Ba a san maci tuwo ba…
Tun daga lokacin da aka rantsar da sabon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sai ’yan adawa suka shiga soki-burutsu da furta kalamu marasa tushe balle makama, wadanda daga sauraronsu za ka san cewa akwai nau’in hassada ko wauta a game da su, domin kuwa bai kamata ba a ce irin wadannan maganganun na firfito wa daga […]
Tun daga lokacin da aka rantsar da sabon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sai ’yan adawa suka shiga soki-burutsu da furta kalamu marasa tushe balle makama, wadanda daga sauraronsu za ka san cewa akwai nau’in hassada ko wauta a game da su, domin kuwa bai kamata ba a ce irin wadannan maganganun na firfito wa daga bakunan wadanda suka san abin da suke yi ba.
Yawancin irin wadancan maganganun ana danganta su ne da bubuwan da Shugaba Buhari ya aikata, ko wanda bai aikata ba, da wadanda aka gasgata ya furta amma aka yi za’ida wajen yi wa jama’a bayaninsu, da kuma wadanda bai furta su ba, amma aka yi masa kazafi game da su. Sau da yawa za ka ji ‘yan adawa da kuma ‘yan kazallaha na mulmulo kalamu masu nauyi, suna jefa wa Shugaba Buhari, wasu na cewa wai ya aike da sunayen wadanda zai haskaka da mukaman ministoci har su talatin da shida ga hukumar EFCC, amma an gano cewa uku ne kawai daga cikinsu suka tsallake siratsin hukumar, kuma saura guda talatin da uku duk ba su cancanta ba, an zubar da su, saboda tsabar ha’inci ko rashin aminci da inganci.
Irin karerayin da suke saurin kullawa ke nan, kuma kafin a tafi ko ina sai a taras cewa kanzon-kurege ne kawai, babu kanshin gaskiya a ciki. Haka nan kuma an sha cewa Shugaba Buhari na nuna tsabar kabilanci da gwada bambancin bangaranci a cikin ‘yan mukaman da ya babbayar bayan hawansa mulki, amma babu mai magana game da muhimman mukaman wasu muhimman hukumomin gwamnatin tarayya sama da talatin, da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya bobbora ‘yan kabilarsa da kuma wasu zaratan magoya bayansa daga shiyyar Kudu-maso-Gabashin kasar nan. Idan aka yi la’akari da kyau za a fahimci cewa Shugaba Buhari ya cike guraban wadannan mukaman da ake masa kwarmato akai ne da wadanda ya gasgata gaskiyarsu da rikon amanarsu, domin kuwa ayyukan da za su yi sun jibanci al’amuran tsaron lafiyarsa ne da kuma hidima, walau a fadarsa ko kuma a ofishinsa.
Baicin haka nan kuma wasu gogaggun ‘yan adawa na zargin Shugaba Buhari da biye son zuciya wajen binciken da yake yi, domin kuwa ya fi matsawa akan gwamnatin da ta shube da shugabanninta da kuma manyan jami’anta, sa’annan kuma ya ja layi, ya ce ba zai binciki sauran gwamnatocin da suka shube ba illa ta Shugaba Jonathan kabai. Shugaba Buhari dai ya ce binciken da zai yi ba shi da wani gefe, ba kuma zai kyale wanda duk aka dadumo, hanunsa dumu-dumu da laifi ba, ko shi wane ne kuma ko ban wa zai banbana kubarsa. An kuma san Shugaba Buhari na da zafi, domin tun farkon farawa ma sai da ya tattara ‘yanuwa da abokansa na arziki da ahalin gidansa, ya yi masu gargabin kada waninsu ya kuskura ya yi takama ko alfahari da shi, domin idan ya bebo ta da zafi, to ya tabbatar a bakinsa zai jefa, ba ruwansa, kuma kada ya ce ya san shi.
To duk a bar ta wadancan batutuwan! Akwai wani batu mai tayar da hankali da ban tsoro, wanda kuma zai iya haddasa gagarumar fitgina a fagen siyasa, har ma a halin yanzu ya fara tayar da kura. Wasu marasa takawa da kaunar zaman lafiya, sun ari bakin Shugaba Buhari, sun ci masa albasa, ko kuma a ce tafarnuwa, suna bi lungu-lungu, rariya-rariya, kwararo-kwararo suna ta barbaba labifin hadisi.
‘Yan adawa, manya da kanana, sun dukufa ka’in-da-na’in wajen nunawa duniya cewa Shugaba Muhammadu Buhari tudun mulki guda zai ci, ba zai sake tsaya wa ba a shekarar 2019, idan Allah Ya kai mu. Wannan lamarin ne ya haddasa bakar siyasar da ake yi a halin yanzu, kuma a sakamakon haka ne aka kasa samun zaman lafiya da lumana a jam’iyyarsa ta APC, domin kuwa akwai wadanda suka zaku da ganin ya kau, domin su haye halifarsa.
To amma wannan duk zuki-ta-malle ce, ko kuma a ce kanzon kurge, domin hadisin nasu labifi ne, babu wani amini ko makusancin Shugaba Buhari da aaka taba ji ya ruwaito haka, babu kuma wanda zai iya saba laya ya ce ya ji Shugaba Buhari ya furta haka, ko ya kawo hujjar kulla yarjejeniyar haka da wasu abokan siyasarsa. Saboda haka nan dai ana nan a gidan jiya, domin ba a san maci tuwo ba sai idan miya ta kare. Shugaba Buhari dai jama’a ne suka jajirce cewa sai shi, kuma a dukkan lokutan da yake fitowa takara talakawa ne ke masa taguwar malum-malum ta mutunci, su ne kuma ke tarairayarsa, su kuma tabbatar da nasarar da yake nema.
To a yanzu ba shi da ta cewa game da takara, sai abin da jama’a suka ce. Idan har ya biya masu bukatarsu yadda suke bukata, sai kawai su sabunta masa wa’adinsa, idan kuma shi ne da kansa ya nemi ya huta, su amince da haka. Baicin haka nan kuma ai a yanzu ba a fara hankoron tsayawa zabe ba, ko wane iri ne kuwa, duk da cewa a Najeriya a kullum za ka ga ana gudanar da harkokin siyasa gadan-gadan kaman gobe za a yi zabe, ko da kuwa washegarin zaben gama-gari ne.
A tsari dai irin na dimokurabiyya akan bai wa shugaban da ke bisa karaga ne daman zabin ci gaba ko akasin haka, a lokacin da aka fara share fagen yakin neman zabe. To sai wadanda suka zazzaro takubbansu don yakin neman zabe, tun a wannan lokacin, su hakura, su mayar da su kube, su guji zuga-zugin ‘yan shan kai, wadanda za su kai su su baro. Batun sake takarar Shugaba Buhari ko akasin haka a shekarar 2019 ya dogara ne a gare shi, domin dabara dai takan rage wa mai shiga rijiya ne.