Ba a mugun sarki sai mugun bafade (2)
Da aka tambayi Malam Aminu Kano me ya koyo a Mulkin Soja? Ya ce da ‘yan jarida, sun koyo idan sun ga abu sai a hana su fada. karshenta aka yi wa Yakubu Gowon juyin mulki, Murtala Muhammad ya zama Shugaban kasa. Shehu Shagari bai fi wata uku da yin wancan magudi ba aka yi […]
Da aka tambayi Malam Aminu Kano me ya koyo a Mulkin Soja? Ya ce da ‘yan jarida, sun koyo idan sun ga abu sai a hana su fada. karshenta aka yi wa Yakubu Gowon juyin mulki, Murtala Muhammad ya zama Shugaban kasa. Shehu Shagari bai fi wata uku da yin wancan magudi ba aka yi masa juyin Mulki. Bacin Awolowo ya ce idan Shagari bai gode Allah ba da shekara hudu da ya yi yana mulki, ya ci gaba maimakon Soja ya dawo.
Ko da Sojan suka dawo Buhari ya zama Shugaban kasa, ashe amfani suka yi da shi, bayan wata 20 suka kawar da shi, suka rusa duk ci gaban da aka gina a Najeriya tun daga lokacin zuwan Turawa zuwa samun mulkin kai, har karshen Jamhuriyya ta Farko. Sojoji suka yi wa kasar rugu-rugu, har da Majalisar koli ta Soja (Supreme Military Council) sai da Ibrahim Badamasi Babangida ya rusa a matsayinsa na Shugaban kasa, ya zama shi kadai ne mai zartar da komai, sai da ya rusa komai, ya sa Alani Akinrinade ya kashe noman rani da na damina, da Hukumar Sayen Amfanin Gona (Marketing Board), ya sa Falae ya rusa darajar Naira, suka ciwo bashi daga IMF suka rika sayar da kadarorin gwamnati, yayin da ake sayar da mai ake ciwo bashi, ake sayar da kadarorin gwamnati, sannan talakawa suka shiga matsanancin talauci da ba su taba ganin irinsa ba.
Aka rusa Hukumar Lantarki ta kasa (NEPA) da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NITEL) da Kamfanin Jiragen Sama na Najeriya (AIRWAYS) da Hukumar Jiragen kasa ta Najeriya (RAILWAYS) da Masana’antar karfe ta Ajakuta (AJAOKUTA STEEL INDUSTRY) da Kamfanin Takin zamani na kasa (NAFCON) da Masakun Najeriya (TEdTILE INDUSTRIES) da Kamfanin bunkasa ci gaban Arewa (NNDC) da bankuna, inda suka mallaka wa kansu rijiyoyin mai da jiragen ruwan daukar mai; suka gina matatunsu na mai a wasu kasashe, bacin sun rusa matatun Najeriya.
‘Yan Kasuwa masu masana’antu da hakar ma’adanai da noma da kiwo suka zama matsiyata, komai yanzu ya zama mallakar masu mulki, daidai da masu tallan Pure Water na Naira biyar a bakin titi babu mai jarin sarowa, sai dai a dora masa talla idan ya sayar a ba shi lada, balle ’yan bumburutu. Duk kadarorin da suka sayar na gwamnati su ne dai suka saye, talakawa ba su da kudin saye ko biya. Wannan shi ne halin da Najeriya take ciki a halin yanzu.
Idan har da gaske muke neman CANJI, to sai mun yi damarar tunbuke duk abin da su IBB da wadanda suka biyo bayansu suka gina, mu sake sabon gini fill, tun daga ‘Foundation’, idan ba haka ba, tamkar rikakkiyar bishiya ce da ta yi saiwoyi can karkashin kasa, tsawon shekaru, a ce za a rika sare rassanta da sunan kasheta, da an yi ruwan sama sai ta sake yin toho da sababbin rassa. Tilas sai mun tumbuko bishiyar tun daga saiwoyinta, mun kayar da ita, mun faskara ta, ta bushe, mun kone ta kaf, sannan mu shuka abin da muke bukata na cigaban mu da kasarmu. Idan ba haka ba, yaudarar kanmu kurum muke yi.
Da wannan tunani na ci gaba da yunkurin hada kan Buhari da Atiku da Bafarawa suka ki, ko suka kasa ganewa. Lokacin da Muhammadu Buhari zai Sani Abacha Sani Abacha zai nada shi Shugaban PTF, gaba-gadi na ce ka da ya karba. karshenta da PTF din ya kawar da hankulan mutane ya yi ta sata. Sai da ya mutu ake ta babatun Abacha Loot….. Haka za mu jira sai Babangida da Abdussalami da Obasanjo sun mutu sannan a yi ta babatu a kan tasu barnar? Haba! Idan ma wata doka ce, tilas a canzata, tunda ba dokar Allah ba ce. Kasancewar masu mulki sun mallake duk arzikin kasar tun daga rijiyoyin mai zuwa bankuna da kamfanonin sadarwa da kadarorin gwamnati – gida da waje, kamfanonin gine-ginen hanyoyi da sauransu, ya zama kowane ne zai yi mulki sai yadda suka yi da shi. Saboda duk dukiyar kasar tasu ce, sun rabe a junansu, shi ya sa marasa hakurin cikin mu da marasa imani irin su da ba su raba da su ba, suka zama tsageru, ‘yan tawaye da kungiyar Asiri da Matsafa, da wadanda ba su yarda da Allah ba balle gwamnati.
Basa yin aiki da dokokin Allah balle na gwamnati, kowa yake yin abin da ya ga dama, masu fataucin kwayoyin sa maye suke cin karensu babu babbaka. Kayan abinci da ake shigo dasu rubabbu, cike da sinadarai da magunguna na jabu da wadanda suka dade da lalacewa.
Ko rance za a ciwo kudin da rukunin barayin kasa suka sace mana suka dankare a wasu kashashe ake rantowa, maimakon a kwato su baki daya. Akwai wajibcin tilas gwamnati ta kafa ‘RADDUL MUZALIM,’ kwatankwacin lokacin Umar bn AbdulAziz, ba sai an jira wani jami’in gwamnati ya bayyana abin da ya mallaka ba, a kafa kwamiti mai karfin sharia da zai bi diddigin duk abin da kowanne shugaba da mukarrabansa da jami’an tsaro da ma’aikatan sharia da sauran ma’aikatan gwamnati daga 1985 zuwa yanzu, har nan gaba, sai an tabbatar da duk abin da kowannensu ya mallaka, a binciki yadda aka yi ya samu idan ba mahaifansa ne suka mutu ya gajesu ba- a kwato mana kayanmu, a hukunta shi a bainar jama’a, hukunci mai tsanani kamar yadda Allah ya yi umarni, ba tare da kowanne bambanci ba. Shi ne zai magance kowanne irin tsageranci da kungiyoyin asiri da masu da’awa da ilimin Badili da suke cewa komai Halal ne babu Haram da masu satar mutane, matsafa da duk masu aikata kowanne irin laifi. Kamar yadda duk wani mulki ana yinsa a kan abubuwa biyar: Kare rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addini na kowanne dan kasa.
Alhaji Abdulkarim Daiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN),
Tsohon Shugaban kungiyar ‘Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Ayyukan Gona – Chamber of Commerce, Industry, Mines and Agriculture
08060116666, 08023106666.