayya ta kimtsa, ala-barshi idan ita ma ta fara sai ta biya ta abin da ta rigaya ta batar dangane da haka. Wannan shi ne masu lura da al’amura a Jihar Kaduna suka kira wayon a-ci wai an kori kare daga gindin dunya.
A daidai wannan lokacin makarantun firamare da yawa sun fara lalacewa saboda wasu ‘yan gyare-gyaren da suka wajaba a dinga yi musu ba a kuma yi ba, ga shi nan kuma kujerun zama da teburan almajirai sun kakkarye, ana bukatar a canja ko a sayi sababbi, kuma babbu kayayyakin aiki a makarantun, kamar allin rubutu bisa allo da dastar share rubutun da littafan da malamai za su yi aiki da su ko wadanda almajiran za su yi amfani da su. Dalili kuwa shi ne gwamnati ba ta fitar da kudi don samar da su.
Wannan ne ya sa aka shawarci Gwamna Nasir cewa maimakon ciyar da almajiran makarantun firamare da ya somo, kuma yana narkar da makudan kudi a kan haka, me zai sa ba zai yi amfani da kudin ba wajen kawar da matsalolin da ake tsananin fuskanta a makarantun, wadanda kuma ke hana malamai sakewa don koyarwa yadda ake so, su kuma almajiran makarantun ba su samun sukunin mayar da hankula kan abubuwan da ake koya musu? A’a gwamnati ba ta dauki wannan shawarar ba, ta fi damuwa da abincin da za a rarraba ma ‘yan makarantar, kuma da zarar sun gama cin abincin, to fa karatu ya kare ke nan, ba a sake samun damar shawo kan su don su natsu, su ci gaba da karatun
Amma maimakon gwamnati ta saurari waccan shawarar da kunnuwan basira sai ta bar makarantun na ci gaba da tabarbarewa, babu kayayyakin aiki, ba a kuma kulawa da gyaransu idan iska ko ruwan sama sun yi musu ta’adi. Haka nan aka yi ta tafiya kan ciyar da ‘yan makaranta har aka kai watanni takwas, ‘yan kwangilar ciyarwar na ta kosawa saboda ba a biyansu a kan kari, har sai da aka ce wai an kashe Naira miliyan dubu goma game da haka. To da yake an ce ta yaro kyau take ba ta karko, sai ga shi ba a kwace wa yaro garma ba, shi da kansa ya ga ba dama ya yar da ita, ya kuma kama gabansa. Gwamnatin Malam Nasir ba girma ba arziki ta yi watsi da batun ciyar da ‘yan makaranta bayan ta rigaya ta shagwabasu, ta koma gefe guda tana jiran gwamnatin tarayya ta biya ta kudin da ta sa kanta kashewa wajen ciyar da ‘yan makaranta. A can gefe guda kuma ga makarantu ba kayayyakin aiki, ba a fitar da kudin samarwa ko kuma gyaggyara su. Amma kodayake an ce an gyara kusan dari hudu daga cikin sama da dubu hudu da dari biyu da ake da su a jihar, ba a fayyace wuraren da aka yi gyaran ba, ba a kuma ce ko nawa aka kashe kan gyarar kowace makaranta ba. Iyakar abin da gwamnati ta yi ta yi shi ne shelar cewa gwamnatin da ta gabata ce ta bar makarantu suka lalace, domin cikin shekaru goma sha shida da suka shude wai ba abin da suka yi don alkinta su.
Akwai kuma batun dinka wa ‘yan makaranta rigunan zuwa makaranta da Gwamnatin Malam Nasir ta cika duniya da yare cewa tana yi, kuma daga bisani sai al’amarin ya balbalce, babu wani dalilin da aka bayar sa’ilin da aka daina dinkawa. An ce aikin dinkin kayan makarantar zai samar da aiki ga dubban matasa, amma ta yaya za a ce an samar wa telan da ya dade yana gudanar sana’arsa aiki don kawai an kawo masa dinkin wasu kayayyakin ’yan makaranta kalilan? Ai kowa ya ga balbela da farinta ya ganta. A Jihar Kaduna dai an sha ganin yadda gwamnatoci ke alkawarin samar da rigunan ’yan makaranta, suke kuma bugewa da nokewa, ba su iya cika alkawari. Haka ne ma Gwamnatin Muhammadu Namadi Sambo ta yi, bayan ta samar da su ga wasu makarantun cikin garin Kaduna guda uku, sai kuma ta gaza, daga nan ba ta sake waiwayar batun ba.
Wannan al’amari na gwamnatoci da ke daukar alkawarin aiwatar da wasu ayyukan inganta makaranatu, daga bisani kuma su kasa ci gaba da su, abin damuwa ne kwarai ga iyayen yara. Idan kuwa da matakan da gwamnoni ke dauka don inganta makarantu na yin tasiri ai da yanzu makarantun kudi a Jihar Kaduna sun zama tarihi, amma iyayen yara dai sun fi amincewa da su domin a can ne kwalliya ke biyan kudin sabulu, kuma ko ta wane irin hali ne iyayen yara za su kukuta su biya kudin makarantar ‘ya’yansu a can.