Ba a yi wa Fulani adalci – Miyetti Allah

Aminiya ta tuntubi shugaban Miyetti Allah na kasa Alhaji Muhammad Kiruwa, Ardon Zuru, domin jin ta bakinsa game da zargin da ake yi wa Fulani na aikata ta’addanci:   Aminiya: Me ya sa duk wani ta’addanci da aka yi sai a ce Fulani ne?Kiruwa Zuru: Akwai abubuwan da suke tada hankali da masifa da suke […]

Ba a yi wa Fulani adalci – Miyetti Allah

Aminiya ta tuntubi shugaban Miyetti Allah na kasa Alhaji Muhammad Kiruwa, Ardon Zuru, domin jin ta bakinsa game da zargin da ake yi wa Fulani na aikata ta’addanci:

g Shugaban Miyetti Allh na Yobe, Malam Aliyu Usman BiririAminiya: Me ya sa duk wani ta’addanci da aka yi sai a ce Fulani ne?
Kiruwa Zuru: Akwai abubuwan da suke tada hankali da masifa da suke faruwa ga al,ummar fulanin Nijeriya, musamman masu kiwo, yadda manoma da sauran al’umma suka sanya Fulani da makiyaya a gaba. Muna kuma ganin tunda ‘yan Jarida ba a can daji suke ba kuma cikin Fulanin nan ba, sai ya zama abubuwan da suke faruwa ga Fulani kashi biyar cikin 100 ba a sani.
Idan bafulatani bai kare kansa da dabbobinsa da ‘ya’yansa da zuriyarsa ba, gaba daya za a kawar da su daga doron dasa. Idan kuma ya tashi kare kansa, daya daga cikin wadanda suka kawo masa hari ya mutu, sai ka ji an ce wai Fulani ‘yan jahadi ko Fulani ‘yan ta’adda sun yi kisa, duk duniya sai a fada musu. Ana ganin kamar Fulani wadansu mutane ne da kawai duk lokacin da suka ga dama sai su dauki makami su kasha mutane.
Idan kuka bi tarihin abubuwan da suka faru a baya, irin dimbin fulaninmu da aka kashe aka kuma kwashe shanunsu, kamar a johohin Nasarawa da Kauru a jihar Kaduna ga kuma na jihar Binuwai a kauyen Agatu da Guma da Logo, a Kwara, Asa da Moro da Pategi, sai na Taraba a karamar hukumar Ibbi da jihar Filato a Wase da Mangu da Barikin Ladi da Riyom da kuma rikicin Agasha da ke karamar hukumar Homa dake jihar Binuwai.
Sai ga shi kwanan nan an ji an kashe mutane an kone masu gidaje   a Enugu, tun kafin a yi bincike sai aka fara yayatawa cewa Fulani ne suka aikata wannan ta’asa, yaya za a ce wai a Enugu Fulani su za su tada wata fitina? Ka san da jin haka akwai lauje cikin nadi, sai ga shi bayan an aikata wannan ta’adi da kwana biyu  sai aka kai wa fulaninmu hari, inda aka kashe masu shanu guda 80 ba gaira ba dalili, ka ga wannan cin amana ne da zalunci.

Aminiya:  Kusan yawancin fashi da makamin da ake yi a wasu sassan arewacin kasar nan ana danganta shi ga Fulani ne, me za ka ce?
Kiruwa Zaru: A kasar nan babu wata kabila ko al’umma da za a ce ba za iya samun musu laifi a cikinta ba, kuma mun san cewa duk wuraren da ake yawan samun rikice-rikice tsakanin Fulani makiyaya da manoma za a samu laifuffuka suna hab aka awuraren, saboda duk al’ummar da aka barta ta fara shiga rikici har aka fara zubar da jini, doka ba za ta zama komai a wurinsu ba. Kuma saboda asarar da mutane suka yi, inda wasu suka rasa iyeyensu, wasu ‘ya’yansu, wasu matansu, za a samu imani ya ragu a wajen irin wadannan mutane. A irin wannan hali sai mutane su shiga take doka, a ga fashi  ya yi yawa. Misali bafulatani na da shanu kamar 50 ko 100 an zo an auka masa an kwashe su an tafi da su, ya dawo ba ya da saniya ko daya kuma bai iya kasuwanci ba, wani sai zuciyarsa ta gurbace ya shiga wani hali, kamar ya zama barawo ko dan fashi, kuma idan rikice-rikice suka faru makamai sukan shiga hannun mutane, kuma idan akwai makamai a hannun mutane, babu yadda za ka hana aikata laiffuka, kamar yadda ake gani a kwanakin baya a jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina da Filato.
Ban ji dadin yadda ake cigaba da dora wa Fulani laifin tada zaune tsaye ba, alhalin kuma sune sukafi tafka asara, Fulani ne ake dora wa laifin da wasu suka aikata. A sace mana dabbobi, wanda a wasu lokuta idan aka yi rashin sa’a, makiyayanmu su rasa rayukansu a kokarin kare dukiyoyinsu, ka ga mu muka fi kowa asara, amma abin mamaki mu ake dora wa laifi a kowane lokaci.

Aminiya: Ta yaya kake ganin za a magance wannan matsala?
Kiruwa Zuru: Hanya guda daya ce, a yi wa jama’a adalci, duk wanda ya aikata laifi ko wane irin kabila ne doka ta hau kansa, kuma kafin a hukunta mutum ya zama wajibi an tabbatar da shi ya aikata laifin.

Aminiya: A karshe mene ne sakonka ga gwamnati?
Kiruwa Zuru: muna kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi 36 har da Abuja, su kafa kwamitoci domin su bincika abubuwan da ake yi wa Fulani,  musamman ma makiyaya a kasar nan. Idan har an tabbatar da babu inda aka taba bafulatani kafin ya kai hari, za mu ba da goyon baya da taimako kan yadda za a hukunta duk bafulatanin da ya aikata laifi, saboda ya zama darasi ga saura.

Bashir Lawal Zakka a Birnin Kebbi

Aminiya: Me ya sa duk wani ta’addanci da aka yi sai a ce Fulani ne?