Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba (1)
Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa,‘Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba. Sai dai da kowace maganar da take fitowa daga wurin Allah.’” (Matiyu 4:4) Manu godiya ga Ubangiji Allah Sarkin sarakuna, Mai iko duka domin kaunarSa da alheranSa zuwa gare mu. A wannan mako za mu yi bincike ne […]
Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa,‘Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba. Sai dai da kowace maganar da take fitowa daga wurin Allah.’” (Matiyu 4:4)
Manu godiya ga Ubangiji Allah Sarkin sarakuna, Mai iko duka domin kaunarSa da alheranSa zuwa gare mu.
A wannan mako za mu yi bincike ne a kan me ya sa Yesu Almasihu ya ce ba da gurasa ko abinci kadai mutum zai rayu ba?
Littafin Maimatawar Shari’a 8:3, “Ya koya muku tawali’u, ya bar ku da yunwa, ya ciyar da ku da manna wadda ba ku sani ba, kakanninku kuma ba su sani ba, domin ya sa ku sani, ba da abinci kadai mutum yake rayuwa ba, amma mutum yana rayuwa da kowane irin abin da yake fitowa daga wurin Ubangiji.” Yakan zamo da wuya ka gaya wa wani cewa ai ba da abinci kadai mutum zai rayu ba. Gaskiya ce, muna bukatar abinci domin gina jikunanmu; wato za mu iya cewa abinci shi ne tushen rayuwa, idan ba a samu abinci ba, babu shakka ba za a kai labari ba. Shi ya sa za mu ga cewa mutane da dama karfinsu da hankulansu na kan abinci da farko kafin bauta ko sanin Ubangiji cikin kwanciyar hankali. Ba su kuwa da sanin cewa idan kana da Ubangiji (wato saninSa) cikin rayuwarka, za ka rayu ka kuma ci moriyar rayuwar.
Ubangiji Shi ne tushen rayuwa, Shi ne kuma Mai tanada abincin, Ya ba da rai ma balle abin ci da jiki-turbaya?
Idan muka lura da rayuwar mutane da dama a yau, za mu ga cewa kowa na tattali don gobe, mutane na sa kudade da dama a cikin bankuna, ko asusu, suna tara abinci a cikin rumbuna, suna gina gidaje domin babu wanda ya san gobe -gida biyu maganin gobara. Abu ne mai kyau kwarai da gaske a yi hakan nan, amma mafi muhimmanci shi ne sanin Ubangiji, domin abin da dan Adam yake bukata cikin wannan rayuwa ita ce “kalma daga wurin Ubangiji.”
Bari mu ga misali da rayuwar wani attajiri a cikin Littafi Mai tsarki; Luka 12:15-21, “Ya kuma ce musu, “Ku kula fa, ku yi nesa da kowane irin kwadayi, don yawan kaya ba shi ne rai ba.” Sai ya ba su misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta yi albarka kwarai. Sai ya ce a ransa, ‘To, kaka zan yi? Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonata.’ Ya kuma ce, ‘To, ga abin da zan yi. Sai in rushe rumbunana, in gina wasu manya, in zuba duk amfanin gonata da kayana a ciki. Zan kuma ce wa raina, “Lallai ina da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru. Bari in huta, in yi ta ci, in yi ta sha, ina shagalina.’” Amma Allah Ya ce masa, “Kai marar azanci! A daren nan za a karbi ranka. To, kayan da ka tanada, na wa za su zama?’ Haka, wanda ya tanada wa kansa dukiya yake, ba ya kuwa da wani tanadi a wurin Allah.” Har wa yau muna da irin wadannan mutane da dama, wato masu dogara da abin da suka gada kosuka tara ko suka mallaka. Yin tanadi ba laifi ba ne, amma dogara ga abin da ka tara, abu ne da Ubangiji Allah ba Ya kaunar mu ’yan Adam mu yi.
Muna da mutane da dama wadanda suke gina gidaje da dama cikin fadin kasa cewa ai suna da abin da za su sayar da idan suka shiga cikin matsaloli. To wai shin ina aka bar Ubangiji Allah cikin wannan lamari? Wa ke da ikon barinka ka ga safiyar gobe ko sakan daya nan gaba, tattalin ka ne ko kuwa Ubangiji?
Yesu Almasihu ya ci gaba da wani misali, idan muka ci gaba cikin Littafin Luka 12:22-31, “Sai ya ce da almajiransa, “Don haka, ina gaya muku, kada ku damu da batun rayuwarku, a game da abin da za ku ci, ko kuma jikinku, abin da za ku yi sutura. Domin rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. Ku dubi dai hankaki! Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba su da taska ko rumbu, amma kuwa Allah Yana ci she su. Sau nawa martabarku ta ninka ta tsuntsaye!” Wane ne a cikinku don damuwarsa zai iya kara ko da taki ga tsawon rayuwarsa? To, in ba za ku iya yin karamin abu irin wannan ba, don me kuke damuwa da sauran? Ku dubi dai furanni yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baki, duk da haka, ina gaya muku, ko Sulaimanu ma, shi da adonsa duk, bai taba yin adon da ya fi na dayansu ba. To, ga shi Allah Yana kawata tsire-tsiren daji ma haka, wadanda yau suke a raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle fa ku? Ya ku masu karancin ban-gaskiya! Kuma kada ku damu a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada kuwa ku yi alhini. Ai, al’ummar duniya suna ta neman duk irin wadannan abubuwa, ku kuwa, Ubanku ya san kuna bukatarsu. Ku kwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah, sai a kara muku da wadannan abubuwa kuma.”
Dogararmu ta zama cikin maganar Ubangiji, ta wurin haka ne kuma za mu ci nasara.
Za mu ci gaba A mako mai zuwa idan Allah Ya bar mu da rai da lafiya.