Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike

Rikicin siyasa a Jihar Ribas na ci gaba da ƙamari tsakanin tsagin Fubara da Wike.

Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike

Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce idan buƙatar tsige Gwamna Siminalayi Fubara ta zama tilas za a iya yi.

Wike ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya jaddada cewa siyasa ba wasa ba ce, kuma ya kamata a bi ƙa’ida wajen tafiyar da mulki.

Hakazalika, ya soki maganar cewa ‘yan majalisa ƙalilan za su iya zama domin yin dokokin jiha.

“Siyasa ba wasa ba ce. Idan har ya aikata abin da ya cancanci a tsige shi, to sai a tsige shi. Ba laifi ba ne,” in ji Wike.

“Ba zan yarda cewa a cikin wannan ƙasa, mutane na tunanin ‘yan majalisa uku za su zauna su yi doka, sannan su ce suna shirin zuwa Kotun Ƙoli.

“Shin har yanzu muna buƙatar yin aiki?” ya tambaya.

Rigimar siyasa a Jihar Ribas ta tsananta bayan da Kotun Ƙoli ta amince da sahihancin ‘yan majalisa 27 da ke goyon bayan Wike tare da soke zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a watan Oktoban 2024.

Har ila yau, Wike ya jinjina wa waɗanda suka ƙalubalanci abin da ya kira rashin bin doka, inda ya bayyana cewa dole ne a mutunta zaɓaɓɓun shugabanni.

“Shugabannin majalisa da ‘yan majalisa ba yara ba ne; an zaɓe su ne, kuma ba yaran kowa ba ne.

“Ya kamata a zauna da su, a gina dangantaka da su,” in ji shi.

Alaƙa dai na ci gaba da zafi tsakanin Wike da yaronsa Fubara, tun bayan da bar mulkin Jihar Ribas.

Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM

Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi

’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina

Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike