Ba a san maci tuwo ba…(1)

Hausawa na cewa wanda duk ya ce ruwan wani ba zai tafasa ba, nasa ko dimi ba zai yi ba, domin kuwa hana wani hana kai ne. Ana iya cewa irin abin da yanzu haka ke faruwa, ke nan tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Chibuike Rotimi Amechi da tsohon abokinsa, Nyesom Wike, wadanda aka gansu […]

Ba a san maci tuwo ba…(1)
Ba a san maci tuwo ba…(1)

Hausawa na cewa wanda duk ya ce ruwan wani ba zai tafasa ba, nasa ko dimi ba zai yi ba, domin kuwa hana wani hana kai ne. Ana iya cewa irin abin da yanzu haka ke faruwa, ke nan tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Chibuike Rotimi Amechi da tsohon abokinsa, Nyesom Wike, wadanda aka gansu a rana sakamakon tsagewar bangwayensu, har kadangarun bariki suka kurkurda. Siyasa ce dai ummul-haba’isin haka, kuma ita ce ta bayar da dama ga ‘ya’yanta su aikata masha’ar da a halin yanzu take wahalar da wadanda suka yi hakan domin su.

Da farko dai tsohon shugaba kasar nan Goodluck Jonathan ne ya fara yin shukar da ta haddasa bakar gaba da kiyayya a fagen siyasar Jihar Ribas, don takura wa Gwamna Amaechi na wancan lokacin a kokarin da yake yi na ganin ya kawo yanayin da zai tabbatar an dora jam’iyyarsu ta PDP bisa tsarin dimokuradiyya wajen gudanar da harkokinta na cikin gida, abin da ya kai har kawunan gwamnonin jam’iyyar ya rabu gida biyu , shi Amaechi na jagorantar guda, tsohon Gwamnan Jihar Pilato , Sanata Dabid Jona Jang kuma na shugabantar gwamnonin da ba su da rinjaye a kungiyarsu. Tsohon Shugaba Jonathan ya tayar da Nyesom Wike, wanda ke rike da mukamin Minista da Amaechi ya sanya aka ba shi domin ya taka wa Rotimi Amaechi burki, saboda an fahimci cewa, yana neman watsawa garin jam’iyyar PDP kasa. Daga nan ne fa aka shiga takun saka tsakaninsu, har hakan ya ba matar Goodluck Jonathan damar shiga cikin al’amarin, ta yi ruwa, ta yi tsaki a ciki, tana kuma tozarta gwamnan jihar, watau Amaechi, har sai da ta kai ta taba ci masa kwala a bainar jama’a.
Daga karshe dai Rotimi Amaechi, tare da wasu ‘yan uwansa gwamnonin jam’iyyar PDP guda hudu, waskewa suka yi daga jam’iyyar, suka tsunduma cikin ta APC, kuma daga bisani sai ga shi nan Amaechin ya zamanto Babban daraktan yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari, kuma hakan ya bakanta wa ‘yan yankinsa na Kudu- maso-kudu, musamman ma wadanda ke nuna matukar kiyayya ga Arewa da daukacin abubuwan da suka shafeta, kuma bayan an kai ga nasara sai suka sake daukar karan tsana suka dora wa Amaechin, don kada Shugaba Muhammadu Buhari ya haskaka shi da wani mukamin da zai kai shi ga kasaitar da za ta dakile yunkurin PDP na karfafa matsayin jam’iyyar a Jihar Ribas da kuma yankin Kudu-maso-gabas gaba daya.
Wannan ne ya sa daukacin sanatocin shiyyoyin kudu-kudu da kuma na kudu-maso-Gabas suka dage wajen kawo cikas a Majalisar Dattijai don kada hakar da ake yi don nada Amaechi minista ta cimma ruwa. To amma an ce shi ramin mugunta ba a gina shi da zurfi don kada mai hakin ya fada cikinsa, to amma jam’iyyar PDP rijiya gaba dubu ta haka don ta jefa Rotimi Amaechi a ciki, sai ga shi bayan ta gama hakin wasu daga cikin gwamnonin da take ji da su matuka, wadanda kuma suka gwanance wajen assasa siyasar bambancin addini da neman ‘tayar da zaune tsaye’ a kasar nan, cikinsu har da jigonsu, watau Sanata Godswill Akpabio tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom suka afka ciki, kowannensu ya gamu da gamonsa. Ana cikin zaman juyayin wannan al’amarin, watau ana kukan targade, sai kuma ga karaya ta samu, kotun sauraren karar zaben Gwamnan Jihar Ribas ta soke zaben da aka yi wa babban makiyin Rotimi Amaechi, wato Nyeson Wike, an kuma bayar da umurni a sake zabe nan da watanni uku masu zuwa.
Dangane da haka ne jama’a da yawa suka yi ta rausaya rawa da wake-wake a daukacin Jihar Ribas, suna ta cewa kada Nyeson Wike ya yi kuka da kowa sai da kansa, domin kuwa kaikayi ne ya koma kan mashekiya.To, amma an tabbatar da cewa Nyesom ba zai dauki wannan batu sako-sako ba, zai daukaka kara kamar yadda tsarin shari’ar kasar nan ya tanada, kuma wajibi ne idan har zai je kotun gaba to tilas ne ya yi hakan cikin kwanaki 21 daga lokacin da aka yanke hukuncin. Idan kuma ba zai yi ba, sai ya sauka daga mukamin gwamna, shugaban majalisar jihar ya rike mukamin gwamna har ya zuwa lokacin da za a yi zaben.
Amma da yake a yanzu an yi wata ‘yar kwaskwarima ga dokokin zabe, saboda haka nan daukaka kara a zaben gwamna ba zai tsaya ga kotun daukaka kara ba kadai, kamar yadda ake yi a da, za a iya zarcewa har zuwa kotun koli, idan har hukuncin da aka bayar a kotun daukaka kara ba ta gamsar da wanda ya kai kara gaban kotun, wato Gwamna Wike ko kuma wanda aka yi karar, Chief Dakuku Peterside na jam’iyyar APC ba. A nan ma an bayar da kwanaki 21 ne ga mai kara ko wanda akai kara don shigar da maganar gaban kotun kolin.Idan kotun koli ta tabbatar da cewa kotun daukaka kara da kuma kotun sauraron kararrakin zabe ta Jihar Ribas sun tabbatar an tattafka magudi, ta kuma yanke hukunci daidai da yadda wanda ya kai kara ke son a yi, to shi ke nan fa sai ta ba mai gaskiya gaskiyarsa, wanda kuma aka kayar ya yi ta kwafa, yana Allah-Ya-isa. Amma idan har ba ta ce ga wanda ya yi nasara ba game da karar, sai ta warware zaben, a kuma sake sabo cikin watanni uku, yayin da Babban Jojin Jihar zai rantsar da shugaban majalisa, ya ja ragamar gwamnati, sai su kuma su koma ga jama’arsu, su ci gaba da yakin neman zabe har ya zuwa lokacin kada kuri’a.
Ta haka ne za a tabbatar da cewa an bi tsarin shari’a yadda ya kamata,kuma har sai jama’a sun sake yanke hukunci, wanda kuma ya sha kasa ya yi ta yin sababi da su. Amma sai dai sai a yi a hankali domin kuwa wadannan matakan da za a dauka na zuwa kotun daukaka kara da kotun koli da kuma yiwuwar sake zaben na cike da hadarin gaske, domin komai na iya faruwa, kuma hakan na iya yin muguwar illa ga hadin kan al’umomin Jihar Ribas, ko kuma agazawa ko ruguza tsarin dimokuradiyya a jihar. Yanzu dai ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare.