Ba a tsayar da ranar auren Zango da Nafisa ba

A ’yan kwanakin nan ana ta yada jita-jitar cewa a ranar 12 ga Satumba, 2015 za a daura auren fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan Adam A. Zango da jaruma Nafisa Abdullahi, sai dai majiyoyin da ke kusa da jaruman sun tabbatar wa Aminiya cewa zancen ba ya da tushe balle makama.Masu yada jita-jitar sun ce […]

Ba a tsayar da ranar auren Zango da Nafisa ba
Ba a tsayar da ranar auren Zango da Nafisa ba

A ’yan kwanakin nan ana ta yada jita-jitar cewa a ranar 12 ga Satumba, 2015 za a daura auren fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan Adam A. Zango da jaruma Nafisa Abdullahi, sai dai majiyoyin da ke kusa da jaruman sun tabbatar wa Aminiya cewa zancen ba ya da tushe balle makama.
Masu yada jita-jitar sun ce fitaccen Furodusa Abdul Amart ne ya sanar da batun auren a shafinsa na Instagram da kuma Twitter, sai dai a hirar da Aminiya ta yi da Furodusan ya musanta batun, inda ya ce shi ma ya girgiza matuka da aka ce wai ya sanar da labarin auren Zango da Nafisa.
Ya ce, “Duk da cewa ina da kyakkyawar dangantaka da jaruman da ake magana a kansu, amma ban yi magana da kowa bisa wannan batu ba, sannan ina tabbatar muku wannan magana ba ita ba alamarta.”
Furodusan ya ja hankalin mutane kan su guji yada jita-jita domin hakan ba abu ne da zai haifar wa al’umma da mai ido ba.
Wata majiya da ke kusa da Adam A. Zango ta ce suna sane da irin jita-jitar da ake yadawa a kan Zango da Nafisa, amma har zuwa yanzu ba a sanya ranar aure ba duk da cewa akwai soyayya mai karfi a tsakanin jaruman.
“Tabbas Nafisa a watan Yuni ta bayyana soyayyarta ga Adam Zango a shafin Instagram, sannan Zango ya amince, kuma dangantaka tsakaninsu ta kara danko, amma har zuwa yanzu babu batun sanya ranar daura aure,” inji majiyar.
Wata majiya da ke kusa da Nafisa ta bayyana wa Aminiya cewa duk da cewa jarumar a yanzu ba ta da wani buri face ta auri Zango, amma har yanzu babu batun sanya rana balle a ce wai 12 ga wannan wata.
“Abin da mamaki, a ina masu yada jita-jitar suka ji wai a ranar 12 ga Satumba za a daura auren jaruman? Wannan batun ba ya da tushe balle makama. Duk da cewa Nafisa ba ta da wani buri face ta auri Zango, amma ba a sa rana ba,” inji majiyar.