Ba a nuna kabilanci a Kungiyarmu – Baba Jede

Mataimakin Shugaban Kungiyar Kanikawa ta Kasa reshen Jihar Kebbi Actor Babajide ya ce, kungiyar ta tsere wa takwarorinta saboda rashin nuna kabilanci a tsakanin mambobin kungiyar. Actor Babajide, ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a ofishinsa da ke Birnin Kebbi. “Da a ce akwai kabilanci a wannan kungiya da babu yadda […]

Ba a nuna kabilanci a Kungiyarmu – Baba Jede

Mataimakin Shugaban Kungiyar Kanikawa ta Kasa reshen Jihar Kebbi Actor Babajide ya ce, kungiyar ta tsere wa takwarorinta saboda rashin nuna kabilanci a tsakanin mambobin kungiyar.

Actor Babajide, ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a ofishinsa da ke Birnin Kebbi.

“Da a ce akwai kabilanci a wannan kungiya da babu yadda za a yi Bayarabe dan Kudu maso Yamma irina ya zama Mataimakin Shugaban Kungiyar Kanikawa a nan Jihar Kebbi da ke Arewa amso Yamma, Arewar Arewa inda duk Hausawa ne. Shi ya sa nake kira ga jama’armu da suke cewa, ana kabilanci su daina fadin haka. Domin yawancin wadanda suka zabe mu tun shekara hudu da suka gabata, da kuma yanzu da aka sake wani sabon zaben Hausawa ne ’yan asalin Jihar Kebbi kuma ba wani abu ne ya kawo haka ba, sai zaman lafiya da kuma yadda kungiyarmu ta kafu a kan akidu masu kyau ba na kabilanci ba, kuma wannan yana daga cikin abubuwan da suka sa muka yi wa sauran kungiyoyi fintinkau,” in ji shi.

Mataimakin Shugaban ya ce, asalin kafa wannan kungiya tasu shi ne don kanikawan Jihar Kebbi su taimaki junansu, ya ce, za su yi iyakar kokarinsu wajen ganin sun taimaki junansu. Ya kuma ce, ba abin da ya kara sa shi jin dadi irin yadda ’ya’yan kungiyar suka hada kansu suka zabi kabilu daban-daban da za su jagoranci kungiyar, akwai Yarbawa da Ibo da kuma Dakarkari da Hausawa.

Saboda haka ya yi kira ga dukan ’ya’yan kungiyar su ba su goyon baya da hadin kai don ganin sun samu nasarar kudirorin da suka sanya a gaba.

Sai ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kebbi a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta tallafa wa ’ya’yan kungiyar da kudade domin su kara dogaro da kansu.

Ya yi godiya ga jami’an tsaro na Jihar Kebbi a kan hadin kai da suke samu daga gare su a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.