Ba a sake wa tuwo suna
Ita dai karya tamkar tusa take, ba ta boyuwa ko da a ruwa aka buga ta. Haka nan kazafi da shaci-fadi akan wani al’amari bai tabbata, domin kuwa dukkansu dangin karya ne, komai zurfin raminta babu wuya a kure shi. Sa’ilin da jama’a suka dukufa cikin kogin bakin cikin abubuwan takaicin da suka faru da […]
Ita dai karya tamkar tusa take, ba ta boyuwa ko da a ruwa aka buga ta. Haka nan kazafi da shaci-fadi akan wani al’amari bai tabbata, domin kuwa dukkansu dangin karya ne, komai zurfin raminta babu wuya a kure shi. Sa’ilin da jama’a suka dukufa cikin kogin bakin cikin abubuwan takaicin da suka faru da Janar Muhammadu Buhari da kuma Sheikh dahiru Bauchi a kwanakin baya, sai ga wasu mutane marasa takawa sun dukufa yin karairayin da za su karkata yatsun zargi zuwa wasu wurare can na daban da kuma neman ci gaba da bata sunan Janar Buhari da yi masa bi-ta-da-kulli, ba domin komai ba kuwa sai don tsananin kiyayyar da suke yi masa wacce ta hadassa muguwar adawar da suke yi da shi.
Da ma Bahaushe ya ce idan mutum bai kaunarka, to ko cikin ruwa ka fada sai ya ce ka tayar da kura. Shi ya sa jim kadan bayan kai harin da aka yi wa Janar Buhari a kusa da gadar Kawo, jami’an tsaro suka hanzarta kame wani mutum da ya batar da kamannu cikin kayan mata, wanda jama’a suka danke sa’ilin da suka yi zarginsa da kokarin sulalewa bayan ya tafka ta’asa, sa’anan bayan zuwan sojoji, sai suka yi awon gaba da shi.
Shi dai wannan mutum jama’a da yawa a lokacin sun tabbatar da cewa tababbe ne, ya kuma dade a wannan wuri, yana fama da wannan lalurar. To shi ne daga bisani bayan an yi bincike, an same shi da wayoyin hannu masu yawa a cikin wata jakar mata, sai babban hafsan hulda da jama’a na rundunar mayakan Najeriya, Manjo-Janar Olukolade ya tara manema labarai ya fayyace masu cewa dubun wanda ya tsara kai hari ga Janar Buhari ta cika, an kuma kame shi. Jaridun Najeriya da kuma na duniya da yawa sun nunnuna hotunan wannan tababben a matsayin jagaban maharan da suka dirkaki Janar Buhari a Kaduna.
To amma da yake mutum na nasa ne, Allah kuma na nasa, amma na Allah shi ne hakkun, sai ga mahaifiyarsa, Malama Zubeida Yusuf ta bayyana wa manema labarai a Kaduna cewa wannan mutum, mai suna Mansir, dai danta ne da ke zaune a layin Aminu Kano, Mando, wanda ya dade yana fama da matsalar tabin hankali wacce ke sanya shi yana shiga da yin wasu dabi’u irin na mata. Baicin haka nan kuma yayan Mansir, watau Ibrahim Yusuf ya kara jaddada abin da mahaifiyarsu ta fada game da shi, daidai kuma da yadda Malam Hassan Maishayi a Kawo ya kara tabbatarwa. Wani mazaunin Kawo, Malam Sirajo Suleiman ya yi karin haske game da halin da aka cafke Mansir, ya kuma ce sa’ilin da aka kame shi ba a same shi da komai dangane da irin abubuwan tayar da bom ba. To amma watakila jami’an tsaro na da tasu hujjar ta dabam, kuma wacce ta gamsar da su cewa wannan tababben da ake kira Mansir ne ummul-haba’isin kitsa harin da aka kai wa Janar Buhari. To idan nan gaba sun gurfanar da shi a gaban alkali, za mu ji hujjojinsu na yin haka, kuma gaskiya za ta yi halinta.
Wannan al’amari ya daure wa talakawan kasar nan kai, musamman ma ganin yadda jami’an tsaro tun daga nan Kaduna ba su tsaya sun binciki kowane ne Mansir Yusuf ba, alhali kuwa ga shi nan kusa da su, baki da hanci, suka aike da al’amarinsa hedkwatarsu, a can ma aka sake kwatawa, aka kuma gaggauta bayar da sanarwar cewa an kame wanda ya kitsa harin da aka kai wa Janar Buhari. To saurin me ake yi game da haka da za a kasa natsuwa, a yi cikakken bincike a tsanake, ko kuwa ana gudun kada a ce jami’an tsaron ba su yi aikinsu ne ba, har suka daki jaki, suka bar taiki, bayan isarsu wurin da aka aikata ta’asar, jim kadan bayan afkuwar haka? Lokaci ne dai zai tabbatar mana da amsar wannan tambayar.
Amma abin da ya fi wannan takaici da ban mamaki shi ne yadda takadarin yankin Neja Delta, Asari Dokubo ya hakikance cewa wai ba ‘yan ta’adda ba ne suka nemi halaka Janar Buhari, wai shi da kansa ne ya kitsa kutungwila mai kama da haka don tsabar kwadayin shugabancin kasar nan. Yanzu idan da jami’an tsaro za su turke shi ya kawo hujjojinsa game da haka zai iya? Irin wadannan kalaman ne kuma suka fito daga bakin babban jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar PDP, Mista Olisa Metuh, wanda ya ce Janar Buhari na kokarin wanke kansa ne daga zargin ta’addancin da duk duniya ta san yana da hannu a ciki don yana neman suna da kuma tagomashin jama’an da za su tausaya masa idan ya tsaya zabe.
Ya fadi haka ne kuwa sa’ilin da yake mayar da martani ga furucin Janar Buhari game da bayyanar gaskiya bisa zargin da ake yi wa jam’iyyar APC da shugabanninta na haddasa ta’addanci a kasar nan, domin kuwa ga shi nan ana zaton wuta a makera sai ta tashi a masaka. To amma komai za su ce game da harin da aka kai wa Janar Buhari sun makaro, domin ita gaskiya ba ta boyuwa, kamar yadda ba a sake wa tuwo suna.