…Ba a taba bin tsarin karba-karba a Jihar Filato ba – Ayuba Pam
Mista Ayuba Pam shi ne mai ba Gwamnan Jihar Filato shawara kan harkokin watsa labarai, ya ce ba a taba bin tsarin karba-karba a Jihar Filato ba: Aminiya: Me za ka ce kan zargin da wasu suke yi cewa harkokin siyasa ba sa tafiya a Jihar Filato duk da cewa zaben badi ya gabato?Ayuba Pam: […]
Mista Ayuba Pam shi ne mai ba Gwamnan Jihar Filato shawara kan harkokin watsa labarai, ya ce ba a taba bin tsarin karba-karba a Jihar Filato ba:
Aminiya: Me za ka ce kan zargin da wasu suke yi cewa harkokin siyasa ba sa tafiya a Jihar Filato duk da cewa zaben badi ya gabato?
Ayuba Pam: Ban san dalilan da suka sa wasu mutane suke zargin cewa wai harkokin siyasa ba sa tafiya a jihar nan ba. Idan muka lura jihar tana cikin wani yanayi na kamun kai, ba wai rashin fitowar mutane su yi siyasa ba. Wato a Jihar Filato muna kamun kai ne kan hare-haren da ake kaiwa a kowanne lokaci da kuma rikice-rikicen da ake samu a wasu kauyukan jihar. Mutanen jihar nan sun fi mayar da hankali kan tsaro da sasanta juna. Kuma idan ka dubi bangaren siyasa babu shakka ana yi, domin idan ka duba a halin yanzu ana shirye-shiryen zaben kananan hukumomi wanda za a gudanar a ranar 25 ga wannan wata. Dangane da zaben kasa baki daya kuwa wanda Hukumar INEC ta fitar da jadawalin zaben, mai yuwuwa ne a jihar nan ba za ka ga ’yan siyasa suna yawo suna yakin neman zabe ba, ba wai don ’yan siyasar ba sa nan ba ne. A Jihar Filato ko kana cikin Jam’iyyar PDP ko baka ciki ko kana siyasa ko ba ka siyasa, za ka san cewa muna cin gajiyar mulkin dimokuradiyya, ta hanyar ayyukan raya kasa da Gwamna Jonah Jang ke yi don bunkasa rayuwar al’ummar jihar nan. Don haka kowa yake addu’ar Allah Ya kawo wanda zai ci gaba da irin wadannan ayyuka na bunkasa rayuwar al’umma. Saboda haka ake taka-tsantsan ba a sauri a kan wannan al’amari.
Aminiya: A tsarin da aka yi an nuna cewa wannan karon yankin Kudancin Jihar nan ne zai fito da dan takarar Gwamna a wannan karo, to amma ana zargin Gwamnan Jang yana kokarin sake dauko dan takara daga yankin Arewacin Jihar inda ya fito, ina gaskiyar wannan batu?
Ayuba Pam: Wadanda suke wannan magana, zan ce kusan hankalinsu ya rabu da jikinsu. Domin idan ka dubi tarihin siyasar Jihar Filato babu lokacin da aka taba cewa za a bi tsarin karba-karba a kujerar Gwamnan Jihar. Duk wadannan yankuna uku wato Filato ta Kudu da Filato ta Tsakiya da Filato ta Arewa, a duk lokacin da zaben Gwamna ya zo sukan fito baki dayansu su shiga takara. Babu wanda ya taba bar wa wani. Idan an taba yin haka, su fito su fada mana. Misali a zaben 1979 da marigayi Cif Solomon Lar ya zama Gwamnan ’yan takara daga yankin Kudu da Tsakiya da Arewacin jihar duk sun fito takara. Amma Cif Solomon Lar wanda ya fito daga Kudancin Jihar ya ci zabe ya zama Gwamna. Bayan haka a zaben 1993 Cif Fidelis Tafgun wanda shi ma daga yankin Kudancin Jihar nan ya fito ya ci wannan zabe ya zama Gwamna. A wancan lokaci ’yan takara sun fito daga yankin Arewa amma Cif Tafgun ya ci zabe. Bayan haka a 1999 da aka zo zaben Gwamna Cif Joshua Dariye wanda daga yankin Tsakiyar Jihar Filato yake ya fito takara a lokacin ma Cif Fidelis Tafgun wanda ya fito daga yankin Kudu da Jonah Jang daga yankin Arewa. Amma Cif Joshua Dariye wanda ya fito daga yankin Tsakiyar Filato ya ci zabe ya zama Gwamna.
Aka sake zuwa zaben shekara ta 2007 ’yan takara daga yankunan Kudanci da Tsakiya duk sun fito takara, ba su ce a bar wa Filato ta Arewa ba, saboda ba su taba yi ba. Don haka wane dalili ne za su ce bai kamata mutanen yankin Filato ta Arewa su fito takarar kujerar Gwamnan Jihar Filato a zaben badi ba?
A wane lokaci ne aka taba yin zama aka kulla yarjejeniya cewa yau wannan yanki, gobe wancan yanki, jibi wancan yanki? Ai ko adashen mata muka dauki misali, za mu ga cewa wadda ta dauki na karshe ita ce take fara daukar sabon zubi. Don haka babu dalilin da zai sa mutane suka rika kawo abin da ba shi a cikin sharadi.
Idan ana son abi wannan tsari na karba-karba a nan Jihar Filato, sai a zo a zauna a tsara yadda za a yi. Ta yadda duk yankin da aka ce an bar masa babu wani dan takara da zai fito daga wani yankin, duk ’yan takarar sai su fito daga wannan yanki da aka bar wa. Idan wannan yanki ya gama wa’adinsa sai a koma wani yanki. Amma idan ba a yi haka ba, aka bari kowa ya je ya yiwo farauta ya kawo gida sai a ce wai kai kada ka fita farauta, idan aka yi haka ba a yi adalci ba. Kuma ba wannan magana ake yi ba, domin Gwamna Jang bai gaya wa kowa cewa daga yankin Arewa za a fito takarar Gwamnan Jihar Filato a zaben badi ba. Don haka ko ka je ka yi masa magana zai ce maka bai san wanda zai gaje shi ba, domin dole ne a nemi fuskar Ubangiji.
Duk wanda zai gaji Gwamna Jang ya san cewa yana da babban aiki a gabansa. Domin ayyukan da ya yi a jihar nan idan ba an samu mutum mai natsuwa da hankali ba, za a koma ’yar gidan jiya. Abin da mutanen Jihar Filato suke tsoro ke nan.