Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba (3)
Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa,‘Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, Sai dai da kowace maganar da take fitowa daga wurin Allah.’” (Matiyu 4:4) Godiya ta tabbata ga Ubangiji Mai iko duka da Ya bar mu cikin masu rai. A wannan makon za mu ci gaba ne da nazari […]
Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa,‘Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, Sai dai da kowace maganar da take fitowa daga wurin Allah.’” (Matiyu 4:4)
Godiya ta tabbata ga Ubangiji Mai iko duka da Ya bar mu cikin masu rai.
A wannan makon za mu ci gaba ne da nazari a kan ikon da ke cikin maganar Ubangiji.
A makon jiya mun ga yadda mutum zai mori rayuwa ta wurin dogara ga kowace kalma da ke fitowa daga wurin Ubangiji. To, ta yaya ake iya sanin kalmar Ubangiji da kuma ikon da ke dauke cikinta? Abu mai sauki, kamar yadda muka sha fadi cikin darussa da dama a kwanakin baya, sanin Ubangiji ne tushen komai. Idan mutum na da sanin Ubangiji cikin rayuwarsa, babu shakka zai gane abin da muke nufi da ikon da ke cikin maganar da yake fitowa daga wurin Ubangiji. Littafi Mai tsarki kuwa ita ce hanyar da za mu iya sanin Ubangiji idan muna bincikensa a koyaushe tare da yin addu’a da ban-gaskiya.
Masu bi da yawa a yau ba sa iya kebe lokacin binciken Littafi Mai tsarki don harkoki da ke gabansu, kamar aikin neman kudi, hira, kallon talabijin, kallon wasan kwallo da makamantansu. Harkokinmu na yau da kullum ba laifi ba ne idan muna yin su ta hanyar da ta dace, amma takan zama abin damuwa idan har ba ma kimantawa. Alal misali, a wuni ana zama a majalisa ana hira, ko a yi sa’o’i biyar zuwa goma ana kalon fim ko wasan kwallo. Idan za mu fadi gaskiya a nan, a rana, awa nawa ne kake kebewa binciken Littafi Mai tsarki? Wane irin lokaci ne kake kebewa domin yin addu’a? Shi ya sa za ka ga mutane da dama ba za su taba gane abin da muke fadi ba, har ma su gaskanta cewa ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace maganar da take fitowa daga wurin Allah. Kafin ka gane ikon da ke cikin maganar Allah, lallai ne mu san me maganarSa/LittafinSa ke fadi? A cikin Littafi Mai tsarki, za mu gani kuma mu gane me Ubangiji Ya fadi game da kanSa da ikonSa da kuma tafarkinSa. Ba ma taba iya ganewa idan ba tare da binciken littafin ba da addu’o’i. Ba za ka taba more rayuwar nan ba idan ba ka san Ubangiji ba. Rayuwar wanda bai san Ubangiji ba na nan ne kamar mutumin da yake tafiya amma bai san inda yake nufa ba, babu shakka irin wannan tafiyar kan kai mutum ga hallaka. Maganar Ubangiji haske ne kuma jagora ce ga tafarkinmu da sawayen rayuwarmu, takan nuna mana hanyar rayuwa da ta dace, hanyar da za mu samu madauwamin rai. Mu yi kokari mu zama masu sha’awar binciken Littafi Mai tsarki cikin rayuwarmu, ko da sa’a daya ne za ka fara bincike, babu shakka za ka samu girma cikin ruhanniya, za mu kuma san ikon rayuwa cikin maganar da take fitowa ta wurin Ubangiji. Idan har mun gane da wannan, lallai babu shakka za mu zama da iko bisa tunanin cewa arzikinmu ne kadai tushen rayuwarmu da kariyarmu.
Akwai misalai da dama cikin Littafi Ma tsarki da za mu iya koyi da su, yadda annabawa da manzanni da ’ya’yan Isra’ila suka rayu ta wurin bin tafarkin Ubangiji da Ya umarce su ta wurin maganarSa kadai, kuma suka ci nasara. Za mu kuma ga inda rashin biyayya ga maganar Ubangiji ta kai su ga hallaka. (Maimaitawar Shari’a 8:3.
Ba za mu iya rayuwa ba idan Ubangiji bai kasance tare da mu ba. Kalmar Ubangiji kadai ce mutum ke bukata domin rayuwa a nan duniya da kuma har abada. Ilimin mutum, iko da arzikin mutum ba sa ba da lafiya ko rai, mu san da wannan domin akwai masu ilimi da arziki da iko cikin tarihi da suka mutu suka bar komai a nan duniya. Wannan ma kadai ya isa ya sa mu gane cewa Ubangiji kadai mutum ke bukata cikin wannan rayuwa ba ilimi da iko ko arziki ba. Babu wani ilimi da mutum zai samu a rayuwar nan da ya fi sanin maganar Ubangiji, babu wani iko da ya fi ikon da ke cikin maganar Ubangiji. Arziki kuma ba yawan kudi ba ne amma wadata cikin (zuciya a kan) komai, wannan kuma kan samu ne ta wurin sanin Ubangiji cikin maganarSa. Ashe idan haka ne, lallai ba da gurasa (abinci da gidaje da motoci da kudi da masu tsaro) ne mutum zai rayu ba, amma sai dai da kowace maganar da take fitowa daga wurin Allah, Halleluya!