Ba a yin kudi a aikin jarida sai arziki – Nasiru Maiwada

Alhaji Nasiru Maiwada, daya ne daga cikin ’yan jaridar da suka shahara da ya yi aiki a gidajen rediyon BBC da Muryar Amurka da Rediyon Kaduna. Aminiya ta gana da shi, inda ya bayyana gwagwarmayar da ya sha, da wasu al’amarura da suka shafi rayuwarsa: Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?Nasiru Maiwada: An haife ni a […]

Ba a yin kudi a aikin jarida sai arziki – Nasiru Maiwada
Ba a yin kudi a aikin jarida sai arziki – Nasiru Maiwada

Alhaji Nasiru Maiwada, daya ne daga cikin ’yan jaridar da suka shahara da ya yi aiki a gidajen rediyon BBC da Muryar Amurka da Rediyon Kaduna. Aminiya ta gana da shi, inda ya bayyana gwagwarmayar da ya sha, da wasu al’amarura da suka shafi rayuwarsa:

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?
Nasiru Maiwada: An haife ni a 1942, a Unguwar Fayamasa da ke Malumfashi. Na fara neman ilimi a makarantar allo a wurin Alhaji Balarabe Maidinki, yayan mahaifina Alhaji Maiwada. Na yi kamar izifi 15, ina zuwa ina yin boko. Da safe a tafi boko da yamma wajen La’asar a tafi akalato karan hura wutar makaranta da daddare mu yi karatun allo. Sai a 1954, da muka je jarrabawa, a da jarrabawa sai ka tafi Katsina, a zo da mota daga En’e, a kwashe ku daga garuruwan hakimai; mu nan Malumfashi makaranta daya ce, ta kofar Fada da yanzu ake kira Firamren Dudi. Sai a dauko ’yan kankara da ’yan Funtuwa da ’yan Bakori ku tafi Katsina. Ma’aikatar ilimi ta lardi. A lokacin aji daya zuwa hudu ake yi a Elemantare. Ba jarrabawa ake yi ba, tsattsame wasu daga cikinku da aka san suna da kokari a aji maza kawai ake yi a kai Katsina, su zauna su yi jarrabawa. To da muka ci jarrabawa a Malumfashi mu 10 ne; kadan da zan iya tunawa su ne: Yakubu Jibrin da ake kira Yakubu Joker, tsohon mataimakin shugaban hukumar shige da fice. Sai dan uwansa Ibrahim Jibrin, muna ce da shi Iro Bolo. Adamu Yanzu; sai Lawai dandayi; sai Salisu Fiyo; sai Marigayi Lawal Nono.
Da muka ci jarrabawa muka je Kankiya muka dasa aji biyar zuwa bakwai a Babbar Firamare. A 1957, aka yi jarrabawa muka ci, muka tafi Katsina, a cikin ajin A da B aka dauki wasu suka tafi Kwalejin Horon Malamai (TTC). A lokacin duk a Arewa daga Katsina sai Ilori sai Bauchi sai Maru a Jihar Sakkwato ake da TTC. Sai a dauki wadanda suka fi tsawo a ce su tafi TTC, in kun ci fa. ’Yan madaidaita masu kopkari da kanana da suka ci sai a kai su sakandaren da ake kira Probincial Secondary School, Katsina. To da aka zo, sai aka ga ba mu da tsawo, kuma mun wuce yara ’yan tsaka-tsaki, sai aka rika kiranmu ’Yan taka-kir. Yaya za a yi da mu, sai aka ce, ai mu ma muna da basira; lokacin Allah Ya jikan rai, Alhaji Jabiru Abdullahi su Garba Kaita ne manya a Ma’aikatar Ilimi ta Katsina, suka ce za mu yi amfani da mu, a bar mu, mu yi shekara muna koyarwa, in mun kai shekara sai mu sake jarrabawa, domin sai ka ci jarabawa. Sai muka zo Katsina muka yi koyarwa ta shekara daya, amma kafur aka fara kai ni. Sai na zama karamin malami na wani malami Alhaji Halilu Kandarawa (Baban Nura Khalil da ya tsaya takarar Gwamna). Shi malamin Larabci ne a lokacin ajin duka bai fi biyu ba. A cikin dalibaina akwai Alhaji Aminu Bello Masari (dan takarar Gwamna a APC). Shi ya sa idan Masari ya gan ni cikin taro sai ya ce kun ga malamina, sai in ce kai bari mana, sai ya ce, ‘to ba zan fadi ba?’ Da shekara ta cika, sai aka ce mu tafi Katsina, mu 12, muka dauki jarrabawar zuwa TTC. A cikin mu 12, mu biyu kawai aka dauka; ni da Abdu Dankama aka ce Bauchi za mu je. Lokacin nan mota da wuya, ga hanya babu kyau. Muka tafi Bauchi a 1960 zuwa 1962 (Grade III da II), a takaice aka ce za mu yi kwas din malami mai daraja ta uku, inda muka yi shekara biyu, saboda mun yi koyarwa ta shekara daya. Don haka aka zabge mana shekara daya. Kuma koyarwa a aji, wani darasi da ake bayar da shaidar karatu a kansa. Cikin mu 25 da muka zauna jarrabawa a Bauchi, mu hudu kadai muka samu shaidar koyarwa a Jihar Arewa.
Na samu wata matsala, wato a cikin darussan da aka jero a manhajar karatu guda tara ko 12; sai na fadi Adabin Ingilishi, al’amarin ya yi matukar ba ni mamaki, saboda ina da kokari a Adabin da shi kansa Ingilishi, amma Lissafi bai ba ni mamaki ba, dama ba ni da kokari wajen lissafi; sai dai in na takarkare nakan samu rabin maki.
Na dawo gida na ci gaba da koyarwa, sai aka aiko mini da takarda cewa in koma Bauchi, in sake yin jarrabawar darussan da na fadi. Na koma na zauna jarrabawar; na ci Adabin Ingilishi da Ingilishi, amma Lissafin nan ya kakare. Aka mayar da ni kafur na zama shugaban makarantar Firamare saboda na taba koyarwa a can, lokacin ina karamin malami. A kafur shekara daya na yi, akwai wani malami a Firamaren Tunau (Malumfashi) an tada shi, sai aka ce na dawo na zama shugaban makaranta.
A wancan zamanin makarantun duka uku ne, daga Dudi ta cikin gari sai Galadima, sai Tunau. Daga nan sai Fatahu Abdullahi, Allah Ya jikanshi, ya bar aikin malanta, ya tafi aikin banki, shi ne Hedimasta a Galadima, sai aka kai ni Galadima. Idan aka kai ka Galadima kamar an daukaka ka ne, domin ana ganin kimarka ta fi ta sauran shugabannin makarantun Firamare. Na je, na kama, Fatahu Abdullahi daga banki, sai ya wuce BBC Landan. Ni kuma da jin ya wuce Landan, sai na ce, ashe dan Grade II yana iya zuwa BBC?
Aminiya: Yaya aka yi ka samu aiki da gidan Rediyon BBC Landan?
Nasiru Maiwada: A Galadima na yi shekara biyu sai na ga cewa, duk lokacin da kake hedimasta kana so ka ga yaranka suna ci gaba. Sai na iske wani irin kidahumin aji, ba matan ba, ba mazan ba; ko karatun ne ba su so? Ka san yaranmu da, sai uba ko uwa su ce in ka je makaranta kada ka yi karatu. Wannan abu sai ya sanya yaranmu suka ci baya, har ta kai ga ba mu samun sakamako mai kyau. Ga shi kowane shugaban makaranta so yake a ce cikin yaransa 30, 20 sun samu sakamako mai kyau. Abin ya yi ta damuna, ashe ni ban gane ba, wadanda na baro kafur, wadanda ba su ci jarrabawa ba, sai na yi ta ganninsu a ma’aikatu, Kano ne, Jos ne, duk sun samu aiki, sai na ce yaya haka? Ashe ita cin jarabawa ta Firamare, ba wai wadanda suka ci su ne kawai za su ci gaba ba. Sai haushi ya kama ni na rubuta takardar barin aiki, saboda ga matsin lamba daga iyayen yara, ga damuwa daga hukumar ilimi ga damuwa daga sarakunan da ke garin, tunda su ke kawo maka yaran, wato da masu unguwanni da sauransu. A lokacin muna matasa ban wuce shekara 20 da doriya ba. Sai na ce hidimar ta yi yawa, dama na ga an buga a jarida ana neman sakatare kuma manaja na kungiyar Tallafa wa Manoma ta Funtua Cooperatibe Society a Funtuwa, wato kungiyar gama kai ta masu saye da sayarwa na auduga da gyada. To, suna zaman kansu ne, amma gwamnati tana aiko da wani jami’in daga ma’aikatar ciniki da kasuwanci. Wannan ma’aikacin gwamnati ne da zai zo ya zauna don ganin yadda ake tafiyar al’amura, sai suka dauke ni aiki, na bar malanta, wannan ya auku ne a 1969.
Takardar ta kawo mishikila, da aka kai ofis Jabiru Abdullahi, ko ya tafi kasashen waje ne, ya shiga cikin wuta sosai, da ya dawo ya ji an ce na yi ritaya. Ya yi mamaki, saboda a lokacin ba wai wasa ka yi ba, in makaranta ta lalace a lokacin nan, irinmu sai a ce mu je can mu gyara. Haka ka yi wa kafur, akwai wani Ibrahim Nadabo, shi aka kai wurin, ya ki zama, wai ta yi masa kauye. Farkon zuwana, sai da aka tattaro yara, wasu na gona, wasu na can daji suna cin ’ya’yan itace. Na ce, a’a, yaya za a ce makaranta da safe babu yara. To haka aka yi ta fama, Maigarin dan Galadinaman kafur ya taimaka mini.
A nan Funtuwa ma, sai na ga yaya ne, domin ka san malamin makaranta bai saba da cuku-cuku ba. Kuma harka ce ta kudi, sai ina jin tsoro, saboda ni daga alli sai rula sai littafi, amma yanzu an zo an sa kudi a hannuna, yaya zan yi da su? To shi wannan jami’i da aka kawo daga Kaduna shi ne kudi ke hannunsa. Sai na ce da jami’in da Alhaji Dauda Mani ni ba zan rike kudi ba. Domin ’yan kasuwar da ake bai wa kudi su yi cinikin gyada da auduga, sukan haifar da asara, wato su rage kudin; idan an kirga kudinsu jaka, sai a ga babu kaza. Sai aka ce, ai shike nan ni zan kai su kotu. Sai na ce, kotu, aka ce ‘eh.’ To ni duk ban san cuku-cukun da ake yi ba. Sai shugaban wurin ya kira ni ya ce, ai ba wani abu za ka yi ba, Nasiru in ka je, kai ke wakiltar wannan ma’aikata, shi mai gabatar da kara shi zai karanta duk laifuffukansu, sai a tattara a tambaye ka, a ce haka ne? Sai ka ce “eh.” Iyakar abin da za ka yi ke nan. Sai na ji karfin jiki. Da aka ci gaba, sai na ji irin wannan cuku-cukun ya dame ni. Ran nan kawai ina karanta jaridar Nigerian Citizen, a yanzu tamkar a ce Daily Trust, ta Hausarsu Gaskiya Ta Fi Kwabo, kamar yadda Aminiya take jaridar Hausa. Aka buga masu neman aiki a BBC a jaridar, inda aka nuna cewa ana neman ’yan shekara 30 zuwa 31, amma in mutum ya wuce haka ba a so.
Da ma kamar na sani, sai na ci gaba da karatun gida a Kwalejin Rapid Result College daga Landan ke aiko mini da littattafan karatu a fannonin Tarihi da Labarin kasa da Ingilishi da Nazarin dabi’un dan Adam. Cikin albashina nake aika musu da kudin. Idan suka aiko da littattafai, sai su ce ka karanta daga shafi kaza zuwa kaza, lokaci kaza za mu aiko da jarrabawar gwaji da za ka yi. Idan aka aiko maka da jarrabawa, ka yi, ka sa cikin ambulan, ka aika musu.
To ina cikin aikin, sai na ji dai ban gane ba, ana rika tsorata ni. Domin akwai wani Hakimi da muka kai masa ziyara cikin dare, lokacin muna zagaya kauyuka, don karbar kudin auduga da gyada. Da muka ce wurinsa, aka ce ranka ya dade an kawo sabon manaja, sai ya ce, wancan fa, kun kore shi ko? Sai ya ce kai ma ka yi hankali. Ka yi hankali yaro, kai ma za su kore ka, ana dariya, amma hankalina ya tashi. Da na ga wannan tallar neman aiki ta BBC, sai na ce, bari in rubuta. To kafin BBC su aiko, ita wannan ma’aikata ta Cooperatibe Kaduna, su ma an gama yaki sun aiko a 1971, cewa Ingila ta bayar da guraben karo karatu, bai fi wata ukku-uku ba; kowa ya bayar da manajansa za a kai shi Ingila, za a yi wannan karatu a wani gari wai Legbrough. A wannan garin, cibiyar hukumomin gama-kai suke. To, ni ban sani ba, sai Hamidu Yahaya, shi ne jami’i a ma’aikatar ciniki da sana’o’i da ya zo Funtuwa ya same ni a kan tebur, sai ya ce, kai me kake yi a nan, bayan an bayar da sunanka za ku tafi Ingila? Sai na ji gabana ya fadi ras! Ya ja ni muka shiga wajen wani jami’i, sai ya ce da shi, ofisa, yaya Malam Nasiru ba ku ga takardarsa ba ne? Ya ce, wallahi ba mu gani ba. Sai ya ce, to, lokaci ya kure, maza ka je, ka dauko kayanka in sanya ka a mota, mu koma Kaduna, a je a yi maka gwajin lafiya sai mu ba ka takarda da tikitin da za ka tafi .

Cigaba a shafi na 25

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu