Ba a mugun sarki sai mugun bafade (I)
Tun ba ni da wayo nake jin ana cewa, ba a mugun Sarki sai mugun Bafade, sai yanzu nake tunanin lallai wannan magana ko karin magana ta yi daidai da yadda na gani a kan Malam Aminu Kano da su Malam Adamu Chiroma da Umaru Shinkafi da Lema Jibrilu da Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar […]
Tun ba ni da wayo nake jin ana cewa, ba a mugun Sarki sai mugun Bafade, sai yanzu nake tunanin lallai wannan magana ko karin magana ta yi daidai da yadda na gani a kan Malam Aminu Kano da su Malam Adamu Chiroma da Umaru Shinkafi da Lema Jibrilu da Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar da Attahiru Bafarawa. Wanda na kasance sha wuya a tsakaninsu a kan kokarin hadin kan su, wanda rashin nasarar samun haduwar kan nasu ya jawo fadawar kasar hannun makiya. A karshe na zama sha wuyar masu mulki.
Da farko tun ina matashi Malam Aminu Kano ya taba dora mini nauyin dawo masa da jiga-jigan mutanensa su 10 da suka hada da Salihi Iliyasu da Abdussamad Iliyasu da Yusuf Ali, da M.T Waziri da Muhammadu Adamu da Malam Muhammadu Inuwa Dutse da sauransu. Kamar yadda Freedom Radio Kaduna suka yi hira da ni a kan tarihin Malam Aminu Kano, na yi musu bayani, bacin mutuwar Malam Aminu Kano na kasance cikin jiga-jigan mutanen Arewa da muka hadu muka je gurin Cif Obafemi Awolowo da sunan Concerned Citizens a kan kudiri 17 wadanda idan ya yarda za mu hadu mu kafa gwamnati tare da shi, kudurorin sun hada da:- (1) Kafa Bankin Musulunci da kuma (2) Mune za mu wakilta wanda zai zama mataimakinsa daga cikinmu. Bacin ya yi bincike game da bankin Musulunci ya sha mamaki, ashe akwai irin wannan tsarin a duniya, amma ake yin shirme? Bacin ya taba zama Ministan kudi lokacin Gowon, amma ya yarda shirme ake yi da – idan aka kwatanta da tsarin Bankin Musulunci.
Lokacin da ya gayyace mu karkashin jagorancin Malam Muhammadu Inuwa Dutse, muka zauna da shi da su Lateef Jakande, na yi masa wata tambaya, inda na ce, Cif ga shi ni ne kusan mafi karancin shekaru a wannan tawaga, amma an dora min nauyin zama kakakin tawagar da zan rika ma’amala da kafafen watsa labarai: Radio da Talbijin da Jaridu da Mujallu na Turanci da Hausa. To amma, ina da wata matsala da ta shafeka, ina ji mutanenmu suna cewa kana da kabilanci da nuna bambanci addini, wane bayani za ka yi min domin in kareka a gun masu irin wannan tunani? Sai Cif Obafemi Awolowo ya yi murmushi ya ce da ni, “My dear dayyabu, if your Sardauna is still alibe and came to my people to canbass for botes to become President of the Federal Republic of Nigeria, they may say the same thing to him, because Nigeria had started as regions and each and ebery one of us is assigned to his particular region, competing with one another. We are now talking about bringing all the regions under one of us; former Premiers of different regions.” Ma’ana:Da Sardaunan ku yana raye, idan ya taho wajen mutanena neman kur’ar su don zama Shugaban kasar Tarayyar Najeriya, irin haka za a fada masa, saboda Najeriya ta fara ne a masayin yanki-yanki, kuma kowanenmu yankin sa aka tura shi, inda suke gasa da juna. Yanzu muna bukatar hada wadannan yankuna wuri guda ne, a karkashin jagorancin dayan mu, wato tsofaffin shugabannin yankuna (Firimiya).
Ya kara da cewa bangarensa cikakken misali ne na Najeriya ta bangaren addini, yana so a tambaye su, idan yana nuna wa wasu bambamci, ya ce a dubi irin ci gaban da ya sama wa bangaren nasa, wanda idan ya samu iko zai ciyar da kowanne bangare haka, ya ce matarsa duk da kasancewar ta Kirista ta biya wa Musulmi takwas zuwa aikin Hajji da guzuri, kanwarsa ta Musulunta ta auri Musulmi, shi, Awolowo shi ne ya biya mata kudin aikin Hajji da guzuri.
Ya kara da cewa sai da shi Awolowo ya kafa Hukumar Jindadin Alhazai ta Musulmi da shekara biyu, sannan Sardauna ya je ya kwafa a gurinsu. karshe ba mu rabu ba sai da ya kira taron ’yan jaridu na duniya a Eko Hotel ya fada wa duniya cewa, da ya samu mulki zai fara da kafa Bankin Musulunci, muka zo Kaduna Darbar Hotel ya maimaita wannan jawabin. Muka hada shi da Makaman Misau, tsohon dan Majalisa a Jamhuriyya ta Farko ya zama mataimakin Shugaban kasa. Ni da sauran mu aka ba mu takarar Sanatoci na Arewa; ni ne na Kano ta Tsakiya, ana maganar shekarar1983. Har da tanadin wakilai na tarayya don shirin ko ta kwana. karshe aka yi magudin da ba a taba yin irinsa ba kafin lokacin, aka ce Shagari ne ya sake cin zabe ko’ina da ko’ina. Muka yi gagarumin taro a Abeokuta babban birnin Jihat Ogun da Awolowo, su Baba Tofe suka zo da cikakken bayanin irin magudin da aka yi, suna so a ba su dama su warware.
A gabana, ina kusa da Lateef Jakande, shi kuma yana kusa da Awolowo daga hagu, Makaman Misau yana daman Awolowo, sai Awolowo ya ce da su Baba Tofe ya san babu yadda za a yi a cinye jihohinsu balle gidansa, amma da zarar an ga ya yi yunkurin kwato hakkinsa, sojoji za su yi yunkurin juyin mulki.
Ya ce shi kuma da soja ya kwace mulki, gara Shehu Shagari ya ci gaba, inda ya kara da cewa duk lalacewar mulkin farar hula ya fi na soja, komai kyawun na soja. Idan ba a manta ba, Awolowo da Aminu Kano sun yi ministoci a Gwamnatin Janar Gowon, amma suka rabu dutse a hannun riga, da Gowon ya ce, maida mulki ga hannun farar hula sai illa masha Allah. Shi ne Malam Aminu Kano da Awolowo suka fice daga gwamnatin. Za mu ci gaba.
Alh. Abdulkarim Daiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN), Tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Ayyukan Gona- Chamber of Commerce, Industry, Mines and Agriculture
08060116666, 08023106666.