…Ba a san kashe-kashe ba a Zamfara a lokacina – Shinkafi
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi ya ce har suka bar mulki a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2011, jihar ba ta san wani abu na kashe-kashe ba, sai dai a ji labari a wasu jihohi ko kasashen waje. Tsohon Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema […]
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi ya ce har suka bar mulki a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2011, jihar ba ta san wani abu na kashe-kashe ba, sai dai a ji labari a wasu jihohi ko kasashen waje.
Tsohon Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau, bayan zargin da aka yi cewa gwamnati mai ci ta gaji kashe-kashen ne daga wurinsa.
Alhaji Mamuda Shinkafi ya ce idan jama’ar Jihar Zamfara za su iya tunawa, gwamnatin Abdul’aziz Yari ta ce tana kashe Naira miliyan 600 a kowane wata kan tsaro, shi a lokacinsa Naira miliyan 40 kawai yake kashewa a harkar tsaro, kuma a cewarsa ko hannunsa kudin ba su shigowa, suna shigewa ne hannun mai bada shawara kan harkar tsaro, wato Manjo Bala. Ya ce kuma a lokacinsa ana kulawa da duk DPO da ke cikin jihar da motocinsu, kuma ana ba su Naira dubu 50 duk wata domin shan mai a motocinsu saboda ko-ta-kwana.
Mamuda Shinkafi ya kara da cewa duk shugabannin kananan hukumomi ana ba su kudnsu da ake amsowa daga Gwamnatin Tarayya a zamaninsa, don haka gwamnatinsa ta ba su umarnin kulawa da jami’an tsaro da suke kananan hukumomin jihar.
Shinkafi ya ce rashin bai wa kananan hukumomi kudinsu ya taimaka wajen jefa al’ummar jihar a cikin mawuyacin hali, domin a cewarsa kudi ba su zagayawa hannun jama’a balle su samu walwala, kuma hakan abin yake cikin kasuwanni da ma’aikatun gwamnanti, don haka ya zargi gwamnatin jihar da sakaci kan salwantar rayukan al’ummar jihar.
Alhaji Mamuda ya ce akwai lokacin da a karamar Hukumar Zurmi, bayan an gaya wa ’yan sanda faruwar wani lamari sai aka nemi Naira dubu 10 don a sanya mai a mota aka rasa. Ya ce wannan abin bakin ciki ne, don haka ya ce a ce gwamnati tana kashe Naira miliyan 600, amma ba su magance matsalar tsaro ba.
Game da zargin da ake masa ya amshi kudi daga matan jihar don za su yi kiwon awaki, ya ce, “Ba mu ce a karbi ko Naira ba a wajen mata, a lokacin wannan hukumar a karkashin danburam su ne suka karbi kudin da ake magana a kansa ba su kai Naira miliyan 10 ba, don ba su wuce Naira 500 zuwa 1000 aka karba, idan ka yi lissafi za ka samu kusan mata dubu 100 aka karbi kudinsu, wanda wannan zai yi wahala, shi ya karba kuma daga bisani sai ya bar PDP ya koma ANPP.”