‘Ba a samar da hukumar tantance yawan mazauna birnin Ikko don haraji ba’

Gwamnatin Jihar  Legas  ta yi bayanin ta samar da  hukumar  tantance  yawan  mazauna  jihar  ne saboda  gane yawan jama’ar da ke kowanne  sashe, amma ba domin karbar haraji daga mazauna jihar ba.Da take wa taron manema labarai jawabi a ofishinta, shugaban hukumar, Madam Yinka Fashola  ta ce makasudin samar da hukumar  shi ne domin gano […]

‘Ba a samar da hukumar tantance yawan mazauna birnin Ikko don haraji ba’
‘Ba a samar da hukumar tantance yawan mazauna birnin Ikko don haraji ba’

Gwamnatin Jihar  Legas  ta yi bayanin ta samar da  hukumar  tantance  yawan  mazauna  jihar  ne saboda  gane yawan jama’ar da ke kowanne  sashe, amma ba domin karbar haraji daga mazauna jihar ba.
Da take wa taron manema labarai jawabi a ofishinta, shugaban hukumar, Madam Yinka Fashola  ta ce makasudin samar da hukumar  shi ne domin gano yadda  gwamnati  za ta  rarraba albarkatun da take da shi ga jama’ar  jihar da kuma gano bukatunsu a kowane lokaci, don gwamnati ta ji dadin tafiyar da ayyukanta na samar da ababen more rayuwa a kowane yanki.
Ta ba da misali da idan wata unguwar ko yankin babbar bukatarsu ruwa ne, kila kuma gwamnati  ta ba su asibiti, amma idan ta san jama’ar da ke kowane yanki  za ta iya hasashen girma ko adadi ko kuma tsarin abin da za ta ba su na more rayuwa.
Madam Fashola ta ce muddin ba samun adadin mutanen kowane yanki gwamnati ta yi ba, to  zai yi wahala ta gane yadda  za ta sarrafa dan abin da ke hannunta domin jin daddi jama’arta, “Haka kuma  gwamnati na iya amfani da wadannan bayanai domin samar da  aikin yi, kana ta kuma taimaka wa masu tunanin zuwa wani sashe na jihar domin saka hannun jari ko dai daga nan cikin gida Najeriya ko kuma daga kasashen waje”. Inji ta.
Shugabar hukumar ta ce ana gudanar da rajistar ne ta kai-tsaye ko kuma ta na’urar kwamfuta, a kowace karamar hukuma, ko kuma ofisoshin koyar da sana’o’i da kuma ofishin kungiyoyin matasa da ke cikin jihar, kuma ba a karbar ko anini illa bayanai.
Madam Fashola ta roki mazauna jihar ta Legas da su mara wa hukumar baya domin ta cimma burinta na ganin yadda za ta  tafiyar da  shirinta na samar da ababen more rayuwa cikin tsari, wanda ba shi da wata nasaba da karbar haraji.