Ba a soke biyan kudin jarrabawar ’yan sakandare a Nasarawa ba – Kwamishina
Hajiya Rakiya Ajuji Abubakar ita ce Kwamishinan Ilimi ta Jihar Nasarawa, a tattaunawarta da wakilinmu ta ce gwamnatin jihar ta fara sallamar shugabannin makarantun firamare da na sakandare da ke karbar kudin Ya ya batun ilimi kyauta a jihar nan da wadansu iyayen yara ke zargin cewa har yanzu suna biyan kudin makaranta?Da farko dai […]
Hajiya Rakiya Ajuji Abubakar ita ce Kwamishinan Ilimi ta Jihar Nasarawa, a tattaunawarta da wakilinmu ta ce gwamnatin jihar ta fara sallamar shugabannin makarantun firamare da na sakandare da ke karbar kudin Ya ya batun ilimi kyauta a jihar nan da wadansu iyayen yara ke zargin cewa har yanzu suna biyan kudin makaranta?
Da farko dai kamar yadda aka sani batun ilimi kyauta tun a shekarar 2004 ne aka sanar da bayar da shi kyauta a makarantun firamare da kananan sakandare na kasar nan. Kuma da zuwan Gwamna Umaru Al-Makura karagar mulki bai yi wata-wata ba wajen aiwatar da shirin a jihar nan, kamar yadda aka sani Gwamna mutum ne mai son ilimi. Ya kuma zo a lokacin da iyayen yara suke fuskantar mayuyacin hali da galibinsu ba sa iya biya kudin makarantar ’ya’yansu. Shi ya sa ya aiwatar da shirin tun a wa’adin mulkinsa na farko. Bayan wannan Gwamnan ya kuma ba da umarni da zuwansa cewa a rage kudin kungiyar Iyaye da Malamai (PTA) da iyayen yara ke biya a makarantun firamare da na sakandare. Saboda haka ina tabbatar maka cewa har yanzu da muke magana iyaye ba sa biya kudin makarantar ’ya’yansu a jihar nan, wato makarantar firamare da karamar sakandare. Gwamnatin jihar nan ba ta taba tunanin dakatar da shirin ba kuma insha Allahu ba za ta yi haka ba.
Wadansu iyayen yara ’yan firamare da sakandare na kuka cewa har yanzu suna biyan kudin makarantan ’ya’yansu. Ya ya gaskiyar lamarin?
A gaskiya mukan samu wannan korafi daga iyayen yara inda suke cewa wadansu shugabannin makarantun firamare da sakandare suna tilasta su su biya kudin makaranta da na PTA da sauransu. Shi ya sa a matsayinmu na jami’an gwamnati a bangaren ilimi muka dauki kwararan matakai wajen gudanar da bincike a kan batun. Kuma binciken da muka gudanar a wasu makarantu mun gano cewa lallai wadansu shugabannin makarantu suna ci gaba da karbar kudin makaranta da wasu kudi daga wurin iyayen yara ba tare da dalili ba, bayan gwamnati tana biyansu albashi kuma ta gargade su cewa su daina yin haka. Shi ya sa muka dauki matakin sallamar duk wani shugaban makarantan firamare ko na sakandaren gwamnati da muka same shi da laifi. Kawo yanzu mun sallami shugabannin makarantu da dama wadanda muka same su da wadannan laifuffuka. Kuma za mu ci gaba da gudanar da bincike a sauran makarantu don sallamar duk wani shugaba ko malamin da ya karbi kudin makaranta a cikin makarantun gwamnati.
Me ya sa gwamnatin jihar ta dakatar da biya wa daliban sakandare kudin jarrabawar NECO bayan ta soma aiwatar da shirin?
Batun biya wa dalibai kudin jarrabawar NECO da gwamnatin jihar nan ta soma aiwatarwa ba ta soke shi kwata-kwata ba ne. Wato mun dan dakata ne na wasu lokuta bayan mun fuskanci matsala. Matsalar kuwa ita ce yadda wadansu iyayen yara daga wasu jihohi ke yin amfani da damar suna turo ’ya’yansu jihar nan domin su amfana da shirin musamman jihohin da ke makwabtaka da mu da suka hada da Benuwai da Filato da Neja da Taraba har ma daga Abuja inda dalibai da dama daga wadannan wurare suke zuwa don su amfana da karamci. Ka ga gwamnatin jihar nan kadai ba za ta iya biya wa dalibanta kudin jarrabawa ta kuma biya daliban da ke zuwa daga waje ba. Shi ya sa muka dakatar da shirin na wani lokaci. Abin da muke yi yanzu shi ne tantance daliban mu zakulo ainihin ’yan jihar nan. Bayan mun kammala sai mu cigaba da shirin. Saboda haka ina so in yi amfani da wannan damar wajen bayyana wa al’ummar jihar nan cewa ba a soke shirin kwata-kwata ba, da zarar mun kammala wannan tantancewar za mu ci gaba.
Jihar nan daya daga cikin jihohin da malaman manyan makarantunsu ke tafiya yajin aiki a kai-a kai, me ke kawo haka?
Haka kuma kamar yadda ka sani jihar ce ta biyu a jihohin kasar nan da ke karbar kudin kaso mafi kankanta daga Asusun Tarayya. Saboda haka abin da zan ce a nan shi ne rashin isasshen kudi musamman wanda ake fuskanta yanzu a kasa baki daya ya shafi bangaren ilimi musamman harkokin manyan makarantu. Shi ya sa a koyaushe muke zama da malaman manyan makarantu na jihar nan muna rokonsu cewa su yi la’akari da haka. Ka ga batun karin albashi bai shafe su ba, haka kuma ba a rage musu albashi ba, ya kamata su dubi kokarin gwamnati a wannan bangare. Kuma ina so in yi amfani da wannan dama in yi kira ta musamman ga ’yan kwadago a jihar nan baki daya su yi hakuri da halin da muka samu kanmu a yau. Su gane cewa lamari ne da ya shafi kasa baki daya, su tuna cewa gwamnatin jihar nan ne ta fara aiwatar da shirin karin albashi ga ma’aikatanta a kasar nan. Su rungumi kaddara kafin lokacin da tattalin arziki zai inganta komai ya daidaita.