Ba cin zabe ne a gaban El-Rufa’i ba – Shugaban APC
Shugaban Jam’iyyar APC a karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna, Ibrahim Koli ya bayyana cewa duk masu fada da gwamna Nasiru El-Rufa’I su sani cewa suna batawa kansu lokaci ne, domin shi yana duba abin da zai amfanar da al’ummar jiharsa da za su zo nan gaba ne, wadanda za su yi alfahari da […]

Shugaban Jam’iyyar APC a karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna, Ibrahim Koli ya bayyana cewa duk masu fada da gwamna Nasiru El-Rufa’I su sani cewa suna batawa kansu lokaci ne, domin shi yana duba abin da zai amfanar da al’ummar jiharsa da za su zo nan gaba ne, wadanda za su yi alfahari da shi tare da tuna shi a matsayin wanda ya taimaki rayuwarsu.
Shugaban, wanda ya bayyana haka yayin tattaunawarsa da Aminiya a garin Kafanchan ya ce wadanda su ke murna kan kotu ta dakatar da korar malamai su sani cewa kada mage ba yanka ba ne, domin ba karshen shari’ar kenan ba tunda yanzu aka fara kuma batun yin jarabawa ga masu son aikin malanta yana nan daram har ga wadanda su ke ganin ba a yi musu daidai ba cikin malaman da suka fadi wancan jarabawar, idan har mutum ya san yana da gaskiya to ya zo ya sake muddin har ya ci to gwamna ya yi alkawarin mayar da mutum aikinsa kuma a matakin da yake ba tare da an rage masa komai ba. “Har kwamiti gwamnati ta kafa don sake duba jarabawar.” In ji shi.
Shugaban ya bayyana cewa abin takaici ne mutum ya kwashi ‘ya’yansa ya kai makarantu masu zaman kansu, amma shi yana koyarwa a makarantar gwamnati.
“Idan har matarka za ta girka maka abinci, sannan ka koma kana sayen abinci a waje ai kana tabbatarwa da kanka ne cewa matarka ba ta iya abinci ba kenan.”
Da ya waiwaya kan ayyukan da gwamnatin jihar Kaduna ke aiwatarwa, Hon. Koli ya ce ko makiyin El-Rufa’i ya san yana ayyukan raya kasa a Jihar Kaduna. “Mu cire ayyukan da ya ke yi a yankin Zariya da Kaduna mu kalli ayyukan da ya ke yi a shiyya ta uku na Kudancin Kaduna musamman kananan hukumomin kaura da Jaba da Kauru da Kachia za a ga kokarinsa. Mu ma a karamar hukumar Jama’a ana gab da fara aiwatar mana da manyan ayyuka da suka shafi gyaran hanyoyi da sauransu wanda har ma’aikatan sun zo sun yi aune-aunensu a kai.”
A karshe shugaban ya yi kira ga jama’a da su sani cewa gwamnatin APC ikon Allah ce domin babu wanda ya yi tunanin za su iya karbar mulki a hanun PDP da ke kan mulki, ga su da karfin tattalin arziki da jami’an tsaro da sauransu amma karfin Allah ya sa mulki ya dawo hanun APC. Don haka ya yi kira ga ‘yan adawa da su sani cewa Allah da Ya baiwa APC mulki har yanzu yana nan kuma mulki na Shi ne don haka da shi suka dogara kuma za su ci gaba da fafutuka.