Ba Buhari ne ya kawo yunwa ba – Sheikh Kabiru Gombe
A daidai lokacin da ‘yan Nigeria ke kokawa da tsadar rayuwa da yunwar da ta addabi jama’a, wacce ake yi wa laƙabi da Buhariyya, shaihin malami Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana cewa ba shugaban ƙasa ne ya kawo tsadar rayuwar da ta addabi jama’a ba. Ya ce shugaba Buhari ba shi ne silar yunwar da ta […]

A daidai lokacin da ‘yan Nigeria ke kokawa da tsadar rayuwa da yunwar da ta addabi jama’a, wacce ake yi wa laƙabi da Buhariyya, shaihin malami Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana cewa ba shugaban ƙasa ne ya kawo tsadar rayuwar da ta addabi jama’a ba.
Ya ce shugaba Buhari ba shi ne silar yunwar da ta addabi talaka ba, domin Allah Ya hukunta cewa a wannan lokacin za a shiga wannan ƙangi, kuma hakan na iya faruwa a lokacin kowane irin shugaba ba sai lallai shugaba Buhari ba. “ Idan kana neman su waye suka janyo wannan matsi na tattalin arzikin ƙasa to waɗanda suka yi sata ne a baya, sukayi rubda ciki da kuɗaɗen jama’a ba wanda yake ƙokari kwato kuɗin da aka sace kuma yake yaƙar cin hanci da rashawa da babakere a kan dukiyar jama’a ba, “ inji shi.
Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana hakan ne a sa’ilin da ya gabatar da muƙala a wa’azin da ƙungiyar Jama’atil Izalatil Bidi’a wa Iƙamatus Sunnah ta shirya wa ɗaukacin jihohin kurmi, wanda ya gudana a ƙarshen makon jiya a jihar Legas.
Ya kuma shaida wa Aminiya cewa tada ƙayar bayan da tsagerun Neja Delta suke yi ne ya ƙara dagula al’amuran ƙasar nan, domin ɓarnar da suke yi na fasa bututun mai da tada bama-bamai a masana’antun fetur sun taimaka sosai wajen taɓarɓarwar halin rayuwa da ƙasar nan ke fama da ita. “ Ko dama can farashin man fetur ya faɗi warwas a kasuwannin duniya, wanda kuma a yanzu da shi ƙasar nan ta dogara kacokan, sai gashi kuma waɗannan tsagerun na ɓarnata fiye da kashi ɗaya bisa biyu na fetur ɗin da ƙasar nan ke samarwa, to ta yaya ba za a samu taɓarɓarewar rayuwa a haka ba, don haka babu hujjar ɗora wa shugaba Buhari alhaki,” inji shi.
Shaihin malamin sai ya yi kira ga al’ummar ƙasar nan da su ƙara haƙuri kuma su ci gaba da addu’a, domin da sannu Allah zai yaye wannan jarabar, mutuƙar mutane sun yi watsi da lalaci da tumasanci da maula da barace-barace, kana suka rungumi aƙidar yin aiki tuƙuru ciƙin gaskiya da riƙon amana. Muddun muka tsaida wannan, to za a samu masalaha kamar yadda a da muka shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi a fannin tsaro a arewacin ƙasar nan. Ni ɗan asalin Arewa maso gabas ne, na san irin halin da muka shiga na taɓarɓarewar tsaro a baya, domin sai da ta kai da na doshi gida Gombe sai fargaba, babu damar yin tafiyar dare, nan tashin bam, can ƙarar bindiga, a Gombe ke nan, ina ga na Barno da Yobe da Adamawa ? Amma yanzu sai son-barka, domin Allah Ya yaye mana, an samu zaman lafiya, ai dole mu yaba wa shugaban ƙasa, kuma duk wanda ka ga yana kukan yunwa da tsadar rayuwa ai don yana raya ne, yana kuma zaune lafiya, wanda bom ya tashi da shi ya mutu ko yake cikin tashin hankali ai bai san dala ta tashi ba, kuma mu dai da tashin bam gara tashin dala, mutuƙar babu tashin bama-bamai, ko dala za ta yi fiffike huɗu ta yi ta tashi sama, muddin muna raye mun san wata rana za ta sauko,” inji shi
Shaihin malamin wanda shi ne babban sakataren ƙungiyar, ya yaba wa ƙoƙarin ‘yan ƙungiyar ta Izala a kurmi, ganin yadda ake samun ƙaruwar gine-ginen masallatai da makarantu a yankin, ya kuma yaba wa Alhaji Abduljalili da shugaban kamfanin Hujjaj, waɗanda su ne suka gina cibiyar addinin musulunci tare da katafaren masallaci a unguwar jakande a Legas, “cibiyar musuluncin da ko a ƙasashen larabawa sai haka,” inji shi.
Ya bayyana cewa ƙungiyar za ta ba da himma wajan yin da’awa a harsunan yarbanci a kurmi domin mahimmancinsa, kasancewarsa yare ne da ake amfani da shi a ƙasashe takwas da ke maƙobtaka da Najeriya, don haka ƙungiyar ke ƙoƙarin buɗe ɗakin watsa labarai a Legas na kafar sadarwar ƙugiyar ta Manara, inda za a dunga yin wa’azin da ya ƙunshi yaran yarbanci.