Ba a taba bai wa Arewa damar tsayar da wanda take so ba – Sabuwar Kungiyar Arewa

A ranar Asabar da ta gabata ce wadansu fitattun ’yan siyasa daga Arewa suka kaddamar da wata kungiyar  maido da tasirin siyasar Arewa. kaddamar da kungiyar wanda ya gudana a dakin taro na tunawa da Shehu Musa ’Yar’aduwa da ke Abuja, ya gudana ne a karkashin jagorancin Alhaji Tanko Yakasai, kuma kungiyar ta sha alwashin […]

Ba a taba bai wa Arewa damar tsayar da wanda take so ba – Sabuwar Kungiyar Arewa

A ranar Asabar da ta gabata ce wadansu fitattun ’yan siyasa daga Arewa suka kaddamar da wata kungiyar  maido da tasirin siyasar Arewa.

kaddamar da kungiyar wanda ya gudana a dakin taro na tunawa da Shehu Musa ’Yar’aduwa da ke Abuja, ya gudana ne a karkashin jagorancin Alhaji Tanko Yakasai, kuma kungiyar ta sha alwashin maido da martabar siyasar Arewa ta hanyar kafa kwamitoci da sakatariyar da aka nada Dokta Umar Ardo a matsayin sakatarenta.

Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP, Alhaji Bello Halliru, wanda ya fara jawabi a taron, ya ce a lokacin da aka tsayar da Cif Obasanjo takara a 1999, ba mutanen yankinsa na Kudu maso Yamma ne suka zabe shi ba, Arewa ce.

Ya ce a bayan da Obasanjo ya kare mulki aka maido da shugabancin zuwa Arewa, ba a kyale ’yan Arewa su zabi wanda suke so ya yi musu takara ba, wadansu ne suka tsayar da shi. “Makasudinmu a nan shi ne idan har an ce Arewa za a ba mulki, to a kyale su ’yan Arewa su zabi wanda suke ganin zai yi wa kasa adalci mu tsayar da shi,” inji shi.

Haka tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce hadin kai muhimmin al’amari ne ga mutanen Arewa musamman a irin wannan lokaci da wasu abubuwa ke kara ta’azzara. 

Ya ce “Muddin ana son mai do da martabar siyasar Arewa, to wajibi ne a hada kai, sannan a gano bakin zaren matsalolin da suke addabar yankin don magance su, idan kuma ba haka ba, to akwai yiwuwar a rika bi ana karkashe ’yan Arewa har cikin gidajensu kamar yadda na fada shekara 15 da suka gabata, ga shi kuma abin da ke faruwa ke nan a yanzu.”

“A kullum sai dai Arewa a rika maganar Sardauna a baki kawai, amma ba a yin abin da ya dace, abin da ya dace shi ne kowa ya zamo Sardauna ta hanyar rungumar halayyarsa domin a tafi baki daya, wanda Allah Ya ba girma a bi shi, maimakon hassada da zagon kasa,” inji shi.

Ya ce, “Dukan sauran sassan Najeriya kamar na Yarbawa da Ibo kawunansu a hade yake, amma ban da na ’yan Arewa.” 

Taron ya samu halartar jiga-jigan ’yan siyasar Arewa da suka hada da Paul Wampana, Sanata Nasiru Mantu, Buba Galadima, Ghali Na Abba, Babangida Aliyu, Idris Wada, Inna Chiroma, Zainab Maina da sauransu.