Ba Amurke ya shafe shekara 12 yana tafiyar kilomita 34 a kullaum

Wani Ba’amurke Robertson ya fara tafiya a kasa bayan da motarsa ta lalace shekara 10 da suka wuce, inda ya rika shafe kilomita 34 zuwa da dawowa daga wurin aiki. Kuma bai taba makara ba tsawon shekara 12. Don haka Amurkawa da suka samu labarinsa, suka tara masa kudi don ya sayi mota. James Robertson […]

Ba Amurke ya shafe shekara 12 yana tafiyar kilomita 34 a kullaum
Ba Amurke ya shafe shekara 12 yana tafiyar kilomita 34 a kullaum

Wani Ba’amurke Robertson ya fara tafiya a kasa bayan da motarsa ta lalace shekara 10 da suka wuce, inda ya rika shafe kilomita 34 zuwa da dawowa daga wurin aiki. Kuma bai taba makara ba tsawon shekara 12. Don haka Amurkawa da suka samu labarinsa, suka tara masa kudi don ya sayi mota.

James Robertson dan shekara 56 ya kan yi tafiya a kasa zuwa wajen aikinsa da ke garin Woodward a Jihar Detroit, sai ya fara hawa bas zuwa wani gari Somerset Collection da ke Toy, kafin ya karasa zuwa wajen aikinsa a Kamfanin Schain Mold & Engineering da ke Rochester Hills, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito.
daruruwan mutane sun taimaka da makudan kudi don wannan mutumin Detroit ya sayi mota. Mutanen sun tausaya masa ne jin cewa yana tafiyar kilomita 34 a kullum wajen zuwa da dawowa daga wurin aikinsa.
Wata kafar yada labarai ta Detroit Free Press ta bayar da rahoton yadda James Robertson ke samun dani ko a rage masa hanya a wasu motocin bas idan ya dauki hanyar tafiya wurin aiki, amma saboda nisan wurin, dole sai ya shafe kilomita 13 a tafiya, haka kuma a hanyar dawowarsa gida. Wani ma’aikacin banki ya sha rage masa hanya, wanda a kullum sai ya tambaye shi me yake yi a hanyar.
“Na dora ma’aunin zuwa wurin aikinmu a kan wannan mutumin,” inji Todd Wilson, manajan Kamfanin.
“Na yanke cewa, idan wannan mutumin zai iya zuwa aiki a kan lokaci, bayan ya share wadannan mila-milai a cikin kankara da ruwan sama, to abin mamaki ne a ce mutanen da ke zaune a Pontiac, wadanda bai wuce su yi tattakin minti 10 ba, su ce ba za su iya zuwa a kan lokaci ba,” inji shi.
Wani dalibi, Eben Leedy, dan shekara 19 a jami’ar Jihar Wayne, da ya karanta labarin mai cin kilomita 34 a kasa, don zuwa wurin aiki, sai ya bude masa shafin neman taimako, mai taken “GoFundMe,” wato a ‘a tara kudin taimakona,” inda manufarsa kawai ya tara Dala dubu biyar, amma sai ya tara masa kudin sama da Dala dubu 90.
Robertson ya ce kansa ya yi girma, jin cewa hankalin mutane ya kawo gare shi, har suna ta shirin taimakonsa.
Da aka tuntube shi game da shirin gwamnati na samar da bas-bas, wadanda za su kai shi wurin aiki, su dawo da shi gida, sai ya ce: “Kamata ya yi a ce tsari ne na sa’o’i 24, amma ba na wani wucin gadi ba.”
“Wannan birnin na bukatar bas-bas a tsawon sa’o’i 24. Kuma a sanar da majalisar mulki da magajin garin wannan birni, cewa ni na fadi haka,” inji shi.