Ba a tashi daya aka kashe Murtala ba – Odilansa
Daga nan sai muka samu tallafin sojojin da ba sa cikin ‘yan tawaye suka fito gadan-gadan da motar yaki. Suka kwashe mu suka kai mu dakin ajiye gawa a asibiti, sai sanyin dakin da kuma warin maganin hana gawa wari ya dame, ni sai na fara na daga hannuna. Sai wani ma’aikaci ya kira likita […]

Daga nan sai muka samu tallafin sojojin da ba sa cikin ‘yan tawaye suka fito gadan-gadan da motar yaki. Suka kwashe mu suka kai mu dakin ajiye gawa a asibiti, sai sanyin dakin da kuma warin maganin hana gawa wari ya dame, ni sai na fara na daga hannuna. Sai wani ma’aikaci ya kira likita ya sanar da shi,aka sa abin kunne aka ce ban mutu ba. Daga nan aka dauke ni zuwa Barikin Dodan, sannan aka kai ni asibiti a kan titin Awolowo. (Kuka)
Aminiya: Watanni nawa ka yi a asibiti?
Odali: Na yi watanni shida a asibiti. Da na fito sai na koma aiki, na yi aiki da Janar Adeneju da Raji Rasaki, kafin aka ba shi mukamin Gwamnan Legas, da kuma Janar Tanko Ayuba.
Aminiya: Shin ko an taba ba ka lambar girmamawa ta kasa ko makamincinta?
Odali: A’a ba a taba ba ni ba.
Aminiya: Yanzu a ina kake zaune?
Odali: Ina zaune a gidan haya, a gida mai daki biyu, a kusa da cocin Mountain of Fire a Maraba da ke cikin Jihar Nasarawa kusa da Abuja. Sannan ina aiki da dan Janar Murtala Ramat Muhammad, watau Riskuwa Murtala Muhammed a Abuja.
Aminiya: Yaushe ka bar aikin soja?
Odali: Na yi murabus ranar 31 ga watan Disambar 1999 da mukamin Samanja.
Aminiya: Akwai danka da ke aikin soja?
Odali: A’a suna karatu a jami’a a yanzu.