Ba Arewa kadai ke fuskantar kalubalen tsaro ba –Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya  bayyana cewa kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta ba a yankin Arewa bane kawai ya shafi duk yankunan kasar. Sarkin Musumin, ya kara da cewa zaman lafiyan Najeriya ne bukatarsu a kullum a matsayinsu na Sarakuna. Ya kuma bayyana hakan ne a jawabinsa a wajen taron Sarakunan […]

Ba Arewa kadai ke fuskantar kalubalen tsaro ba –Sarkin Musulmi

Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Musulmin Najeriya.

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya  bayyana cewa kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta ba a yankin Arewa bane kawai ya shafi duk yankunan kasar.

Sarkin Musumin, ya kara da cewa zaman lafiyan Najeriya ne bukatarsu a kullum a matsayinsu na Sarakuna.

Ya kuma bayyana hakan ne a jawabinsa a wajen taron Sarakunan Arewa da aka gabatar a ranar Litinin din nan a jihar Kaduna.

An kuma yi taron ne a gidan tarihi na Arewa da ke a jihar wanda kuma ya samu halartar Sarakuna daga yankin Arewacin kasar nan.

Taron Sarakunan Gargajiya da aka yi a Kaduna