Ba a yin kudi da aikin jakadanci, sai dai sanin mutane – Jakada Salisu
Jakada Salisu Umar shi ne mukaddashin jakadan Najeriaya a kasar Tanzaniya, a tattaunawar da ya yi da jaridar Aminiya a kasar ta Tanzaniya ya bayyana riba da rashin ribar aikin jakadanci. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Tun yaushe aka dawo da kai aiki a wannan kasa, kuma ko ya ka ga kasar? Jakada: Yanzu […]

Jakada Salisu Umar shi ne mukaddashin jakadan Najeriaya a kasar Tanzaniya, a tattaunawar da ya yi da jaridar Aminiya a kasar ta Tanzaniya ya bayyana riba da rashin ribar aikin jakadanci. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Tun yaushe aka dawo da kai aiki a wannan kasa, kuma ko ya ka ga kasar?
Jakada: Yanzu watannina bakwai da fara aiki a wannan kasa. Tanzaniya tana da mutane masu haba-haba da neman na kansu. Kuma k=a gaba-gaba a yankin kasashen da ke gabashin Afirka. Duk da haka ina bukatar ‘yan Najeriya da su rika neman fasfo da biza, watau izinin shiga kasa, kafin su bar Najeriya domin gudun wulakanci. Domin duk wanda zai shiga kasashen yankin Arifka ta yamma ba sai ya nemi izini ba, amma dai duk wanda yake da takarda ya guje wa wulakanci, ita kuwa Tanzaniya tana Afirka ta gabas ne, don haka sai dan Najeriya ya samu izini sannan zai shige ta. Dalili shi ne, idan mutum yana da takarda, ofishin jakadanci na saurin sanin ya shiga matsala, sannan zai yi gaggawar taimaka masa. Sannan tunda a yanzu akwai hanyar sadarwa ta yanar gizo, duk wanda zai fita waje, to ya karanta dokokin kasar don sanin irin dokokin da al’adun jama’a.
Aminiya: Shin kai ma’aikacin jakadanci ne cikakke ko dan siyasa ne?
Jakada: Ni ma’aikacin jakadanci ne cikakke ba dan siyasa ba, domin na yi shekaru 31 ina aikin nan, tun da na gama karatun digiri ban san komai ba sai aikin jakadanci. A wata mai zuwa zan cika shekaru 32 cif-cif.
Aminiya: Ya akayi ka fara aikin har ka kai kololuwa?
Jakada: Na fara ne a matsayin ma’aikaci mai digiri na farko, a matasayin matakin albashi na 8, har yanzu na kai mai matsayin albashi na 17.
Aminiya: A wadanne kasashe ka yi aiki?
Jakada: Na fara aikin jakadanci ne a kasar bienna na Austriya, na biyu kasar Ingila, sai kasar Kamaru, sai kuma kasar Saudi Arabiya, sannan sai kuma aka kara mayar da ni kasar Kamaru, sannan kasar Nijar, sai kuma yanzu aka tura ni kasar Tanzaniya.
Aminiya: Ya kake fama idan an kai ka kasa mai sanyi har da zubar da dusar kankara kamar Austriya?
Jakada: A lokacin da nake kasar Astireliya inada sauran kuriciya sosai, sannan na fahimci dalilin da ya sa turawa suke zuwa bakin teku domin su sha rana, don sanyi ya yi yawa. Amma ba suna yi ba ne domin ba su da kunya ko nuna tsaraici, kamar sanyi mai tsananin da aka yi a 1986.
Aminiya: Ya ka yi fama da sauyin harshe na kasashen da ka zauna?
Jakada: Muna da jami’ai da suka lakanci harsuna da dama, su suke fara koya mana kafin mu kama hanya mu yi hijira. A yanzu ina jin Larabci da Turanci da kuma Farasansa.
Aminiya: Shekaru nawa ma’aikacin jakadanci yake yi kafin a tura shi wata kasa?
Jakada: Yanayin shekaru uku ko hudu.
Aminiya: Da an yi wa ma’aikacin jakadanci sauyin wurin aiki yake tafiya da iyalansa ko sai ya je ya yi sharar fage kafin ya aiko su bi shi?
Jakada: Ina tafiya ne da iyalina gaba-gadi, domin akwai shirin a tarbe mu a duk inda za mu nufa. Kuma iyalina na jin Turanci da Larabci da Farasanci, sannan kuma matata tana jin fillanci harshe mu da kuma Hausa. Idan yarana suna inda ake turanci suna sauya harshe, haka yake idan suna wurin da ake sauran harsunan. Kuma yarana sun fi ni jin harsunan nan kwarai.
Aminiya: Ko za ka so su gaje ka?
Jakada: Ya dangata da idan suna son aikin. Jakadu ba sa yin kudi sai dai sanin mutane, watau sanin maza jari ne a aikin jakadanci da sanin harkan duniya.
Aminiya: Shin ana barin iyalin ma’aikacin jakadanci su yi aiki?
Jakada: A da ba sa yin aiki. Amma a yanzu an yi bita inda aka yarda da matan ma’aikatan jakadanci su yi aiki a ofishin jakadanci ko a kasar da suke. Amma fa ma’aikatar jakadanci tana ba da tallafin kudi ne ga mata daya da yara hudu. Sai dai dokokin kasa sun yarda da mutum ya auri mata fiye da daya da haihuwar yara da yawa, shi ya sa wadansu ma’aikatan ke yin haka.
Aminiya: Mene ne ya sa ‘yan Najeriya ba sa iya bin karamar doka, kamar na bin layi da sauransu?
Jakada: Duk dan Najeriya da ya fita kasashen waje yana zama ne mai bin doka. Kuma da yake shugaban kasa Muhammadu Buhari mai taka-tsantsan ne wannan ya sa ko a Najeriya abin ya fara sauyawa.
Aminiya: Watanni nawa yake dauka kafin wanda aka yi wa sauyin aiki ya kama aiki?
Jakada: Ana yin bitar sanin-makamar-aiki na makonni biyu zuwa uku, sannan mutum ya kama aiki cikin watanni biyu.
Aminiya: Yaya ka ji da sauyin tukin mota a Tanzaniya inda direban mota yake tuki daga hannun dama, maimakon yadda ake yi a Najeriya a hannun hagu?
Jakada: Ai na san lokacin da ake tuka mota mai sitiyari a hannun dama kafin sauyin da aka yi a tsakanin 1970 zuwa 1972 a Najeriya, sannan na yi zaman Landan ina matashi, don haka ba sabon abu ba ne a gare ni, inda na dan ji bambanci bai wuce na tsawon kimanin watanni uku.
Aminiya: Me ya taba faruwa da kai na mamaki a aikin da ka yi a kasashen duniya da dama?
Jakada: kasashe na da abubuwa na ban mamaki iri-iri. Sai dai a wadansu kasashen idan an ganka ana maka kallon uku-kwabo, amma idan ka nuna musu cewa kai ba na-baya-ga-dangi-ba ne, sai su gane kurensu. Kamar yadda ya faru a kasar Sin, watau China, inda har suka furta cewa ina da hakuri ba kamar sauran mutane bakaken fata ba.
Aminiya: Mene ne abin da ka yi da kake jin dadinsa?
Jakada: Da na isa kasar Tanzaniya sai na lura gidan jakadan na neman garanbawul, domin tun a shekarar da muka samu ’yancin kai aka gina su a yankin da jakadun duniya ke zama, inda har wani makwabcin gidan bajamushe ya ce ko an sayar da gidan ne, aka ce masa an gyara ne, ya ce sai an yi masa sallama da ni. Sannan wannan ya sa ’yan jaridu suka dauki rahoton a talabijin na kasar, inda hukumar kula da tsabta ta umurci duk mazauna gidajen da su ma su yi wa nasu kwaskwarima.
Aminiya: Shin ko akwai abin da idan ka tuna yake bata mata rai dangane da wannan aikin?
Jakada: Babban abin shi ne rabuwa da dangi. Domin idan ka koma gida sai ka nemi daurin targaden rashin makwabta da dangi da abokai. Sannan kuma gwanjon gidajen ma’aikatan harkokin kasashen waje da gwamnati ta yi ga ma’aikata wadanda suke Abuja kadai aka bar mu da muke aikin gina kasa a waje haka nan, bai yi mini dadi ba.
Aminiya: Yaya za a yi a tada komadar kaurin sunan da Najeriya ta yi a baya?
Jakada: Ya dace ‘yan kasa, musamman matasa, su ba wannan gwamnati goyon baya domin ta fidda kasa daga matsi zuwa ga walwala, don na baya su ji dadi.
Aminiya: A takaice mene ne tarihinka?
Jakada: Ni dan Jihar Admawa ne, sannan na yi karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano. Na yi karatun digiri na biyu a Legas na kuma yi kwasa-kwasai da dama a gida da waje.
Aminiya: Wane shiri kake yi don idan ka yi murabus ka tsunduma ciki gadan-gadan?
Jakada: Ina so in rubuta littafai da kuma komawa aikin gona gadan-gadan.