Ba abin da ya raba PDP da sojojin da aka kora daga mulki – Kankarofi

Daya daga cikin wadanda suka nemi yin takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin tsohuwar Jam’iyyar ANPP a zaben shekarar 2011, Alhaji Ibrahim Kankarofi ya ce mulkin kama-karyar da Jam’iyyar PDP ke yi ya sa ba ta da bambanci da sojojin da ’yan siyasa suka kora daga mulki, don haka ya kamata jam’iyyun adawa su sake […]

Ba abin da ya raba PDP da sojojin da aka kora daga mulki – Kankarofi
Ba abin da ya raba PDP da sojojin da aka kora daga mulki – Kankarofi

Daya daga cikin wadanda suka nemi yin takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin tsohuwar Jam’iyyar ANPP a zaben shekarar 2011, Alhaji Ibrahim Kankarofi ya ce mulkin kama-karyar da Jam’iyyar PDP ke yi ya sa ba ta da bambanci da sojojin da ’yan siyasa suka kora daga mulki, don haka ya kamata jam’iyyun adawa su sake hada karfi su kore ta daga mulki don ceton kasar nan.
Alhaji Ibrahim Kankarofin, ya bayyana haka ne a yayin da ’ya’yan kungiyar magoya bayan sabuwar Jam’iyyar APC suka ziyarce shi a gidansa a birnin Kano, ya ce, “Kamar yadda a 1999 ’yan siyasa suka hadu suka kori soja daga kan mulki, haka ma yanzu Jam’iyyar APC ta zo don ta kori PDP daga mulki.”
Ya ce babu abin da PDP ta sa a gaba na gina kasa tun da ta hau mulki a tsawon shekaru, sai abubuwan da suke mayar da kasar nan baya. Ya kara da cewa koma-bayan da ke faruwa ya shafi duk bangarorin rayuwa kuma “komai ya tsaya cik, tattalin arzikin talaka ya kara tabarbarewa,” inji shi.
Sai ya yaba kan samar da wannan kungiya ta magoyan bayan APC, ya ce ya kamata mutane su tashi tsaye wajen kakkafa irin wadannan kungiyoyin wayar da kai don su rika mara wa Jam’iyyar APC baya a yakin da ta saka a gaba, na kwace mulki daga hannun PDP, wadda ya ce tana tauye hakkin talakawan Najeriya.
Tunda farko a jawabin shugaban kungiyar Alhaji Bello Isa Bayero, ya ce sun kafa kungiyar ce don kawo hadin kai da dinke magoya bayan Jam’iyyar APC, tare da sasanta ’yan takara da wayar da kan masu zabe don su zabi jam’iyyar ta kafa gwamnati a matakai daban-daban.