Ba baraka ce ta hana Buhari zuwa gangamin APC na Sakkwato ba – Tambuwal

Alhaji Abubakar Umar danlawan din Tambuwal, tsohon shugaban karamar Hukumar Tambuwal, shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC a yankin Kudancin Jihar Sakkwato. Wakilinmu ya tattauna da shi kan gangamin da jam’iyyarsu ta yi a Sakkwato da sauran al’amuran da suka shafi jam’iyyar da jihar: Kwanan nan ne jam’iyyarku ta yi gangami tare da kaddamar da […]

Ba baraka ce ta hana Buhari zuwa gangamin APC na Sakkwato ba – Tambuwal
Ba baraka ce ta hana Buhari zuwa gangamin APC na Sakkwato ba – Tambuwal

Alhaji Abubakar Umar danlawan din Tambuwal, tsohon shugaban karamar Hukumar Tambuwal, shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC a yankin Kudancin Jihar Sakkwato. Wakilinmu ya tattauna da shi kan gangamin da jam’iyyarsu ta yi a Sakkwato da sauran al’amuran da suka shafi jam’iyyar da jihar:

Kwanan nan ne jam’iyyarku ta yi gangami tare da kaddamar da shugabannin Arewa maso Yamma a Sakkwato, yaya ka kalli taron?
Alhamdulillah ita Jam’iyyar APC kacokam in aka yi maganarta to Arewa maso Yamma ce cibiyarta, wannan yanki shi ne ke da gwamnoni uku na jam’iyyar, tana da jiga-jigan jam’iyyar kuma yanki ne da ke da mafi yawan jama’a, kashi 80 na masu ra’ayin ci gaba da kokarin kawo canji mai ma’ana da alfanu a kasar nan duk daga yankin suke. Wannan gangami da aka yi ya tabbatar da haka domin dimbin jama’ar da muka gani bai ba mu mamaki ba, da ikon Allah a zaben badi dukkan gwamnonin wannan yankin na APC ne, in aka yi la’akari da hadin kan da wannan jam’iyya mai farin jini ke samu. A matakin jiha muna shirin kaddamar da shugabanni da bude ofishin yanki, muna fatar samun nasara kamar yadda shuganinmu na kasa suka samu.
Ba ka ganin rashin zuwan wasu jiga-jigan jam’iyyar kamar Janar Buhari da El-Rufa’i na iya kawo wa tafiyar cikas?
Har yanzu ba ka ji an ce ga korafin Buhari ba, ya kamata ka fahimci Buhari mutum ne kamar kowa yana iya samun matsalar da za ta hana shi halartar taron da ya kamata a gan shi kuma rashin ganinsa a taro ba shi ke nuna matsala a jam’iyya ba, don haka Jam’iyyar APC lafiya lau take, wasu ne kawai ke son shigo mana da wasu abubuwa na cikas kuma da yardar Allah ba za su yi nasara ba. Domin shugabanninmu kansu hade yake mu mabiyansu haka, tafiya ce da muka dauko don ceto kasarmu da Arewa saboda haka rashin zuwan Buhari gangamin Jam’iyyar APC a Sakkwato ba matsala ba ce, saboda ba mu samu wani korafi daga Janar din ko magoya bayansa ba.
A matsayinka na jigon APC a Jihar Sakkwato kana ganin yadda abubuwa ke tafiya in suka dore a haka jam’iyyarku za ta iya lashe zaben Gwamna a 2015?
Haba ko ba a nan jihar kake ba ya kamata ka tabbatar da muna iya lashe zabe mai zuwa da babbar tazara, domin jama’a ne siyasa na tabbata jam’iyyarmu ta samu karbuwa a jihar, ina da imanin duk wani mai hankali a jihar nan APC yake goyon baya fiye da duk wata jam’iyya, kuma ka je ka bincika, ina da yakini da ikon Allah daga kansila har Shugaban kasa mu ne za mu samu nasara. Wannan kyakkyawar tafiya ta samu ne ta dalilin adalcin jagoranmu, Mai girma Gwamna Wamakko, shi ya sa duk wanda ake kira dan siyasa a Jihar Sakkwato yana tare da Wamakko, saboda kishin jiha da sallamawa ga abin da mutane ke so, lallai mun ga nasara da ikon Allah.
Mene ne ra’ayinka dangane da kalaman da ake yawo da su a nan jihar cewa bayan da Gwamna Wamakko ya dare kujera ba wata kulawa da ya yi wa shugabannin kwamitocin rumfunan zabe?
Wannan magana ce kawai don ko taronmu na karshe da aka yi na masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a jihar nan, musamman ya kira taron ne kan abin da ya shafi rumfunan zabe, maganar cewa ba a kula da shugabanin kwamitin rumfa ba gaskiya ba ne, kai ba wasu mutane ne daban ba ke zama shugabannin kwamitin rumfa illa jagororin jam’iyya da mabiyansu da suke cikin gwamnati, kuma kundin jam’iyyarmu ya yi magana kan kwamitocin rumfuna. Ba a taba karfafa kwamitin rumfuna fiye da lokacin wannan gwamnati ba, wasu kawai ke yin magana a bayan fage wadda ba gaskiya ba, ko ni da ke rike da mukamin mataimakin shugaba ina iya zama shugaban rumfa ko mamba, don kowane dan siyasa rumfa yake bugun gaba da ita. Mai girma Gwamna ya karfafa rumfuna ya ja hankalin kowa da ya jingine komai yake ji a sanya wadanda ke iyawa su jagoranci rumfuna domin samun nasara.
Kwana nan Sakataren Jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato ya rubuta takarda ga Gwamna kan rashin biyan fansho da garatuti a kan kari da gwamnatin Wamakko ke yi, za ku duba kalamansa domin gyara ko kun dauka yarfen siyasa ce?
To in aka ce akwai ’yan adawa ba za ka raba su da yin kalamai na batanci, hanya kawai suke nema ta cin zarafi amma maganar fansho tun lokacin da Gwamna ya hau mulki yake kokari a kai, shi ne dalilin da ya sa kungiyarsu take yabon gwamnati a koyaushe. Maganar da nake yi maka mahaifina yana cikin wadanda ke karbar fansho, shekaranjiya aka tantance su cikin wadanda za a biya hakkinsu. Don haka dan adawa ba za ka hana shi fadin albarkacin bakinsa ba, gaskiya ko karya. Maganar fansho lamari ne da sai an tara sa’annan a zo a biya gaba daya, tunda ba lokaci daya mutane ke barin aiki ba, a koyaushe cikin tantancewa ake domin biyansu hakkinsu.
Yankinku na Sakkwato ta Kudu masu son tsayawa takarar Gwamna a Jam’iyyar APC na da yawa kana ganin in aka tsayar daga wani bangare za ku mara masa baya?
To, kamar yadda tsari yake muna kyautata zaton a bar wa yankinmu ya yi, domin tunda aka fara siyasa yankimu bai jagorancin wannan jiha ba. Gabas da Tsakiya duk sun yi, to in aka zo da maganar adalci mu ne za mu yi, kuma mun san maganar adalci mai girma Gwamna ke yi, don haka muke zaton yankinmu ne zai fitar da dan takarar Gwamna.
Ko kana da kira ga magoya bayan Jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato?
Kirana ba zai wuce irin kalaman da Gwamna ke yi kullum ba na a zauna lafiya, kada mu dauki doka a hannunmu, sa’an nan mu ci gaba da addu’a, zaben da ke tafe a yi shi lafiya a kammala lafiya, kuma mu samu nasara. Matasanmu, kada su bi wadanda ke son kawo tashin hankali in sun ga ba za su samu nasara ba.