Ba Buhari ne zai canja komai ba
Idan ’Yan Nijeriya Sun Tuna Cewar Shekaru 16 sun shude shekarun da ’yan Nijeriya suka sha bakar azaba, kunci, fatara da firgici,Rashin ilimi da uwa uba lafiya. Shekarun da babu mai fatan sake ganinsu ko da a wasa kuwa a tsawon lokacin ne mu talakawan Nijeriya muka rasa alkiblar da za mu dora rayuwarmu a […]
Idan ’Yan Nijeriya Sun Tuna Cewar Shekaru 16 sun shude shekarun da ’yan Nijeriya suka sha bakar azaba, kunci, fatara da firgici,Rashin ilimi da uwa uba lafiya. Shekarun da babu mai fatan sake ganinsu ko da a wasa kuwa a tsawon lokacin ne mu talakawan Nijeriya muka rasa alkiblar da za mu dora rayuwarmu a kai, haka mun kasance tamkar bayi a cikin mahaifarsu. A yayin da matsin ya yi kaimi ne, muka shaida yadda al’umma baki dayanta ta wayi gari cikin kuma jin neman karya zalunci da murya daya a kuma kowane yanki babu birni babu kauye, babu Kudu babu Arewa, inda aka yi fito-na-fito domin tabbatar da kalma daya, an dukufa da addu’o’i, ba dare, ba rana wajen ganin kalma daya ta tabbata. Mazaje sun hana idanunsu barci wajen gabatar da bukatu zuwa ga Mahaliccin kowa da komai domin samar da abu daya, tsofaffi da yara sun yi wa azzalumai kofar rago, ta hanyar zolaya da wofantar da su. Duk ba don wani abu ba, sai domin neman abu daya ya tabbata, wannan muhimmiyar kalma, ita ce “Canji!”
Tabbas na sani kuma kowama ya sani cewar ’Yan Nijeriya sun taka muhimmiyar rawa da addu’o’in a wajen neman biyan bukata, kuma Allah Ya biya bukatarmu, canjin da aka jima ana nema ya zo. Bisa al’ada idan ka yi addu’a har ka samu biyan bukata, ya zama dole ka yi wa wanda Ya ba ka nasarar godiya. Ma’ana ka gode wa Allah da ya amsa maka addu’ar. Amma muddin kuma mutun ya yi butulci, hakika za ka iya samun kanka cikin wata matsalar daban. Talakawan Nijeriya sun ci nasara, sun juya akalar shugabancin kasar da hannayensu, sun kuma mika al’ammarinsu a hannun amintattun shugabannin da suka zaba.
To kamar yadda na fada a baya yan zuma zan kuma cewar duk wani dan kasa nagari me kishin talakawa ya sha kurumun sa, a Bawa wannan sabuwar gwamnatin dama ta cika wata shida 6 sannan ministoci su zauna a guraben su duk dan kasar nan zai girbi abun da ya shuka da yardar Allah saboda duk wadancan matsalolin na baya da aka samu in Allah ya yarda za su kau.
Abin da yake daure min kai, shi ne, mutanen da suke fitowa suna caccakar wannan gwamnatin ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari wasu na zagi suna cewar an rike kudi to kada ku manta cewar wannan kasar a baya ta hadu da shugabanni Azzalumai su ne suka kassarata ta kowane bangare.
Kuma A cikin wani hadisin Annabi {S.A.W} ya ce: mutukar al’umma suna yin (zina balle luwadi da madigo) Allah zai saukar da annobar mutuwa da fari, kamar yadda ake ciki yanzu” kowa yana ganin irin halin da muke ciki haka bafa zabar Buhari ne kawai zai canja halin da muke ciki ba, matukar galibin jama’a ba su gyara halinsu ba, sun tsarkake zukatansu tsakani da Allah ba, tilas ne kowanen mu ya daura aniyar fara gyara daga kansa. Akwai abubuwan da ba gwamnati ce ko Buhari ne zai zo ya gyara mana ba, musamman yadda kowanen mu, yake gudanar da mu’amalarsa a tsakaninsa da iyalinsa da yadda yake yi da makwabtansa da mutanen unguwarsu da wuraren harkokinsa, ba Buhari ne zai tsaya a kansa ya ce ya yi abin da ya dace ba. Imaninsa da Allah da hukunce-hukuncensa zai yi amfani da su wajen yin abin da ya dace ko akasin haka. Hakkin da yake kan shugabanni shi ne idan mutum ya ketare iyaka a huldarsa da abokan zamansa ya kai ga shiga hakkinsu da doka ba za ta iya lamunta ba. Yaya Buhari zai yi da kai idan a boye kana tauye mata da ’ya’yanka saboda kai ne mijinsu ko mahaifinsu? Ina ma zai samu labarin abin da kake yi?
Duk wanda ba ya jin tsoron Allah, ba ya jin kunyar mutane bai kamata a ji tsoronsa ba, balle ma a ji kunyarsa.Duk abin da yake tunkaho da shi Allah ya fi shi, kowane ne shi, ko dan wane ne. Allah ne kadai abin tsoro.
Daga Anas Saminu Ja’en Gidan Makera Jihar Kano. 07033882307