Ba a yanke shawara kan kasafin kudi ba – Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta ce ba a yanke shawara kan kasafin kudin bana ba. Ministan Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma ya bayyana haka a shekaranjiya Laraba bayan taron Majalisar Zartarwa na awa hudu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.Ana ci gaba da takaddama a tsakanin bangaren zartarwa da majalisa kan kasafin, inda wakilan majalisar suka […]
Gwamnatin Tarayya ta ce ba a yanke shawara kan kasafin kudin bana ba. Ministan Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma ya bayyana haka a shekaranjiya Laraba bayan taron Majalisar Zartarwa na awa hudu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Ana ci gaba da takaddama a tsakanin bangaren zartarwa da majalisa kan kasafin, inda wakilan majalisar suka yi canje-canjen da suka sanya Shugaban kasa ya ki sanya hannu a kai.
Udoma ya ce ya maimaita cewa suna tattaunawa a kan kasafin a lokacin da manema labarai suka tambaye shi kan kasafin da kuma yaushe za a kawo karshen batun da kuma ko bangaren zartarwa ya maya wa majalisa da kasafin.
Majalisar ta umarci Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya gana da Shugaban kasa Buhari don warware takaddamar.
Ana zargin majalisa da shigar da wasu “bakin” ayyuka har 386 da za su ci Naira biliyan 12.6 a kasafin Ma’aikatar Gona. Kuma Dogara ya ce sakamakon wannan takaddama za su duba wuraren da ake da matsala don samun maslaha.