Ba da aron waya ya jawo kama matar aure a Suleja

Sojoji sun yi awon gaba da wata matar aure mai suna Fatima Ahmadu a Unguwar Magaji da ke garin Suleja, Jihar Neja, a ranar Asabar din makon jiya, inda har yanzu ba a sake jin duriyarta ba ko sanin inda aka wuce da ita. Wasu ’yan uwan matar da wakilinmu ya zanta da su sun […]

Ba da aron waya ya jawo kama matar aure a Suleja
Ba da aron waya ya jawo kama matar aure a Suleja

Sojoji sun yi awon gaba da wata matar aure mai suna Fatima Ahmadu a Unguwar Magaji da ke garin Suleja, Jihar Neja, a ranar Asabar din makon jiya, inda har yanzu ba a sake jin duriyarta ba ko sanin inda aka wuce da ita.
Wasu ’yan uwan matar da wakilinmu ya zanta da su sun ce Fatima Ahmadu mai shekara 31, an kama ta ne da misalin karfe 2:00 na dare bayan sojoji sun kutsa cikin gidan.
Bayanai sun ce an kama matar ne sakamakon ba da aron wayarta ga wata makwabciyarta ta yi magana da mijinta, wanda kuma jami’an tsaron ke nema.
Aminiya ta samu labarin cewa matar da ta yi wayar da mijinta da ’ya’yansu biyu sun ce sun je Suleja ne daga Jihar Taraba saboda tashe-tashen hankula mako daya kafin samamen sojojin.
Mijin Fatima, Malam Ahmadu Ibrahim ya bayyana wa wakilinmu cewa a lokacin da sojojin suka kutso cikin gidan, sun fara yada zango ne a wurin matar inda suka tambaye ta inda mijin yake da kuma wayar da ta yi amfani da ita wajen yin magana da shi.
Ya ce daga nan ne suka nufo dakinsu bayan sun samu labarin cewa wayar da ta kira mijin nata ta matarsa ce. “Sun bukaci wayar matata, bayan ta ba su, sai suka wuce da wayar tare da wancan matar da ’ya’yansu biyu. Sai dai bayan dan lokaci sai suka sake dawowa suka sanar da ni cewa dole sai an tafi da matata, amma za a dawo da ita bayan an yi bincike,” inji shi.
Malam Ahmadu ya ce bayan an tafi da ita da farko wayarta na kadawa idan aka buga mata, amma bayan kwana biyu sai wayar ta daina samuwa. Ya ce matar tasa ta bar ’ya’ya hudu a gida, kuma ta tafi da karami da take shayarwa.
Shi dai mijin matar da jami’an tsaron ke nema, bayanai sun ce kwanansa biyu a gidan, kuma har zuwa ranar da aka kama matarsa ba a sake jin labarinsa ba.